Ko yaƙin da Taliban ke yi da sauyin yanayi alheri ne ga maƙwabtansu?

- Marubuci, Firuz Rahimi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service in Northern Afghanistan
- Lokacin karatu: Minti 5
Yana da faɗin sama da mita 100 kuma ya miƙe har iya ganin ido, katafaren aikin gine-gine da ƴan Taliban ke gudanarwa a arewacin Afganistan wani babban abin a zo a gani ne.
Wani ɓangare na manufarsa shi ne yin wani abu wanda ya saba da kudurorin ƙungiyar, wadda ta karɓi mulki a shekarar 2021 - yaƙi da sauyin yanayi.
An kashe sama da dala miliyan 600 kuma zai kai tsawon kilomita 285 idan an kammala shi, babban magudanar ruwa ta Qosh Tepa za ta kawo ruwan da ake matuƙar buƙata zuwa larduna uku a arewacin Afghanistan.
Wannan gagarumin aikin ba magance sauyin yanayi kaɗai zai yi a yankunan noma da ake da su ba, har ma da nufin mayar da busasshiyar ƙasa mai fadin murabba'in kilomita 5,000 zuwa ƙasa mai albarkar noma.
Taliban na fatan za ta inganta yanayin abinci da kuma rayuwar dubban ɗaruruwan mutane.

Asalin hoton, AP
Damuwar ƙungiyar game da sauyin yanayi ya ɗauki hankulan duniya lokacin da wakilai da dama suka isa taron sauyin yanayi na COP29 a Azerbaijan.
Yayin da akasarin ƙasashen duniya suka yi watsi da su, an bai wa ƴan Taliban damar halartar taron saboda munanan matsalolin da Afganistan ke fuskanta.
An lissafa ƙasar a matsayin ɗaya daga cikin goma da ke cikin haɗari kuma mafi ƙarancin shiri don tunkarar matasalar sauyin yanayi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wajen taron, ƙungiyar Taliban ta buƙaci ƙasashen duniya da suka dakatar da bayar da kuɗaɗe don ayyukan daƙile sauyin yanayi a lokacin da ƙungiyar ta karɓe mulki, da su dawo da shirin ba su gudummawa.
Matuil Haq Khalis, shugaban hukumar kare muhalli ta Afganistan, ya shaida wa manema labarai cewa, "Muna fatan a ƙarshen wannan taro, za a samar da mafita ga ayyukan da aka dakatar a Afghanistan."
Canal Qosh Tepa yana ɗaya daga cikin ƴan ayyukan da ke da alaƙa da yanayi da ke ci gaba da gudana.
Gwamnatin Taliban ce ta samar da kuɗaɗen ta kuma fara gudanar da aikinta ba tare da wani taimako daga waje ba kuma tana samun ci gaba cikin sauri inda ta riga ta gina sama da kilomita 100.
Aiki ne da zai ci makudan kuɗi ga ƙasar, wadda tattalin arzikinta ya ragu da sama da kashi 2 cikin 100 tun lokacin da ƙungiyar ta karɓi ragamar mulki kuma inda sama da kashi 90 cikin ɗari na mutanen ƙasar ke rayuwa cikin talauci.
An fara tsara shirin ne a cikin shekarun 1970, tare da manufar daƙile bushewar arewacin Afghanistan. An dakatar da aikin na shekaru da dama, galibi saboda da rikice-rikicen da aka daɗe ana fama da su a ƙasar.
Gwamnatin da ta gabata ta ɗora alhakin tafiyar hawainiya da aikin ke yi kan ayyukan da tsagerunTaliban ke yi a yankin.

