Wa zai mulki Gaza? Tambayar da kowa ke ƙoƙarin samun amsa a kanta

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images
- Marubuci, Mohamed Morsy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- Lokacin karatu: Minti 8
"Yakin ya kawo ƙarshe." Wannan shi ne yadda Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana sakamakon yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas, wadda aka cimma ƙarƙashin jagorancinsa bayan shekaru biyu na rikici a Zirin Gaza.
Yarjejeniyar ta haɗa da janyewar sojojin Isra'ila daga wasu sassan Gaza da musayar waɗanda ake tsare da su, ciki har da fursunoni da kuma waɗanda ake garkuwa da su.
Sai dai, wasu muhimman batutuwa da aka bayyana a shirin Trump har yanzu ba a warware su ba, kuma hakan na iya kawo barazana ga tsagaita wutar da aka cimma.
Saboda haka, gaba ɗaya makomar Gaza na iya kasancewa cike da ƙalubale, kuma babu tabbacin cewa Hamas za ta ajiye makamai gaba ɗaya.

Asalin hoton, Getty Images
Wa zai jagoranci Gaza ƙarƙashin shirin Trump?
A ƙarƙashin shirin Trump, Gaza za ta samu shugabancin wucin-gadi ta hannun wani kwamitin ƙwararru na Falasɗinawa waɗanda ba su da alaƙa da siyasa wanda zai kula da gudanar da ayyukan yau da kullum na jama'a da kananan hukumomi.
Kwamitin zai haɗa da ƙwararrun ƴan Falasɗinawa da masana daga ƙasashen waje, ƙarƙashin kulawar wata sabuwar hukumar wucin-gadi ta duniya, wadda a cikin takardar shirin aka kira ta "Board of Peace".
Za a sanar da sauran mambobi da shugabannin ƙasashe a hukumance nan gaba, inda ake sa ran tsohon firaministan Birtaniya Tony Blair zai samu wani matsayi a ciki.

Asalin hoton, PA Media
Shirin kuma ya nemi Amurka, tare da haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa da ƙasashen duniya su kafa wata rundunar wucin gadi da za ta samar da zaman lafiya daga ƙasashen duniya.
Za a tura wannan rundunar zuwa Gaza domin horarwa tare da tallafawa rundunar 'yan sandan Falasɗinawa da aka amince da su.
Rundunar za ta ci gaba da aiki tare da haɗin kai da Jordan da Misira, kuma an tsara ta a matsayin mafita ta dogon lokaci ga tsaron cikin gida.
A halin yanzu, Birtaniya da Faransa suna aiki kan wani ƙudurin Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya don kafa wannan rundunar.

Asalin hoton, Dawoud Abu Alkas / Reuters
Shin Hamas za ta ajiye makamai?
Is'raila dai ta dage cewa dole Hamas ta ajiye makamanta.
Bayan komawa Amurka daga Gabas ta Tsakiya, Trump ya ce, "Idan ba su ajiye makamai ba, za mu tilasta musu su ajiye." Kuma hakan zai faru nan ba da jimawa ba watakila kuma cikin tashin hankali.
"Na yi magana da Hamas, na ce, za ku ajiye makamai, ko? sai suka ce "E, ranka ya daɗe, za mu ajiye makamai. Wannan ne abin da suka faɗa mini."

Asalin hoton, Bashar Taleb / AFP via Getty Images
Sai dai, kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito a baya wani jami'in Hamas yana cewa ba su da niyyar ajiye makamai, kuma ba su tunanin yin hakan.
Bayan yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki, AFP ta ruwaito wani jami'in Hamas da bai bayyana sunansa ba yana cewa ƙungiyar ba za ta sanya kanta a mulkin Gaza ba a lokacin samar da gwamnatin wucin-gadi.
Amma jami'in ya faɗa wa AFP cewa Hamas za ta ci gaba da kasancewa muhimmin ɓangare na al'ummar Falasɗinawa.
Ƙungiyar ta nuna shakku game da shiga harkokin ƙasashen waje, musamman rawar da Tony Blair na Birtaniya zai iya takawa.

Asalin hoton, Reuters
A ina mayaƙan Hamas suke yanzu?

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images
Majiyoyin cikin gida sun shaida wa BBC cewa Hamas ta tura dubban jami'an tsaro domin sake karɓe iko da wuraren da sojojin Isra'ila suka fice kwanan nan.
Sai dai Hamas ta musanta cewa tana da niyyar sake samun cikakken iko a Gaza.

