Ko mata na iya tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasar Iran?

Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon bidiyon

Yayin da ya rage kwanaki ƙalilan a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Iran, ko mata suna iya tsayawa takara a ƙasar mai bin dokokin addinin Musulunci?

Za a yi zaɓen ne ranar Juma’a 28 ga watan Yunin da muke ciki, bayan rasuwar Shugaba Ebrahim Raisi a wani hatsarin helikwafta.