Me ya sa ake binciken 'Qatar-gate' a Isra'ila kuma ta yaya hakan zai shafi Netanyahu?

Asalin hoton, EPA
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yana shan suka bayan kama wasu mutum biyu na kusa da shi bisa zarginsu da alaƙa da Qatar.
A ranar Talata cewa wata kotun Isra'ila ta tsawaita tsare Yonatan Urich, wanda hadimin Netanyahu ne da Eli Feldstein, wanda tsohon kakakinsa ne domin a ƙara bincike. Sai dai dukansu sun musanta aikata wani laifi.
Netanyahu - wanda shi ma da kansa ya bayar da bahasi a gaban ƴansanda game da binciken na "Qatar-gate" ba a bayyana shi a cikin waɗanda ake zargi ba.
Shi ma wani jami'in Qatar ya yi watsi da binciken, inda ya ce "yunƙurin ɓata suna ne"
Dama can Netanyahu yana fuskantar zarge-zarge da dama na cin hanci da rashawa, waɗanda ya daɗe yana musantawa.
Haka kuma an sha gudanar da zanga-zangar adawa da wasu daga cikin matakan, ciki har da komawa fagen daga a yaƙinsa da Hamas, da dakatar da daraktan jami'an tsaron cikin gidan ƙasar da ake kira Shin Bet, wanda shi ne yake jagorantar binciken na Qatar, da ma yunƙurin yi wa ɓangaren shari'ar ƙasar garambawul.
Abin da muka sani game da binciken
An fara binciken ne kimanin wata biyu da suka gabata, amma ya lamarin ya ƙara fitowa fili ne bayan ƴansandan Isra'ila sun sanar a ranar Litinin cewa sun kama mutum biyu da ake zargi.
Ana zarginsu ne da alaƙa da wani ejan na wata ƙasa, da cin hanci da cin amana, kamar yadda rahotanni daga Isra'ila suka ruwaito.
A ranar Talata, mai shari'a Rishon LeZion na kotun majistare ya tsawaita tsare waɗanda ake zargin guda biyu da ƙarin kwana uku, inda kotu ta ce lallai "akwai abin da ya kamata su amsa." Ƴansanda sun buƙaci a tsawaita tsaron ne da kwana tara.
A ranar Alhamis Qatar ta musanta zarge-zargen, waɗanda ta bayyana da "marasa tushe", sannan ta yi gargaɗin cewa "ana yunƙurin kawo tsaiko kan sulhu."

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wakilin ƴansanda ya bayyana wa alƙalin cewa ana zargin Urich da ba ƴanjarida wasu bayanai daga wata majiya da ke da alaƙa da Qatar, waɗanda aka nuna tamkar sun fito ne daga wani babban jami'in gwamnati ko na tsaro.
Masu bincike suna zargin mutanen guda biyu da yin wasu abubuwa da suke "ɗaga darajar Qatar" da "yaɗa labarai marasa daɗi game da Masar da matsayinta na shiga tsakani kan batun tsagaita wuta a Gaza.
Domin wannan ne, alƙalin ya ce, an "an ƙulla alaƙar kasuwanci da tattalin arziki" da wani kamfanin Amurka da ke Qatar ta hanyar ayyukan Urich domin ya samu kuɗi da Feldstein ke karɓo masa" ta hannun wani ɗankasuwa ɗan Isra'ila.
Qatar ta ce ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da kawo ƙarshen yaƙin Gaza, kuma tana aiki da Masar.
Ƙasashen guda biyu "suna tattaunawa a kullum domin shiga tsakanin," kamar yadda wata sanarwa da aka kalato daga wata kafar watsa labarai ta Qatar.
A makon jiya, kafofin watsa labarai na Isra'ila ta wallafa wata murya, inda a ciki aka ji muryar na cewa ya tura kuɗi zuwa ga Feldstein a madadin kamfanin na kamun-ƙafa.
Sai dai lauyan Felstein ya ce kuɗin da ake magana an tura kuɗin ne domin biyan "Feldstein kuɗin aikinsa na tsare-tsare da watsa labaran da ya yi wa ofishin firaminista, ba kuɗin Qatar ba ne."
Me hakan ke nufi ga Netanyahu?
Netanyahu ba ya cikin waɗanda ake zargi, amma shi ma yana fuskantar zarge-zargen cin hanci. Ya dai sha musanta zargin, amma duk da haka zarginsa kawai da cin hanci matsala ce babba.
Bayan bayyana bahasinsa a ranar Litinin, Netanyahu ya yi watsi da bincike, wanda ya bayyana da "bincike mai alaƙa da siyasa."
Jam'iyyar Likud ta Netanyahu ta ce binciken da kamen da ake yi, ana yi ne domin hana dakartar da Bar - wanda zai cigaba da zama a ofis har kotun ƙoli ta tantance buƙatar.
Gwamnatin ƙasar ta sallami Bar ne a ranar 21 ga Maris, inda ta ce ya gaza wajen daƙile harin Hamas na ranar 7 ga Oktoban 2023 wanda ya jawo yaƙin Gaza.
Jam'iyyar Likud ta fitar da sanarwa, inda a ciki ta zargi ofishin babban mai shari'a na ƙasar da shugaban rundunar Shin Bet na ƙirƙirar ƙarya da yunƙurin "tursasa Yonatan Urich ya bayar da bayanan ƙarya game da firmanistan."
Masanin harkokin tsaro da leƙen asiri na Isra'ila, Yossi Kuperwasser ya ce abin da yake faruwa a ƙasar akwai ɗaure kai.
Ravit Hecht, ya rubuta a jaridar Hareetz cewa idan aka gano akwai wata alaƙar harkokin kuɗi tsakanin ƙasar da Qatar - wadda ke da alaƙa da jagororin Qatar - musamman bayan harin 7 ga Oktoban 2023 "zai ba da mamaki" kuma wataƙila "ƙarshen" Netanyahu ke nan wanda dama yake fuskantar ƙalubale.
Me Qatar ta ce?
Ƙasar Qatar dai ta kasance tana cikin mai shiga tsakani domin sulhunta tsakanin Isra'ila da Hamas, kuma ta ce za ta cigaba da hakan, duk da zargin, wanda ta ƙaryata.
A lokacin da ake yaƙin Isra'ila da Gaza, Qatar tare da Amurka da Masar sun taimaka wajen cimma yarjejeniyar tsagaita da sakin waɗanda ake tsare da su.
Qatar dai ta daɗe tana taimakon mutanen Falasɗinu, kuma jagororin siyasa na Hamas suna zama a ƙasar, wadda ita ma Isra'ila da Birtaniya da Amurka da wasu ƙasashe ke gani a masayin ƙungiyar ƴanta'adda.
Amma duk da haka, Isra'ila ba ta ayyana Qatar ba ta taɓa bayyana a matsayin abokiyar adawa

Asalin hoton, Getty Images
Wani jami'in Qatari ya bayyana wa jaridar Financial Times ta Landan cewa, "ba yau aka fara ba ne waɗanda ba so a kawo ƙarshen Isra'ila da Hamas suka fara ɓata mana suna."
Haka kuma ƙasar ta fuskanci zargin karɓar kuɗi domin yin wani aiki a baya - duk da ta musanta.










