Fifa Club World Cup: Za a fara gasar mata daga Janairu zuwa Fabrairu

Za a fara gasar kwallon kafa ta mata ta zakarun kungiyoyi nahiyoyin duniya, wato Women Club World Cup daga Janairu zuwa Fabrairun 2026, in ji Fifa.

Za a fara gasar da kungiyoyi 16 da za ake yi duk bayan shekara hudu da za ta fada a lokacin da ake Champions League na mata a Turai daga karawar rukuni zuwa zagaye na biyu.

Ana fara gasar kwallon kafa ta mata ta Amurka daga farkon watan Maris.

Fifa ta sanar da wannan tsarin tun daga Disambar 2022, yayin da babban taron da ta gudanar a Bangkok ranar Laraba ya tabbatr.

Barcelona ce ke rike da kofin Champions League na mata na bana, yayin da NY Gotham ce ke rike da kofin NWSL da kuma Corinthians ta Brazil mai Copa Libertadores na mata.

Haka kuma taron ya amince da kalandar da za ake buga wasa na kasa da kasa daga 2026-29 da zai bayar da damar da 'yan wasa za suke samun hutu, inda daga karawa shida ya koma biyar.

Za a fara sabuwar gasar cin kofin zakarun kungiyoyi nahiyoyi duniya ta maza wadda aka sauya mata fasali daga badi, wadda za ake yi duk bayan shekara hudu.

Haka kuma a taron an kusan kada kuri'ar kasar da za a bai wa bakuncin gasar cin kofin duniya ta mata da za a yi a 2027, inda ake takara tsakanin Brazil da kuma hadaka tsakanin Belgium da Jamus da kuma Netherlands.