Barazanar da ake fuskanta daga sauyin yanayi ya sanya ana buƙatar magudanar ruwan cikin gaggawa.
Haji Rajab na ɗaya daga cikin masu buƙatar wannan taimakon.
Ya yi noma a kusa da magudanar ruwan a gundumar Aqcha, a lardin Jawzijan, tsawon rayuwarsa, amma ruwan bazara da ya dogara da shi ya ci gaba da raguwa.
Da yake nome busasshiyar ƙasa a ɗaya daga cikin gonakinsa, manomin mai shekaru 70 ya ce yankin ya yi fama da fari na shekaru uku kuma babu amfanin gona a nan.
“Mutane suna kokawa. Ba su da isassun kuɗaɗe kuma fari ya sanya su cikin matuƙar wahala,” in ji shi.
A cikin ƙasar da sama da kashi 80% na al'ummar ƙasar suka dogara kan aikin noma, wannan babbar matsala ce - sama da mutane miliyan 12 suna fama da matsanancin ƙarancin abinci.
Sai dai ba Afganistan ba ce kaɗai a yankin da ke fama da matsalar sauyin yanayi ba. Ruwan zai samu ne daga kogin Amu wanda ya ratsa kan iyakar arewacin Afganistan ya wuce zuwa Uzbekistan da Turkmenistan.
Babbar cibiyar nazarin harkokin tsaro ta Manohar Parrikar, ta yi gargadin lokacin da magudanar ruwar ta fara aiki sosai, za ta iya rage yawan ruwan da ke kai wa ƙasashen makwabta da kashi daya cikin biyar.
Kasancewar Turkmenistan da Uzbekistan sun dogara sosai kan kogin Amu don aikin noma, sun nuna damuwa kan aikin magudanar ruwan.
Wani rahoto da cibiyar ta fitar ya ce: "lamarin na ci gaba da ta'azzara sosai yayin da ƙasashen ke fuskantar rashin tabbas."
An kuma nuna damuwa kan saurin da ake yi wurin aiwatar da aikin da kuma ko akwai isassun kwararru a Afganistan don kammala irin wannan gagarumin aikin ba tare da taimako daga waje ba.
Ƙungiya mai rajin kare muhalli ta 'Rivers Without Borders' ta bayar da rahoton cewa, tuni aka samu wani babban malalar ruwa daga magudanar a cewar binciken da suka yi na hotunan tauraron ɗan‘adam.

Jami'ai a Afganistan dai sun ce wannan gagarumin aikin yana tafiya yadda ya kamata kuma za a kammala shi a kan lokaci a shekarar 2028.
Zabihullah Miri shi ne babban injiniya kuma a baya ya yi aikin haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da dama kan manyan ayyukan gine-gine na farar hula a ƙasar.
Ya yi imanin cewa damuwa da ake nunawa game da ruwan da magudanar za ta karkatar daga kogin Amu bai dace ba.
"Za mu iya cewa ba wani babban lamari ba ne kuma ba zai shafi ruwan da wasu yankuna ke samu ba," in ji shi.

Mutane da dama a Afghanistan suna fatan hakan ne lamarin zai kasance.
Iyalan Abdul Mobin sun kwashe shekaru da dama suna noma gona ɗaya a gundumar Dawalatbad, a lardin Balkh.
Amma a cikin shekaru uku da suka gabata babu abin da aka iya shukawa saboda fari.
Duk da cewa ba a kammala aikin magudanar ruwan ba, ruwan da ke cikin kasa da ke ɓulɓula a cikinsa ya shayar da gonarsa har ya sake fara noma.
Ga manomin mai shekaru 37, wanda ke tallafa wa matarsa da ƴaƴansa uku da surukarsa, wannan lamari ne da zai yi matuƙara sauya rayuwarsa.
"Ina so in gina gida don iyalina, ina so in dawo nan da zama," in ji shi. "Saboda za mu sami ruwa kuma za mu yi noma mu kuma shuka duk abin da muke buƙata a wannan ƙasa, tun daga tumatir zuwa ƴaƴan itatuwa."
Yayin da barazanar sauyin yanayi ke ci gaba da ƙamari, ba ƙaramin fata ake da shi kan wannan katafaren aikin ba.











