Trump ya kafe cewa "kowa na son" shirinsa na karɓe iko da Gaza

Lokacin karatu: Minti 5

Shugaba Trump na Amurka ya tsaya kai da fata cewa "kowa na ƙaunar" shirinsa na Amurka ta ƙwace zirin Gaza.

Ya faɗi hakan duk da irin watsi da suka da bayyana shirin nasa da al'ummar Falasɗinawa da shugabannin Gabas ta Tsakiya da gwamnatocin ƙasashen duniya suka yi.

"Kowa na ƙaunar ƙwacewar" kamar yadda Trump ya shaida wa ƴanjarida a fadar White House lokacin da aka tambaye shi martaninsa dangane da shirin nasa.

Ya kuma ƙara da cewa "lokaci bai yi ba" na yin wasu ƙarin tambayoyi a lokacin da ke sa ido kan shan rantsuwar babban mai shari'a na Amurka, Pam Bondi.

Donald Trump dai ya firgita Falasɗinawa kan shawarwarinsa game da makomar zirin Gaza, saboda ya ce Amurka za ta ƙwace iko da zirin tare sauya fasalinsa.

Wannan ne sauyi mafi girma game da manufofin Amurka kan yankin gabas ta tsakiya cikin gomman shekaru.

Trump ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a fadar White House tare da firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.

"Amurka za ta ƙarbi ikon zirin Gaza kuma za mu mallake zirin kuma mu dauki alhalin kwance nakiyoyin da aka dąsa sannan kuma gyara wuraren da aka lalata," in ji Trump.

Nan da nan firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya nuna jin dadinsa ga kalaman na Mr Trump, inda ya ce hakan zai canza tarihi.

Netanyahu ya ce "ina kara maimaitawa, muradinmu uku ne kuma na uku shi ne tabbatar da cewa zirin Gaza bai kara zama barazana ga Isra'ila ba."

Shugaban Amurkar ya kuma bayyana abin da yake tunani game da makomar gabar yamma da kogin Jordan, inda ya ce yana tunanin nuna goyon bayansa ga shirin Isra'ila na kwace iko da gabar yamma din.

Netanyahu dai shi ne shugaban wata kasa na farko da ya kai ziyara fadar White House tun da Trump ya koma kan karagar mulki a karo na biyu.

Abin da Trump ya faɗi kan ƙwace Gaza

"Amurka za ta karɓe zirin Gaza, kuma za mu yi abin da ya dace. Za mu mallake shi kuma za mu ɗau nauyin tsaftace zirrin da lalata duk wasu abubuwan fashewa masu haɗari da bama-bamai da ba su fashe ba, da sauran makamai.

"Zamu daidaita komai da kau da gidajen da aka ruguza. Zamu share birnin da samar da cigaba na tattalin arziki da zai samar da ayyuka mara iyaka da gidaje ga mutanen yankin.

"Za mu yi aiki na gaskiya. Za mu yi abubuwa na daban. Babu koma wa baya. Koma wa baya na nufin a sake faɗawa gidan jiya irin yanayin da ake ciki shekaru 100 baya."

Bayan waɗannan kalamai, Anyi wa Trump tambayar cewa wani irin iko yake da shi na raba mutane miliyan 1.8 da Gaza.

Martaninsa: "Na hango mun mallake wannan wuri, sannan na hango yadda hakan zai tabbatar da zaman lafiya a wannan yanki na gabas ta tsakiya, babu mamaki baki ɗaya Gabas Ta Tsakiya ma, kuma duk wanda nayi magana da shi, ya fahimci hakan ne mafita.

"Duk mutanen da na tattauna da su, sun nuna goyon-baya da wannan shawara ta Amurka na mallake zirrin, samar da cigaba da ayyuka ga dubbai, tsari ne da ba a taba ganin irinsa ba."

Me Trump ya ce kan sake tsugunar da al'ummar da ke Gaza a yanzu?

Kafin a shiga taron manema labarai, Trump ya tattauna da Netanyahu a gaban manema labarai a Fadar White House, inda ya yi waɗannan kalamai:

"Idan aka yi waiwaye, kullum mutuwa ake yi. Abu ne da an shafe shekaru yana faruwa, kullum mutuwa. Idan muka samu wuri mai kyau da zamu tsugunar da mutanen na dindindin a gidaje masu kyau, inda za su yi rayuwa cikin farin ciki, babu batun harbi ko kashesu, babu batun kashesu da wuka kamar abin da ake gani a Gaza...

