Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa na soke yin Hawan Sallah - Sarkin Kano na 15 Aminu Ado
Yanzu za a iya cewa al'ummar Kano, jiha mafi yawan al'umma a arewacin Najeriya sun yi ajiyar zuciya bayan da sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya sanar da soke hawan sallah da ya shirya yi bayan azumin Ramadana.
Hawan sallah na daga cikin manyan al'adun Hausa da masarautar Kano ta yi fice a kansa kuma take tutiya da shi.
Sai dai rikicin masarautar na baya-bayan nan ya sanya sanarwar hawan sallah na wannan shekarar ta jefa al'ummar jihar cikin zulumi.
Tun farko an ji gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewa za a yi hawan sallah a Kano, wanda hakan ke nufin Sarki Sanusi II, wanda gwamnatin jihar ta mayar masa da rawaninsa a shekarar 2023 shi ne zai jagoranci hawan.
Sai kuma wasu takardu suka ɓulla na sanarwar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero - wanda gwamnatin Kano ta kwance wa rawani - ya tura wa hukumomin tsaro suka ɓulla, kan cewa zai gudanar da hawan sallah bayan watan azumin Ramadana.
Wannan ya sanya al'umma sun riƙa nuna fargaba kan abin da zai iya faruwa idan dukkanin ɓangarorin biyu suka dage kan ƙudurin nasu.
Sai dai a ranar Laraba, sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya fitar da sanarwar bidiyo inda ya bayyana cewa ya soke hawan sallah da ya shirya yi.
A cikin bidiyon, Aminu Ado ya ce: "Yanayi da muke fuskanta a halin yanzu ya zame mana wajibi mu janye duk wani tsari ko shiri da muka yi na gabatar da haye-hayen sallah."
A cikin wata takardar sanarwa da mai taimaka wa Sarkin Kanon na 15, Aminu Ado ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labarai Abubakar Balarabe Ƙofar Na'isa, ya buƙaci al'ummar jihar su gudanar da bukukuwan sallah cikin lumana.
'Mu masu son kiyaye zaman lafiya ne a Kano'
Aminu Ado ya ce sun soke hawan sallah ne saboda "kiyaye zaman lafiya a garin Kano da kuma ƙasa baki-ɗaya,".
''Yanke wanan hukunci ya biyo nasihohi da muka samu daga malamanmu da muke ganin girmansu da darajarsu da kuma ƙimarsu," in ji Sarkin Kano na 15.
Ya kuma ƙara da cewa sun duba buƙatar janye hawan sallar ne bayan samun kiraye-kiraye daga shugabanni da iyaye waɗanda suke da daraja, da kuma shawara da ƴan majalisarsa.
"Muna fatan janye wannan hawan sallah zai janyo sanadin ƙarin zaman lafiya a garinmu," in ji shi.
Ya ce "hawan sallah ba abu ne na ko a mutu ko a yi rai ba, don haka in zai janyo sanadiyyar tashin hankali - ya zama wajibi mu hakura.
Aminu ya yi kira ga jama'a da su yi amfani da lokacin bukukuwan sallah wajen sada zumunci tsakanin ƴan uwa da abokan arziki.