Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sana'ar yankan farce ta kai ni inda ni kaina ina mamaki - Rabi'u
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Lokacin karatu: Minti 3
Duk da cewa matasa masu jini a jika suna ganin suna tashe, akwai wasu sana'ar hannu da suke ganin "ƙasƙanci" ne a riƙa ganin suna yi, inda wasu sukan zaɓi wasu ayyuka da ake yin shiga ta alfarma ko da kuwa bai kai ƙaramin sana'ar samun kuɗi ba.
Amma shi Rabi'u Halliru sai ya zaɓi haɗa biyun a guri ɗaya: Matashi ne da ke sana'ar yankan farce, amma sai ya zaɓi ya inganta sana'ar ta hanyar shiga kamar likita, sannan yake amfani da kayan asibiti.
Rabiu Halliru ɗan Kano ne, wanda aka haifa a Tudun Wadan Ɗankade, amma ya je garin Wamba da ke ƙaramar hukumar Wamba a jihar Nasarawa domin karatun allo da barace.
"Ina almajiranci ne sai na fara tunanin wace sana'a zan yi domin in tafiyar da rayuwata ba tare da bara ba. Sai na yi tunanin irin sana'ar da zan yi da ba ta buƙatar jari sosai. Shi ne na zaɓi in fara sana'ar yankan farce."
Sai dai Rabiu ya ce maimakon ya riƙa sana'ar kamar yadda aka saba tun zamanin iyaye da kakanni, "shi ne na fara tunanin yadda zan zamanantar da sana'ar. Shi ne sai na tara kuɗi, na tattara kayan aiki na asibiti, sannan na saya kayan aikin asibiti domin in riƙa shiga kamar likita."
Ya ce tun farkon fara sana'ar ne sai ya haɗu da wani tsohon sanata a jihar Nasarawa. "Yana neman mai yankan farce ne sai aka kai ni, da na yi masa aiki, sai ya ji daɗin aikin da na yi masa, shi ne ya tambaya ko na yi makaranta, na ce na yi firamare, shi ne ya saka ni a makarantar sakandare, har na gama."
Yanzu Rabiu yana fita ne daga Nasarawa ya shiga Abuja, inda yake zagayawa yana sana'arsa, idan ya yi kwanaki sai ya koma gida ya huta.
A game da yadda irin shigarsa ke taimakonsa, Rabiu ya ce, "mutane da dama idan suka ganni a haka, suka irin shigar da na yi, ko ba su yi niyyar yanke farce ba, sai su ce in musu aiki saboda irin shigar da na yi."
Sai dai ya ce lokacin da ya fara shigar irin ta likita domin fita sana'arsa, wasu aboknsa sun riƙa masa dariya, "suna cewa me ya sa zan riƙa shiga haka, ina kuma ɗaukar akwatin kayan aiki mai nauyi."
Kyautar da ya samu
A game da irin kyaututtukan da Rabiu ya samu a sanadiyar wannan sana'ar da yake yi, ya ce babu abin da zai ce wa Allah sai godiya.
Ya ce idan ya duba irin garin da ya fito, da kuma wuraren da ya shiga a sanadiyar sana'ar sai ya riƙa mamakin irin nasarorin da yake samu.
Sai dai ya ce wani wanda ya fara ba shi naira dubu 5 domin ya fara sayan kayan aiki, da wanda ya biya masa kuɗin makaranta, suna cikin waɗanda ba zai taɓa mantawa da gudunmuwar da suka ba shi a rayuwa ba.
"Haka kuma akwai wata mata da ta haɗa ni da mijinta, sai ta buƙaci ya nema min aiki, kuma haka aka yi, ya sama min aiki a wani babban asibiti a Nasarawa, duk a sanadiyar yankan farce. Duk idan na tuna irin waɗannan nasarorin, sai kuma na ga daga ƙauyen da na fito, sai kawai in ƙara yi wa Allah godiya.
Burin Rabiu
Rabiu ya ce duk da yana godiya ga Allah, akwai wasu burukan rayuwa da yake so ya samu idan ya samu dama.
Ya ce, "babban burina a yanzu shi ne in samu dama in koma makaranta, ina ƙara karatu. Wannan shigar da nake yi ta aikin asibiti, ina so Allah ya cika min burina. Shi ya sa nake kallon shigar nan da nake yi a matsayin gwaji kafin in fara saka na asalin aiki," in ji Rabiu.
A game da bambancin da ya samu tsakanin yanzu da lokacin da yake almajiranci, Rabiu ya ce ko ɗansa ba zai bari ya je almajiranci ba.
"Ni yanzu ai ba zan iya komawa bara ba, kuma ko yarona ba zan iya kai shi makarantar allo ba. Ko abokai na fi son masu sana'a. Lokacin da nake makarantar sakandare wasu abokan karatuna sun riƙa cewa wai bai kamata ina makarantar sakandare ba, kuma ina fita sana'ar yankan farce ba."
Ya ce sukan saka shi dariya, "domin na san abin da nake yi, kuma na san ina da burin da nake so in cika."
A game da irin kuɗin da yake samu, Rabiu ya ce akwai riba sosai a sana'ar, "ina samun aƙalla dubu 10, watarana kuma nakan samu dubu 15.