"Ina ganin babu laifi sake tsugunar da su, kuma ina ganin za mu cimma hakan a yankunan da shugabannin ke cewa A'a."

Me Trump ya ke cewa kan mafita da yanayin da Gaza zai kasance?

A karshen taron manema labaran, Trump ya ambato muradansa kan yanayin da Gaza zai kasance nan gaba:

"Har na hango mutane na rayuwa a can, mutane daga sassa na duniya. Ina ganin zamu mayar da zirrin wani yanki da duniya ta jima bata gani ba. Gaza wuri ne da ke da dimbin albarkatu.

"Ina ganin duk duniya - wakilai daga ko ina a duniya - za su kasance acan, su ma Falasdinawa za su zauna acan, mutane da dama za su zauna acan...

"Dole mu koyi da abubuwa daga tarihi, ba za mu bari tarihi ya cigaba da maimaita kansa ba. Muna da damar yin abubuwa na daban.

"Za mu tabbatar mun yi abin da zai kai kololuwa a duniya, zai kayyatar da mutane, Falasdinawa musamman da ake magana a kansu. Duk da dai suna nuna adawa, ina da yaƙinin cewa Sarkin Jordan da kuma kasar Masar za su buɗe mana zuciyarsu da bamu irin yankin da muke so, saboda tabbatuwar burinmu, mutane su yi rayuwa cikin haɗin-kai da annushuwa."

Hamas ta yi tir da Trump

Jim kadan bayan Trump ya kammalan waɗannan jawabai na sa ga 'yan jarida - ɗaya daga cikin jagororin Hamas, Sami Abu Zuhuri ya ce wadannan shawarwari na Trump shirme ya ke yi kuma sun yi tir da hakan.

Ya bayyana matakin da shirin haifar da hargitsi da rashin kwanciyar hankali a yankin.

"Duk irin wadannan shawarwari yunkuri ne na ingiza rikici," a cewarsa, kamar yada kamfanin dillanci labarai na Reuters ya rawaito.

Abu Zuhri ya kuma yi martani kan batun da Trump ke yi cewa a sake wa 'yan Gaza matsugunai a ƙasashe da ke kurkusa, yana cewa wannan wani lamari ne na sake kunna wutar sabon rikici da tashin hankali a gabas ta tsakiya".

"Mutanenmu da ke zirrin Gaza ba su yarda da wannan shiri ba. Abin da ake bukata shi ne kawo karshen mamaya da musgunawa mutane, ba rabasu da yankinsu ba," kamar yada ya faɗawa 'yan jarida.

Kalaman Trump na zuwa ne a yayinda ake cigaba da kokari na shiga tsakani domin kawo karshen yaƙin Isra'ila da Hamas, a mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni.

Ƙasashen Larabawa sun bijire

Saudiyya ta mayar da martani cikin gaggawa kan ƙudurin Trump na shirin ƙwace iko da zirin Gaza, inda ta yi watsi da duk wani yunƙuri na raba Falasdinawa da ƙasarsu.

Saudiyyar ta ce ba za ta ƙulla wata alaƙa da Isra'ila ba har sai an samar da ƙasar Falasdinu.

Ƙasashen Masar da Jordan suma sun bayyana rashin amincewarsu da yunkurin na Trump na tsugunnar da Falasdinawa a ƙasashensu.

A wata sanarwar hadin-gwiwa, shugabannin kasashe daga Gabas Ta Tsakiya da ƙungiyoyi sun yi gargaɗi abin da ka iya biyo bayan wannan shiri, sannan sun ce babu wanda zai aminta da duk wani yunkuri na share wata al'umma ko rabata da asalinta.

Jakadan Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour, ya ce 'yan Gaza na son komawa gidajensu da sake gina yankin, saboda nan ne "asalinsu kuma suna son rayuwa a inda yake nasu."

"Ina ganin lokaci ya yi da ya kamata shugabanni su ke mutunta muradai da fatan Falasdinawa," a cewarsa.