Matashiyar da ta rubuta Qur'ani ta hanyar zayyana
Ku latsa alamar wannan hoto da ke sama domin kallon Kur'anin da Fatima ta rubuta.
Fatima Ibrahim Maikarfi mai shekara 23 ta rubuta Alkur’ani mai girma na farko a cikin shekaru biyu da rabi.
Matashiyar wanda take karatun digiri na biyu a fannin kimiyyar siyasa da diflomasiyyar kasashe a yanzu haka ta kware a zayyana, abin da ya sa ma take rubuta Qur’anin da irin wannan salo na zayyana ko kuma ‘Calligraphy’.
An dai haifi Fatima a Najeriya to amma ta tashi a kasar Belgium inda ta samu cikas dangane da karatun addini.
“Mahaifana ne kawai suke koya min abin da Allah ubangiji ya hore musu.”
Sai dai bayan dawowarsu Najeriya ne Fatima ta koma makarantar Islamiyya inda ta nemi a kai ta ajin farko na yara.
Na fuskanci kalubale a ajin nan domin yaran sai su rinka tambaya ta wai da me nake yin sallah saboda sun ji ana biya min Fatiha.”