Mane ba zai yi wa Senegal wasan farko a rukuni a Kofin Duniya ba

Sadio Mane

Asalin hoton, Getty Images

Sadio Mane ba zai buga wa Senegal wasan farko ba a rukuni a Gasar Kofin Duniya a Qatar, kamar yadda hukumar kwallon kafar kasar ta sanar.

Dan wasan na jinya, bayan raunin da ya ji a gasar Bundesliga a wasan da Bayern Munich ta casa Werder Bremen.

Teranga Lions ta bayyana Mane cikin 'yan wasan da za su wakilce ta a babbar gasar tamaula ta duniya, duk da raunin da ya ji.

Bayern ta ce dan wasan mai shekara 30 ya ji rauni, sai dai kociyan Senegal, Aliou Cisse ya ce Mane baya bukatar a yi masa tiyata.

Senegal za ta fara wasa a rukuni na uku da Netherlands ranar Litinin, sannan ta buga da mai masaukin baki Qatar 25 ga watan da kuma Ecuador 29 ga watan Nuwamba.

Wani Mamba a hukumar kwallon kafar Senegal ya ce ''Za mu buga wasan farko ba tare da Mane ba, muna kuma fatan mu yi nasara.'' in ji Abdoulaye Sow.

"Ba wanda zai so hakan, amma abin da zai kasance da mu kenan."

Sow ya kara da cewar kada Senegal ta kadu saboda rashin zakaran kwallon kafa na Afirka karo biyu.

Mane kashin bayan Senegal ne, wanda ya ci mata fenariti da ta lashe kofin nahiyar Afirka a karon farko a Kamaru a watan Fabrairu, bayan cin Masar.

Haka kuma Mane shi ne ya taka rawar da Senegal ta doke Masar ta kuma samu gurbin shiga gasar kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci.