'An gano' jirgin da ya ɓata ɗauke da 'yan ci-rani 200 a cikin teku

Asalin hoton, SALVAMENTO MARITIMO/FACEBOOK
Masu aikin ceto sun gano wani jirgin ruwa maƙare da ƴan ci-rani, wanda aka bayyana cewa ya ɓace bayan da ya bar gaɓar teku daga Senegal a ranar 27 ga watan Yuni.
Masu aikin ceton sun ce an gano jirgin ne a nisan kilomita 114 daga tsibirin Gran Canaria da ke tsakiyar tekun Atlantika.
Mai magana da yawun tawagar masu ceton ta ce: “jirgin da aka tura ya gano wani jirgi da ya yi kama da wanda muke nema, domin daga sama an gano cewa jirgin na ɗauke da mutum kimanin 200.”
"Duk da ba mu tabbatar ɗari bisa ɗari cewa jirgin ba ne, da alama shi ne.”
An bayyana cewa an tuni aka tura wani jirgin ruwa da zai je domin ceto mutanen.
Masu ceto suna bincike a gaɓar ruwan tsibiran Canary saboda wani jirgin ruwan da ke ɗauke da 'yan ci-rani aƙalla 200 daga Afirka da suka ɓata tsawon fiye da mako ɗaya.
Yadda aka yi aikin bincike
A ranar Litinin, Ƙungiyar bayar da agaji mai suna Walking Borders ta ce jirgin masunta da ke tafiya daga Kafountine, a wani garin gaɓar teku a kudancin Senegal da ya kai kilomita 1,700 daga Tenerife, ya ɓace.
Ƙungiyar ta ce akwai ƙananan yara da yawa a ciki, kamar yadda rahotanni daga Efe kamfanin dillancin labaran ƙasar Sifaniya suka ambato.
Akwai irin wannan jirgin ruwa guda biyu ɗauke da gomman mutane da su suka ɓace.
Ma'aikatan ceto a teku na ƙasar Sifaniya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na EFe cewa wani jirgin sama ya shiga sahun aikin bincike.
Jirgin ruwan mai ɗauke da mutum 200 ya bar Kafountine ranar 27 ga watan Yuni inda ya nufi tsibiran Canary.
Bayanan da ake da su ƙalilan ne game da sauran jiragen ruwa guda biyu, sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato Helena Maleno ta ƙungiyar Walking Borders na cewa ɗaya daga cikin jiragen na ɗauke da kimanin mutum 65, akwai kuma wani mai ɗauke da sama da mutum 60.
Abin da ya sa jimillar mutanen da suka ɓata a cikin jiragen kwale-kwalen uku suka kai kimanin 300.
Labarin na zuwa ne 'yan makonni bayan nahiyar Turai ta shaida hatsarin jirgin ruwan 'yan ci-rani mafi muni a tekun Maditereniya, lokacin da wani jirgi maƙare da mutane ya nutse a kusa da gaɓar tekun Girka.
Aƙalla mutum 78 ne aka tabbatar da nutsewarsu, sai dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta ba da rahoton cewa fiye da mutum 500 ne har yanzu ba a gani ba.
Tafiya daga Afirka ta Yamma zuwa tsibirin Canary na cikin mafi hatsari da 'yan ci-rani ke yi, akasari saboda suna shiga teku ne da jiragen kamun kifi waɗanda ƙarfafan igiyoyin teku ke iya tunkuɗe su.
Bara, aƙalla mutum 559 ne suka mutu a cikin teku lokacin da suke yunƙurin tsallakawa zuwa tsibirin na ƙasar Sifaniya, a cewar Hukumar kula da Ƙaura ta Majalisar Ɗinkin Duniya. Yawan waɗanda suka mutu a 2021 ya kai mutum 1,126.











