Za a ɓullo da hukuncin ɗauri ga masu ƙona Alƙur'ani a Denmark

Asalin hoton, YAHYA ARHAB/EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK
- Marubuci, Daga Paul Kirby
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Gwamnatin ƙasar Denmark ta ɗauki aniyar haramta ƙona Alƙur'ani Mai Tsarki a bainar jama'a bayan jerin ƙone-ƙonen da suka haddasa yamutsi a ƙasashen Musulmai.
Ministan shari'ar ƙasar, Peter Hummelgaard ya ce irin wannan mataki na ƙona Alƙur'ani ya cutar da Denmark kuma ya sanya al'ummarta cikin hatsari.
Dokar wadda ake shirin kafawa za ta mayar da duk wani matakin wulaƙanta Alƙur'ani ko Littafin Bayabul, matsayin laifi da za a iya hukunta mutum, ta hanyar cin tara ko ɗauri a gidan yari tsawon shekara biyu ko sama da haka.
Gwamnatin ƙasar mai sassaucin ra'ayi ta ce tana son aika wani saƙo ga al'ummar duniya.
Ministan harkokin waje, Lars Lokke Rasmussen ya ce Denmark ta shaida jerin zanga-zanga har 170 cikin 'yan makonnin nan, a ciki har da ƙona Ƙur'anai a gaban ofisoshin jakadancin ƙsashen waje.
Hukumar leƙen asirin Denmark ta yi gargaɗin cewa al'amuran da suka faru a baya-bayan nan sun tsananta barazanar kai harin ta'addanci.
Ita ma ƙasar Sweden mai maƙwabtaka ta shaida jerin ƙone-ƙonen Alƙur'ani kuma jami'an tsaronta sun yi gargaɗin cewa al'amuran tsaro za su taɓarɓare. A watan Yuli, masu zanga-zanga sun cinna wuta kan ofishin jakadancinta a Iraƙi.
Sai dai duka ƙasashen Denmark da Sweden sun jinkirta ɗaukar mataki a kan ƙone-ƙonen saboda dokokinsu na sassaucin ra'ayi a kan 'yancin faɗar albarkacin baki. A shekarun 1970 ne Sweden ta soke dokarta ta haramta saɓo.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Gwamnatin birnin Copenhagen ta yanke shawarar ɗaukar mataki bayan ƙarin ƙone-ƙonen Alƙur'ani a ƙarshen watan Yuli cikin Denmark da Sweden.
Ƙungiyar Ƙasashen Musulmai ta Duniya (OIC) ta yi kira ga mambobinta su ɗauki matakan da suka dace a kan ƙasashen da ake wulaƙanta Alƙur'ani.
Ministan shari'ar ya yi dage a kan cewa ƙudurin canza dokar ba zai shafi furuci ko rubutun bayyana albarkacin baki ko zanen shaguɓe ba. Sai dai ya ce ƙona littattafan addinai ba su da wata manufa sai haifar da ɓaraka da haddasa gaba.
"Wani ginshiƙin al'amari ne ga tsarin dimokraɗiyyarmu cewa mutum na da 'yancin faɗar albarkacin bakinsa," a cewar Mataimakin firaminista Jakob Ellemann-Jensen. "Kuma ya kamata mutum ya riƙa sara, yana duban bakin gatari."
Denmark ba za ta tsaya ta zuba ido kawai ba a lokacin da irin waɗannan abubuwa masu nakasu ga tsaron ƙasar ke faruwa, ya ƙara da cewa.
Firaministan Sweden, Ulf Kristersson, ya ce gwamnatin Stockholm ba za ta ɗauki irin wannan mataki na maƙwabciyarta ba, saboda hakan mai yiwuwa zai buƙaci yi wa tsarin mulkin ƙasar garambawul.
Ministan shari'ar Sweden Gunnar Strommer ya faɗa wa manema labarai cewa shawarar sake nazari kan dokar tabbatar da kwanciyar hankalin jama'a, ta yi daidai.
Gwamnatin ƙasar na son canza dokar domin ta haramta tarukan da za su yi barazana ga tsaron al'ummar Sweden.
Ministoci a Denmark sun ƙuduri aniyar yi wa dokar sauye-sauye ranar 1 ga watan Satumba, sannan su gabatar da sauye-sauyen ga majalisar dokoki don zatarwa kafin ƙarshen wannan shekara.
Ana sa ran, haramcin za a yi shi ne a sashen kundin aikata laifuka da ke hana 'yan ƙasar muzanta wata ƙasar waje, ko tutarta da sauran wani tambarinta.











