An kori sanatan da bai taɓa halartar zaman majalisa ba

Asalin hoton, GAASYY/YOUTUBE
'Yan majalisa a Japan sun kori wani sanata a majalisar dattawan ƙasar bayan da ya kwashe wata bakwai bai halarci zaman majalisar ba.
Mutumin - wanda fitacccen mai amfani da shafin YouTube ne - ya zama ɗan majalisa na farko da aka kora ba tare da ya taɓa shiga zauren majalisar dattawan ba tun da aka zaɓe shi.
'Yan majalisar dattawan sun kori Sanata Yoshikazu Higashitani ranar Talata sakamakon rashin halartar zaman majalisar.
Tun da aka zaɓe shi watanni bakwai da suka gabata, ko sau ɗaya bai taɓa halartar zaman majalisar ba.
Kwamitin ladabtarwa na majalisar ne ya yanke hukunci korarsa daga majalisar saboda ci gaba da ƙin halartar zaman majalisar da yake yi.
Fitaccen mai amfani da shafin YouTube
A watan Yulin da ya gabata aka zaɓi mista Higashitani zuwa majalisar dattawan ƙasar.
Sanatan - wanda aka fi sani da 'GaaSyy' a shafin YouTube inda ya yi fice wajen wallafa shahararrun bidiyoyinsa - ya zama sanata na farko da aka taɓa kora bisa laifin ƙin halartar majalisa.
Hukuncin kora shi ne hukunci mafi tsauri da ɗan majalisa zai fuskanta.
Kuma a tarihin ƙasar wannan shi ne karo na biyu da hakan ta taɓa faruwa tun shekarar 1950.
Nan gaba kaɗan ne cikin makon nan majalisar za ta tabbatar da korar ɗan majalisar a hukumance.
Rahotonni sun ce ɗan majalisar na zaune ne a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Kafofin yaɗa labaran Japan sun ce sanatan ya ƙi halartar zaman majalisar ne sakamakon fargabar kama shi bisa zargin aikata laifin zamba, da ɓata suna da wasu shahararrun mutane ke yi masa.
Yana ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun 'yan majalisa biyu daga jam'iyyar hamayya ta NHK, jam'iyya ɗaya tilo da ke kiraye-kirayen sauya ɓangaren yaɗa labaran ƙasar.
Jaridar Asahi Shimbun ta ce Jam'iyyar na yawan sauya sunanta saboda dalilai na neman shahara.
Bijirewa kiran 'yan majalisar
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A makon da ya gabata, Majalisar dattawan ta nemi Mista Higashitani da ya je birnin Tokyo domin neman afuwar a zauren majalisar kan kin halartar majalisar da ya yi.
'Yan majalisar sun ce wannan ita ce dama ta ƙarshe da za su bai wa sanatan domin ci gaba da kasancewa mamba a majalisar.
To sai dai mista Higashitani ya ƙi yadda ya halarci zaman majalisar, kamar yadda abokan aikinsa suka buƙata.
A maimakon haka, sai ya bayyana a shafinsa na YouTube cewa zai tafi ƙasar Turkiyya.
Kuma ya faɗa cewa yana shirin sadaukar da albashinsa domin tallafa wa mutanen da bala'in girgizar ƙasar Turkiyya ta shafa.
Rashin halartarsa zaman majalisar ya tunzura sanatocin - waɗanda suka amince da kaɗa ƙuri'ar korarsa a wannan makon.
Ɗan majalisa ɗaya tilo da ke jam'iyya ɗaya da mista sanatan, Hamada Satoshi, ya ce korar sanatan da aka yi bisa laifin rashin halartar majalisar ba ya kan tsarin doka.
Amma duk da haka kwamitin ya amince da korar ɗan majalisar da murya ɗaya.










