Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Boko Haram da ISWAP na ƙara samun fasahohin zamani don ayyukansu
Ƙwararru kan yaƙi da ta'addanci a duniya sun bayyana fargabar cewa ƙungiyar Boko Haram ɓangaren ISWAP ta samo hanyar amfani da jirage marasa matuƙa masu kai hare-hare a kan jami'an tsaro da sauran cibiyoyin gwamnati da jama'a.
"Yanzu haka ita ƙungiyar ISWAP ɗin, ta fara ƙoƙarin yadda za ta yi ta fara ɗaura bama-bamai da sauran abubuwan fashewa a jikin irin wannan jirgin maram matuƙi, 'yan ƙanana," a cewar ɗaya daga cikin mahalarta tarukan a Amurka.
Barista Audu Bulama Bukarti, babban mai bincike a Gidauniyar Tony Blair da ke Birtaniya ya ce matuƙar hakan ta faru, ISWAP na iya kai hare-hare a kan sojoji da sauran wuraren da suke son kai farmaki, ko da ba su tura mayaƙansu ba.
"Kuma wannan, babban abu ne mai hatsari".
Wannan wani ɓangare ne da ƙwararrun suka yi ankararwa a kai yayin tarukan a kan yaƙi da ta'addanci a ƙasashen Afirka musamman Najeriya.
Ya ce taron farko a Jami’ar George Washington da ke birnin Washington ya mayar da hankali a kan gano hanyoyin da ƙungiyoyin ‘yan ta’adda ke samun kuɗaɗe.
"Sai kuma taro na biyu wanda na shekara-shekara ne a hedikwatar kamfanin Meta mai mallakar Facebook a cikin jihar Kalifoniya da ya mayar da hankali a kan ci gaban da ƙungiyoyin 'yan ta-da-ƙayar-baya ke samu wajen amfani da intanet."
Taron ya kuma yi tsokaci kan yadda ƙungiyar ISWAP ta sake samun intanet mai inganci ta hanyar amfani da fasahohin ci gaban zamani mai tsada.
Barista Bukarti ya ce a watannin baya-bayan nan sun gano cewa ƙungiyar ta samo wata hanyar samun ingantacciyar intanet.
"A baya, na yi muku bayani a kan yadda ISWAP take samun intanet, bayan ta shirya bidiyon da take son ta aika ko saƙo. Sai sun zo kusa da gari, sannan su yi ta ƙoƙarin neman intanet. Wani lokacin sai sun ɗebi awanni, ba su samu nasarar samun intanet ɗin da za su tura saƙonninsu ba," in ji mai babban bincike kan ayyukan ƙungiyoyin 'yan ta-da-ƙayar-baya.
Intanet na Thuraya
A cewar ƙwararren duk da yake hanyar tana da tsada sosai amma suna iya sayowa wayar salula ta thuraya da ke amfani da intanet ɗin tauraron ɗan'adam wajen gudanar da harkokinsu.
Barista Bulama ya ce suna sayo wayoyin ne daga Lagos da kuma ƙasar Chadi.
"A Najeriya ba wanda ya fi su samun intanet mai inganci, in ba wanda yake da irin na'urarsu ta thuraya ba".
Akasari dai ƙungiyoyin 'yan ta-da-ƙayar-baya suna amfani da intanet don aika saƙo ga mambobinsu da yaɗa farfaganda da jan hankalin matasa cikin ƙungiyarsu da samun horo da sauransu.
Amfani da jirage marasa matuƙi
Jami'in na gidauniyar Tony Blair ya ce 'yan ta-da-ƙayar-bayan kuma na amfani da jirage marasa matuƙa don gudanar da ayyukansu.
Ya ce tun kimanin shekara biyar da ta wuce, sun lura da yadda 'yan Boko Haram suka samu irin waɗannan jirage na dakon kaya, inda aka gan su a wani bidiyo suna wasa da su.
A cewarsa: "Daga baya sai muka sun fara amfani da wannan drones ɗin wajen leƙen asirin ayyukan sojoji".
Barista Audu Bulama ya ce akwai wani hari da suka kai kafin su ƙaddamar da harin sai da suka saki wannan jirgin ya ɗauki hoton barikin suka ga meye a cikin barikin sannan suka kai wannan harin.
Ya ce abu na gaba mafi tayar da hankali da ƙwararrun suka gano shi ne ƙoƙarin yadda ƙungiyar ISWAP za ta yi amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare.
Mene ne abin yi?
Barista Audu Bulama Bukarti ya ce mahalarta taron sun ba da shawarwarin da suka haɗar da jan hankalin gwamnatoci da jami'an tsaro game da buƙatar ɗaukar matakan daƙile hanyoyin da mayaƙan ISWAP ke samun intanet na thuraya.
"A bi a toshe duk hanyoyin suke samo (wayar) thuraya".
Ya kuma ce lallai ne a bi a tsohe hanyoyin da 'yan ta-da-ƙayar-bayan ke bi wajen samun ƙananan jirage marasa matuƙa.
Haka zalika, babban mai binciken ya buƙaci ƙasashen Afirka kamar najeriya su horas da sojojinsu kan dabarun lalata jirage marasa matuƙa da nufin durƙusar da waɗanda ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi suka mallaka.
Ya kuma ce akwai buƙatar ganin an tabbatar da cewa 'yan Boko Haram ba su samu nasarar yin amfani da jirage marasa matuƙa wajen ɗaura musu bama-bamai don kai hare-hare ba.