Indiya na shirin wuce China wajen samar da wayar salula

Asalin hoton, Deepa Aswani
Sayen sabuwar way ana daga cikin shirin Deepa Aswani, wadda ke aiki a bangaren kasuwanci a Mumbai.
“Ina da irin wayoyin da nake son rika saye a ko da yaushe. Bana son sayen masu tsada can, a cewarta.
Bayan shafe watanni biyu tana kai-kawo, a karshe ta zabi wayar da ake kira OnePlus 10R, wadda ake sayarwa kan dalar Amurka 400, ba ta yi muguwar tsada ba, amma duk da haka kudade ne masu yawa a kowacce kasar, musamman kasashe masu tasowa irinsu Indiya.
“Manufar itace sayan wayar da ba za ta yi maka nauyi ba a aljihu, amma mai kyan fasali duk da haka. Ina farin ciki da wayar da na saya,” in ji ta.
Wani kamfanin kasar China da ke aiki a Indiya ne ya kera sabuwar wayar ta Deepa Aswani wani kamfanin an hada ta ne a kasar China – a wata yarjejeniya da suka cimma a kwanakin nan.
Amma a baya-bayan nan, kamar 2014, mafi yawan mayoyin da ake sayarwa a Indiya shigo da su kasar ake yi.
A shekarun bayan nan kuwa duka lamarin ya sauya. A 2022, kusan dukkan wayoyin da aka sayar a India a cikin kasar aka yi su, kamar yadda Hukumar kula da harkokin wayoyin salula da kayan wuta ta Indiya ta bayyana.
Kamfanonin kasashen waje ne da ke aiki a India ke hada wadannan wayoyin, kamar irinsu Kamfanin wayar Foxconn na Taiwan ko kuma Kamfanin Samsung na Koriya ta Kudu.
Yawan wayoyin da ake kerawa a Indiya na karuwa cikin gaggawa.

Asalin hoton, Micromax
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kamfanin Micromax Informatics na daya daga cikin irin wadan nan kamfanoni. Ya kuma fara kasuwanci waya ne a 2008. Cikin shekara biyu ya bunkasa zuwa daya daga cikin manyan kamfanonin da suke hada waya masu araha, wadanda ake ce musu masu madannai.
Duk da wannan ci gaba da aka samu, daya daga cikin shugabannin kamfanin Micromax Rajesh Agarwal ya ce abu ne mai wuya su goga kafadarsu da ta kamfanonin da ke hada waya a China.
Yayin da kamfanin ya kaddamar da sabuwar wayarsa, Rajesh ya ce suna fatan sayar da kimanin waya miliyan daya a Indiya. Amma kamfanin hada waya na China zai iya sayar da waya miliyan 10 ko sama da haka, hakan yana ba su wata dama mai yawa.
“Suna da matukar karfi ta fuskar samar da kayayyaki,” in ji shi.
Baya ga wannan, kamfanonin China suna samun duka kayan hada wayoyinsu a cikin gida.
Amma Indiya na samun wasu a gida da suka hada da caja da batiri da sauransu, amma mafiya mahimmancin irinsu sikirin da kananan maganadisun waya wanda sai a kasashen waje ake samunsu.

Asalin hoton, Micromax
“Amma ta bangaren masana’antu wannan wani mafari ne a tafiyar. Ya kamata a ce mu ne muke samar da wadannan maganadisu a cikin gida,” in ji Mista Agarwal.
“Fatan shi ne mu tashi daga wadanda muke saya kawai zuwa wadanda muke hada abubuwan da kanmu, har mu iya bai wa duniya, ba kuma waya ba ko kwamfuta a a har ma da sauran na’urori,” ya kara da cewa.
Gwamnatin Indiya na fatan hanzarta wannan buri.
A 2021, ta kaddamar da wani shiri na taimakawa masu harkokin wayar salula da ake kira da PLI.
Wata sabuwar doka da gwamnati ta shigo da ita, wadda a baya aka taba yi, da ke shirin kara yawan abubuwan da ake sarrafawa a Indiya ake fita da su waje.
Shirin ya saukaka kayayyakin waya da ake samarwa a Indiya, domin kamfanonin da ke samar da wayoyi su iya saya domin aiki da su a gida.

Asalin hoton, Micromax
Kididdiga ta nuna kimanin kaso 15 zuwa 20 na kayan wayar akan samunsu a cikin Indiya.
Fatan shirin PLI shi ne kara yawan kayayyakin zuwa kaso 35 ko 40.
“Shirin zai sauya komai a bangaren harkar samar da kayan wuta,” in ji Shugaban shirin Pankaj Mohindroo.
“Indiya na daya daga cikin kasashen masana’antun waya ke ci gaba cikin gaggawa a duniya, kuma it ace yanzu ta biyu wajen kera wayar salula a duniya, in ji shi.











