Masana sun samo hanyar gano kansar mafitsara cikin sauri

Asalin hoton, Getty Images
Masana kimiya a Birtaniya sun ce sun gano cewa ɗaukar hoton cikin jikin mutum da ake kira MRI, ya fi saurin nuna kansar mafitsarar maza fiye da gwajin jini.
Binciken ya tabbatar da cewa hanyar gano cutar kansa ta amfani da ɗaukar hoton jikin mutum ya fi gano alamomin cutar kansa.
Na'urar daukar hoto ta MRI kan ɗauki hoton alamomin cutar kansa da gwajin jini na PSA ke kasa ɗauka.
A halin yanzu babu wata cikakkiyar hanyar gano cutar, saboda ana kallon hanyar gwajin jini ta PSA a matsayin wadda ba za a iya dogara da ita ba, duk kuwa da cewa ana amfani da ita wajen gano cutar tsakanin mazan da suka haura shekara 50.
Masu sabon binciken sun bayar da shawarar yin amfani da hanyar daukar hoton jiki ta MRI domin gano cutar.
Sai dai sun yi kiran faɗaɗa bincike domin ƙara haɓaka hanyar.
Me ake nufi da kansar mafitsara?
- Cutar kan kama wani ɗan ƙullutu da girmansa bai wuce na goro ba, wanda ke ƙarƙashin jakar fitsari.
- Sai ta mamaye hanyar mafitsara - wanda ke ɗaukar fitsari daga cikin jakar ajiye fitsari zuwa waje.
- Kansa cuta ce da za a iya dakatar da ƙwayoyin da suke haddasa yaɗuwa.
- Amma kansar mafitsara tana girma ne a hankali.
- Za ta iya ɗaukar lokaci mai tsawo ba tare da nuna alamu ba
- Kansa na haifar da matsala har ma da kisa a wasu lokuta.
- Don haka ganota da wuri don daukar mataki abu ne muhimmi.
Sabon binciken da aka wallafa a shafin jaridar BMJ da ke bincike tare da lalubo mafita kan batutuwan da suka shafi al'umma ya nuna maza sama da 300,000 ne tsakanin shekara 50 zuwa 75 aka yi gwajin gano cutar ta hanyar amfani da MRI a asibitin koyarwa da ke Landon.
Daga cikin mutum 303 da aka yi wa gwajin, an gano cewa mutum 48 na ɗauke da cutar, inda mutum 25 daga cikinsu, suka fara karɓar magani.
Fiye da rabin mazan da aka gano suna ɗauke da cutar ta hanyar gwajin MRI, hanyar gwajin jini ta PSA ba ta gano suna ɗauke da cutar ba.
Shugaban binciken Farfesa Caroline Moore, ya ce ''sakamakon bincikenmu ya gano cewa hanyar gwaji ta MRI na da inganci wajen gano ƙwayar cutar da wuri''.

Asalin hoton, UCLH
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Paul Rothwell, mai shekara 62 na daga cikin mutanen da aka gano suna ɗauke da cutar bayan da aka yi masa gwajin MRI, an gano cutar da wuri sannan aka ɗora shi a magani.
Yana jin ya yi sa'a saboda gwajin cutar ta hanyar jini na PSA da aka yi masa ya nuna cewa baya ɗauke da cutar, lamarin da ya sa ya kusan kuskure wa gwajin MRI.
Paul, daga Hertfordshire, ya shaida wa BBC cewa "idan da na biye wa gwajin jini da zan ci gaba da rayuwa ta, ba tare da sanin cewa ina ɗauke a cutar ba, kuma zuwa lokacin da alamominta za su bayyana a jikina ta riga ta yi mini illa a lafiyata''.
Ana kallon hanyar gwajin jini ta PSA a matsayin mai amfani amma wanda ba za a iya dogara a kansa ba wajen gano cutar kansa.
Ko da akwai kansar, hanyar gwajin jini ta PSA kadai ba za ta iya tantance mutanen da ke cikin tsananin buƙata.
Sabon binciken ya nuna cewa baƙaƙen fata sun fi fararen fata zuwa domin yin gwaji fiye da ninki biyar, duk kuwa da cewa fararen sun fi hatsarin kamuwar da cutar.

Errol McKellar, mai shekara 66, daga Essex, an gano yana ɗauke da cutar shekara 13 da suka gabata.
Bayan kammala shan magani a yanzu ya koma aiki a matakin bakaniken mota, ya kuma fara yi wa kwastomominsa, matuƙar suka je wajen aikin nasa da takardar gwajin cutar ko ta abokinsu.
A yanzu yana gudanar da gidauniyar Errol McKellar Foundation, da ke wayar da kan jama'a kan cutar, tare da tabbatar da maza da yawa sun je domin yi musu gwajin cutar.
Ya shaida wa BBC cewa "A lokacin da suka kawo min motocinsu domin gyara wa nakan tambaye su yaushe rabon su da yin gwajin kansar mafitsara?"
Farfesa Mark Emberton, babban mawallafin binciken ya ce ya kamata a ci gaba da gudanar da gwajin cutar har zuwa gomman shekaru masu zuwa.
"Adadin masu Kansar mafitsara a Birtaniya ya ninka na ƙasashen Amurka da Sifaniya da saboda hanyoyin da ƙasashen ke amfani da su ba irin na Birtaniyar ba ne''.
Mataimakin daraktan binciken Simon Grieveson, ya ce "idan aka gano cutar da wuri za a iya magance ta.
Amma abin taƙaicin shi ne duk shekara mutum 10,000 ne ake ganowa suna ɗauke da cutar bayan ta gama yi musu illa".
Mene ne alamomin cutar?
Fitattu daga cikin alamomin cutar sun haɗar da:
Jin fitsari a kai- a kai - musamman cikin dare.
Jin zafi gabanin fara fitsari.
Rashin ƙarfin fitar fitsari tare da ɗaukar tsawon lokaci yana fita.
Cakuɗuwar jini da maniyyi a cikin fitsari.
Waɗannan alamomi akwai abubuwa da dama da ke haifar da su, to amma yana da matuƙar muhimmanci a tuntuɓi likita idan aka ga irin waɗannan alamomi.











