Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya kawo fargabar rashin tsaro a Lagos?
Rundunar ƴan sandan jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya ta ce za a tsaurara matakan tsaro a birnin, domin daƙile duk wani hari a wasu sassan jihar.
Hakan na zuwa a dai-dai lokacin aka ruwaito cewa mambobin ƙungiyar ISWAP sun fara samun mafaka a yankin kudu-maso-yammacin ƙasar.
Fargabar samun mafakar ISWAP ta samu ne tun bayan harin da suka kai Cocin Katolika na garin Owo a jihar Ondo, da ya yi sanadin kashe sama da mutum 40 tare da raunata wasu da dama.
A halin yanzu, ƙungiyar sintiri kan harkokin tsaro ta Amotekun a shiyyar gudanar da binciken yadda wasu matasa daga arewacin ƙasar ke kwarara zuwa yankin, cikin manyan motocin dakon dabbobi da cimaka – wani lamari da mazauna yankin ke bayyana fargabarsu a fili.
Dama tun ba yau ba gwamnatin Legas tare da haɗin gwiwar rundunar ƴan sanda suka bayyana shirinsu na tabbatar da tsaro a fadin jihar.
To sai dai sabon rahoton sirri da hukumomin tsaro a jihar suka samu ya ƙara zaburar da jami’ansu sake ƙara ɗaukar wasu dabarun na daƙile duk wani yunƙuri da ke da nasaba da matsalolin tsaro.
Ko da yake a yanzu ba a bayyana ainihin waɗanda suke shirin kai farmaki ga mazauna birnin Legas ba.
To amma rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa akwai wasu miyagun mutane da muradunsu shi ne tayar da zaune tsaye a birnin da ake zaune lafiya a tsakananin ƙabilu da kuma mabiya addinai.
Wasu rahotanni sun nuna cewa mambobin ƙungiyar ISWAP sun fara samun mafaka a kudu maso yammaci, tun bayan wani hari da suka kai cocin a jihar Ondo har aka hallaka sama da mutum 40 ya ƙara tayar da hankalin shugabanni da sauran masu faɗa a ji da ke shiyyar baki ɗaya.
Haka kuma rahotannin da ake ƙara samu masu nasaba da tuɗaɗowar ƴan arewacin ƙasar cikin wani yanayi da suke ce na baiwa al’ummar kudu maso yammaci tsoro, ya sanya waɗannan jihohi shida da ke shiyyar ƙara sa idanu kan masu shiga shiyyar daga arewaci.
Me ƴan Legas ke cewa?
To ko yaya mutane suke ganin wannan mataki mai nasaba da ƙara tsananta matakan tsaro a Legas, babban birnin kasuwancin jihar?
Wata mazauniyar Legas ta ce “hakan na da kyau ƙwarai da gaske, misali a yanzu babu ƴan sanda kusa da unguwarmu, sun ƙaura zuwa wata shiyya da ke dab da babbar hanya.
“To amma fitowar wannan rahoto zai bai wa jami’an tsaro damar sintiri a lungunan layukanmu. Hakan zai ba su damar su ba mu kariya.
“Dole ne a tambayi duk waɗanda ake zargi domin sanin daga inda suka fito da sunayensu da kuma aikinsu. Idan suka gaza bayar da amsa a kama su.
Shi ma wani mazaunin birnin ya ce “To lalle na goyi bayan matsayin da kwamishinan ‘yan sanda ya ɗauka kan tsananta matakan tsaro a jihar.
“Saboda yanayin tsaro a kasar babu dadin ji. Yanayin da ake ciki shi ne yadda ake samun rahotanni masu nasaba da matsalolin tsaro suna firgitar da mazauna shiyyar.
“Ina ganin shi ne dalilin da ya sa kwamishinan ‘yan sanda ya ce za a shaida bincike da kuma tsananta matakan tsaro a jihar.
Rahoton ya ce kwamishinan ‘yan sanda a jihar Legas, Abiodun Alabi, a ranar Laraba ya ce akwai wani ɓangare na ƙulle-ƙullen da jami’an tsaro suka yi a jihar saboda barazanar hare-hare daga wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba.
Rahotanni sun ce ba a rasa nasaba da barazanar tsaro da aka ruwaito a babban birnin kasuwancin na Najeriya.
Alabi ya bayyana hakan ne a Legas a yayin taron ƙungiyar masu ruwa da tsaki na jihar Legas kan almundahanar ‘yan sanda na kowane wata da bayar da kyaututtuka.
Rundunar ta ce ka da mazauna jihar su tayar da hankalinsu kan wasu sabbin matakan tsaro da jami’anta za su dauka a sassa daban-daban da ke fadin jihar.
Hakan ba wani abu ba ne face don tabbatar da an bai wa kowanne mazaunin jihar mai bin doka da oda kariya da kuma dukiyoyinsu.
Idan ana iya tunawa a ‘yan makwannin nan rundunar sintiri kan harkokin tsaro ta Amotekun da ke a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya ta kama wasu mutane da rahotanni suka nuna sun fito ne daga arewacin Naijeriya.