Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masu sayar da motoci sun ce kwastam na kwace masu motoci
Masu sayar da motoci da ke yankin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, sun koka kan yadda suka ce hukumar kwastam ke yawan kai masu samame tana kwashe masu motocin da suka kasa.
Masu sayar da motocin sun ce, wannan al'amari na gurgunta harkokin kasuwancinsu, tare da jefa su cikin mawuyacin hali.
Alhaji Muhammad Lawal Legas, daya ne daga cikin masu sayar da motocin, ya shaida wa BBC cewa, ''bidi-bidi jami'an kwastam sai su dira a wuraren kasuwancinmu su kwashe mana motoci.''
Ya ce," Sai sun zo sun duba motocin sai su ce wai an biya rabin kudi, kuma mu a yanzu ma mun daina zuwa Cotonou mu sayi mota, Legas muke zuwa mu sayi motoci."
Alhaji Muhammad Lawal Legas, ya ce sun daina zuwa Cotonou su sayi mota ne saboda yadda canjin kudin cefa ya tashi.
Mai sayar da motocin, ya ce idan suka sayi motocin a Legas suka taho, a hanya ma an rinka tare ka nan da kyar suke samu suke isa Abuja.
Ya ce, " Idan ka zo Abuja da motocin ma ka ajiye su, wata motar sai ka yi wata shida ba ka sayar da ita ba."
Alhaji Muhammad Lawal, ya ce suna bin duk wasu ka'idoji na shigo da mota, to amma jami'an kwastam sai su yi ta zuwa suna kwashe musu motoci.
Ya ce, "Bayan mun biya kudin fito tun a Legas, a Abuja idan mun zo Abuja aka daukar ma mota sai ace wai rabin kudi ka biya, dole sai mutum ya kara biyan wani kudin."
Mai sayar da motar ya ce, "To mu dai ba mu sani ba ko akwai dokar da ta ce idan ka biya kudin fito a Legas, a Abuja ma sai ka kara biyan wani kudi."
Ya ce su dai yanzu haka suna cikin wani hali domin wani mai mota biyar yanzu ya dawo yana da guda kawai, wani ma gaba daya an kwashe motocin ba shi da ko daya.
To sai dai kuma mukaddashin sifiritandan kwastam, Abdullahi mai Wada, na sashen hulda da jama'a na hukumar hana fasa kauri ta Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, dalilai biyu ne ke sa hukumarsu ta kai irin wannan samame.
Ya ce, na farko idan aka shigo da mota ta haramtacciyar hanya, ko kuma an shigo da motar ta halattaciyar hanya amma kuma ba a biya haraji yadda ya kamata ba.
Jami'in na kwastam, ya ce idan har aka kwace wa mutum mota, to ya zo ya gabatar da cikakkun takardunsa sannan ya biya kudaden da suka kamata ba cuta a ciki, to za a mayar wa mutum motarsa.
Ya ce,"Mu abin da muke so mu fada wa masu motocin shi ne su tabbata sun biya kudaden da ya kamata su biya wa gwamnati."
Masu sayar da motocin dai na son jami'an kwastam din su rinka yi musu adalci wajen bambamce gaskiya, kamar yadda suka yi korafi.