Shugaban Amurka ya sa hannu kan dokar sauƙaƙa magunguna ga tsofaffi

US President

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Madeline Halpert
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, New York

Shugaba Joe Biden ya ba da sanarwar wasu magunguna guda 10 da hukumomi ke ƙoƙarin sassauta farashinsu ta yadda za su kasance masu sauƙin kuɗi ga tsofaffi.

Dokar Rage Hauhawar Farashi ta Mista Biden a karon farko, ta bai wa tsofaffi 'yan shekara 65 damar neman ragi daga masana'antu a kan farashin magunguna a ƙarƙashin shirin kula da lafiya na gwamnati wato Medicare.

Sassaucin na nufin Amurkawa tsofaffi za su iya samun magunguna masu sauƙi nan da shekara ta 2026.

Magungunan guda goma sun ƙunshi magunguna masu matuƙar tsada na ciwon suga da cutar daji ko kansa da kuma ciwon zuciya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, gwamnatin Biden ta ce sasantawa kai tsaye tsakanin gwamnati da kamfanonin sarrafa magunguna, za ta bai wa Amurkawa tsofaffi damar samun "magani a kan farashi mai rangwame" idan likitoci sun rubuto musu magani.

"Tun daɗewa ne, Amurkawa ke biyan maƙudan kuɗi wajen sayen magungunan da likitoci suka rubuta musu idan an kwatanta da duk wata ƙasa mai ci gaban tattalin arziƙi," Mista Biden ya ce.

"A yau, gwamnatin Biden-Harris tana gabatar da wani muhimmin abin ci gaba wajen aiwatar da doka mai cike da tarihi ta Shugaba Biden d a ke samar da sauƙi a tsarin kula da lafiya da rage tsadar magunguna da kawo wani sabon zamani ga Amurkawa tsofaffi."

Matakin mai yiwuwa ne zai fuskanci adawa daga kamfanonin sarrafa magunguna da 'yan majalisar dokoki na jam'iyyar Rifablikan, waɗanda tuni suka fara sukar lamirin wannan mataki.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mafi yawan tsofaffi 'yan shekara 65 ko sama da haka - su kimanin miliyan hamsin - na amfani da shirin inshorar lafiya na Amurka mai taken Medicare don samun magungunan da likita ya rubuta musu.

Duk da haka, kusan kashi ɗaya cikin huɗu na Amurkawa tsofaffi sai sun yi faɗi-tashi kafi su iya sayen magungunan da suke buƙata, a cewar KFF, wata cibiyar binciken ayyukan lafiya mai zaman kanta.

Fadar White House ta ce tsofaffi Amurkawa sun kashe kusan dala biliyan uku da rabi a shekara ta 2022 daga aljihunsu wajen sayen magunguna guda goma, ciki har da Eliquis mai tsinka jini da Jardiance, wani fitaccen maganin ciwon suga.

Cibiyoyin lafiya na Medicare da Medicaid ne suka zaɓi magungunan guda goma saboda akasari su ne mafi tsada, kuma ba su da madadi sannan miliyoyin mutane ne suka dogara da su a matsayin "hanyar magance larurori masu barazana ga rayuwa ciki har da ciwon suga da ciwon zuciya da kuma cutar daji", fadar White House ta ce.