Sirrin giwaye masu dogwayen haure da ba su da yawa a duniya
Daga Swaminathan Natarajan
BC World Service

Asalin hoton, Tsavo Trust
"A lokacin da na fara ganin giwa mai dogon haure, na yi mamaki matuƙa. Wani abu ne mai matuƙar kyau," a cewar Nick Haller, wani matuƙin jirgin sama ne da ke aiki da gidauniyar Tsavo, wacce ke aiki don kare giwaye mafiya tsayin haure, wadanda tsawon haurensu yake taɓa ƙasa.
"A irin wannan lokacin sai ka ga ka zama ƙarami, kuma kana kallon kyakkyawar dabba da ke nuna kyawun hauren."
Ƙungiyar kare dabbobi ta IUCN ta ce kusan giwayen Afrika 415,000 suke daji kuma kusan 50,000 na yankin Asiya ne, amma dozin biyu daga cikin su ne kawai masu dogwayen hauren.
Ranar 12 ga watan Agusta ne Ranar Giwaye ta Duniya, kuma mun yi duba kan muhimmancin kare giwaye masu dogwayen haure da ba su da yawa a duniya.

Asalin hoton, Tsavo Trust
Tafiya a hankali
Haller ya fara ganin giwa mai dogon haure ne shekara hudu da suka wuce lokacin da yake tafiya a mota a gandun daji a Kenya.
“Ina tunawa sosai yadda na ga giwa mai zanƙalelen haure da ban taɓa gani ba.
“Da ganinsu ka san giwaye ne na musamman. Ba a cika samun su ba kuma dole mu kare su.”
Giwar ita kadai ce kuma a hankali take tafiya, kuma ba ta da faɗa.
Dukkan giwayen masu dogon haure an saka musu sunaye.
Daga baya Haller ya gano cewa sunan giwar da ya gani a ƙarƙashin bishiya Lugard.
"A yanzu an san Lugard sosai. Babbar giwa ce mai ɗaukar hankali,” ya faɗa cikin farin ciki.
Barazana daga mafarauta
Giwayen kan yi amfani da zanƙalelen hauren nasu wajen tono da ɗaga abubuwa da ma cicciɓe bishiya don mamayar waje.

Asalin hoton, Swaminathan Natarajan
Giwaye masu suna
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Lugard na ɗaya daga cikin giwaye masu dogwayen haure tara da suka rage a gandun dajin mai girman kilomita 42,000.
Haller yana tunanin giwayen masu dogon haure 24 ne kawai suka rage.
“Tsayin hauren yawancin giwayen ya kan kai mita biyu kuma nauyinsu kan kai kilogiram 50,” in ji Haller.
Sai dai abin mamaki, sukan shafe tsawon lokaci kafin hauren ya yi wannan tsawon. Yawancin giwaye masu dogwayen hauren tsofaffi ne da suka haura shekara 50.
Yawancin giwaye kan rayu tsawon shekara 60 ne a duniya, don haka za a iya cewa sai a wuraren ƙarshen rayuwarsu ne hauren ke tsawo,” a cewar Haller.
Akwai kuma wasu giwayen mata da girmansu yake kamar na saniya, waɗanda haurensu ke tsawo fiye da ƙima, duk da dai su ba sa taɓa ƙasa.
A yanzu ƙungiyar Tsavo tana da a ƙalla irin wadannan giwayen masu yanayin saniya har biyar.
“Muna da giwaye masu rikiɗewa zuwa masu dogwayen haure har 27. Suna da manyan haure amma ba su kai na waɗancan ba.
“Idan suka ɗauki lokaci suka kuma samu sarrai za su zama irin wadancan,” in ji Haller.
Ana kuma samun giwaye masu dogwayen haure a gandun dazuka a Botswana da Tanzania.

Asalin hoton, Tsavo Trust
"Za ka iya gane cewa an fi girmama giwaye masu dogwayen haure fiye da sauran a cikin garkensu.
"Daga abin da na fahimta, su ne shugabannin tawagar," in ji Haller.
Dukkan giwaye mata da maza suna da haure. Amma bincike daga Jami'ar Princeton ta Amurka ya gano cewa giwaye mata kan rasa haurensu saboda yawan farautar hauren giwayen da ake yi a wurare da yawa.
Mafarauta sun fi farautar giwaye masu dogwayen haure.
A 2017, an kashe wata giwa mai dogon haure mau suna Satao 2 a gandun dajin Tsavo.
Tun daga sannan ake tsaurara sa ido ta sama da ta ƙasa.
A watan Afrilun bana, an bai wa wani mafarauci dala 50,000 don ya harbo wata giwa mai dogon haure da ta fi girma a Botswana.
Haller kan yi shawagi a jirgi a yankunangandun dajin don gano mafarauta.
"Abin daɗi ne ka gan su a daji. YA kamata mu ci gaba da bakin ƙoƙrinmu don kare su - saboda ƴaƴanmu - da jikokinmu - su ga irin wadannan giwayen masu ban al'ajabi.

Asalin hoton, Tsavo Trust











