Man United za ta tsawaita kwantiragin Rashford, Juve na son karɓar Luiz ta bayar da Kean

Rashford

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United na shirin tattaunawa da dan kwallon tawagar Ingila, Marcus Rashford, mai shekara 24, kan tsawaita zamansa a Old Trafford, bayan da ya fara kakar bana da kafar dama. (Sun)

Dan wasan Southampton, mai shekara 28 dan kwallon Ingila, Nathan Redmond na dab da zuwa Besiktas domin a auna koshin lafiyarsa a shirin da yake na komawa kungiyar da taka leda kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a kasar Turkiya ranar Alhamis. (Turkish Football, via Hampshire Live)

Juventus na shirin yin musaya da dan wasan Aston Villa mai shekara 24 dan kasar Brazil, Douglas Luiz, domin ta bayar da Moise Kean, mai shekara 22, zuwa Ingila da taka leda. (JuveLive, via HITC)

Ana sa ran Luiz zai bar Villa a karshen kakar bana a matakin wanda kwantiraginsa zai kare a kungiyar. (UOL, via Sun)

Galatasaray ta amince ta dauki aron dan kwallon Paris St-Germain mai shekara 29 dan kasar Argentine, Mauro Icardi. (Fabrizio Romano)

Haka kuma tsohon dan kwallon Manchester United da tawagar Sifaniya, Juan Mata, mai shekara 34, na dab da komawa taka leda Galatasaray. (Ali Naci Kucuk)

Thomas Tuchel ya yi mamaki da Chelsea ta sallame shi daga Stamford Bridge, bayan da ya bukaci mahukuntan kungiyar su kara masa lokaci. (Sun)

Da kyar ne idan Everton za ta nemi mai tsaron raga bayan da golan Ingila, Jordan Pickford, mai shekara 28, zai yi jinyar watanni, bayan ya ji rauni a wasan hamayya na Merseyside derby da Liverpool ranar Asabar a Premier League. (Sky Sports)

Barcelona ta ki amincewa da tayin da mai tsaron bayanta mai shekara 35 mai tsaron bayan tawagar Sifaniya, Gerard Pique mai son sayen hannun jari a Barca Studios. (ESPN)

Shakhtar Donetsk na neman sama da £30m kudin da za ta sayar da dan kwallon Ukraine Mykhaylo Mudryk, mai shekara 21, bayan da Everton da Arsenal ke son sayen dan kwallon (Gianluca di Marzio, via HITC)