Ziyarar da shugaban Guinea-Bissau zuwa China cikin hotunan Afrika

Zaɓaɓɓun ƙayatattun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya a makon da ya gabata

.

Asalin hoton, VINCENT THIAN/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Shugaban ƙasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo ranar Laraba yayin ziyarar da ya kai China.
.

Asalin hoton, GUILLEM SARTORIO/AFP

Bayanan hoto, Diane Rwigara, fitacciyar mai sukar Shugaban Rwanda, Paul Kagame a gidanta da ke Kigali. An dai hanata tsayawa takara a zaɓen ranar Litinin. Ta yi zaman gidan kurkuku na sama da shekara ɗaya, kafin a wanketa.
.

Asalin hoton, TIM DE WAELE/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar Lahadi ne Biniam Girmay ɗan ƙasar Eritrea ya lashe gasar tseren kekuna ta mataki na takwas ta Tour de France.
.

Asalin hoton, GEOFFROY VAN DER HASSELT/AFP

Bayanan hoto, Faith Kipyegon ƴar wasan tseren gudu daga Kenya, ta yi nasara a tseren mata da aka gudanar a Faransa ranar Lahadi.
.

Asalin hoton, PEERAPON BOONYAKIAT/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar ne kuma ɗan wasan ƙwallon Table Tennis kuma ɗan Najeriya Quadri Aruna ya fafata a gasar taurarin Table Tennis ta duniya da aka gudanar a Bangkok.
.

Asalin hoton, AHMAD HASABALLAH/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar Lahadi ne mabiya tafarkin Sufaye suka gudanar da bikin sabuwar shekarar Musulunci a Al ƙahira babban birnin ƙasar Masar.
.

Asalin hoton, KHALED DESOUKI/AFP

Bayanan hoto, A birnin ne kuma ranar Laraba, wani mai sana'ar yin huluna ya fitar da sabuwar hula samfurin dara.
.

Asalin hoton, MICHELE CATTANI/AFP

Bayanan hoto, Mai sayar da ƙarafunan mota zaune a shagonsa a birnin Nouakchott dake ƙasar Maurtaniya ranar Litinin.