Asalin hoton, Getty Images
Waɗanne ƙabilu ne Hamas ke yaƙi da su?
Zirin Gaza da ya sha wahala daga yaƙi ya yi asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.
Bayan fara tsagaita wuta, rikici ya ɓarke tsakanin Hamas da wasu ƙabilu masu riƙe da makamai, inda aka samu kashe-kashe da raunuka da dama.
A yayin tafiyarsa zuwa Gabas ta Tsakiya, Trump ya ce Hamas ta samu izinin gudanar da "ayyukan tsaro na cikin gida" a Gaza.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar na son "dakatar da matsalolin" kuma "an ba su izinin yin hakan na wani lokaci".
A ranar Alhamis, Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa idan Hamas ta ci gaba da kashe mutane a Gaza, abin da ba ya cikin yarjejeniyar, ba za mu samu wani zaɓi ba face mu shiga mu kashe su."
Daga baya ya fayyace cewa "mu" ba yana nufin sojojin Amurka ba ne.

Masanin harkokin yankin Falasɗinawa, Jihad Harb, ya shaida wa BBC cewa zaɓi biyu ne kawai ake da shi game da makomar Gaza: ko dai a bar Hamas ta ci gaba da kula da Zirin tare da izinin Isra'ila, ko a miƙa ikon ga Hukumar Falasɗinawa PA, batun da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ƙi amincewa da shi.
Hukumar PA na da takaitaccen iko a kan yankin Gaɓar Yamma da Korgin Jordan da Isra'ila ta mamaye.

Asalin hoton, Reuters
A watan Yuni, Netanyahu ya ce Isra'ila ta "ingiza wasu kabilu" a Gaza domin su yi adawa da Hamas.
Hamas na zargin waɗannan kabilun da haɗa baki da Isra'ila.
Bayan rahotannin cewa ya amince a bai wa ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Yasser Abu Shabab makamai, Netanyahu ya ce, "Mene ne matsala a cikin yin hakan tunda har za su ceci rayukan sojojin Isra'ila," a wani bidiyo a shafin X.
Kwanan nan, Hamas ta yi arangama da wata ƙungiya, ƙabilar Daghmash, tana zargin wasu daga cikin ƙungiyar da alaƙa da wata tawagar soji da ke biyayya ga Isra'ila.
Mene ne ra'ayin Isra'ila?

Asalin hoton, Abir Sultan / EPA / Shutterstock
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ɗan jaridar Isra'ila, Eli Nissan, ya shaida wa sashen Larabci na BBC cewa ba ya tunanin Hamas na da wata rawa da za ta taka a shugabancin Gaza ba – "ba kawai saboda adawar Isra'ila ba, har ma saboda rashin jin daɗin mazauna Gaza bayan shekaru biyu na yaƙi."
Matsayin hukumar Isra'ila ƙarƙashin Netanyahu shi ne ƙin amincewa da Hamas a shugabancin Gaza.
Isra'ila ma ta ki amincewa da dawowar Hukumar Falaɗinawa (PA) wajen mulkin Gaza.
Wannan matsayi ya ƙara ƙarfi bayan harin Hamas na 7 ga Oktoba wanda ya kashe kusan mutum 1,200, sai kuma yaƙin sojojin Isra'ila wanda, bisa rahoton ma'aikatar lafiyar Hamas, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 67,000.
A cikin wata hira da Fox News a watan Agusta, kafin a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, Netanyahu ya ce Isra'ila na shirin karɓar cikakken iko a Gaza sannan daga baya ta miƙa wa wata "ƙungiyar shugabanci ta Larabawa" da bai ambaci sunanta ba.
Ya ce Isra'ila na da niyyar miƙa mulkin Gaza ga "ƙasashen Larabawa da za su tafiyar da ita yadda ya dace, ba tare da zama barazana gare mu ba, tare da tabbatar da rayuwa mai kyau ga mazauna Gaza."
Nissan ya ce gwamnatin Netanyahu ta ƙi bai wa Hukumar Falasɗinawa damar tafiyar da Gaza saboda yana son guje wa haɗin yankin Gaza da gabar Yamma da Kogin Jordan.

Asalin hoton, Jalaa Marey / POOL / EPA / Shutterstock
Hukumar Falasɗinawa
Kamar yadda aka ambata a baya, Hukumar Falasɗinawa tana da ƙaramin iko ne kawai a yankin gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye.
Shirin Trump yana ganin cewa a ƙarshe hukumar za ta karɓe mulkin Gaza.
A cewar shirin, hakan zai faru ne bayan hukumar ta kammala wani shirin sauye-sauye "kamar yadda aka tsara a wasu tsare-tsare, ciki har da shirin zaman lafiya na Trump na 2020 da kuma tattaunawar zaman lafiya ta Saudiyya da Faransa."
Sauye-sauyen da Amurka ke so ya haɗa da rage zargin cin hanci da rashawa a cikin Hukumar.

Asalin hoton, Reuters
Isra'ila ta mamaye Gaza bayan yaƙin 1967, amma Hukumar Falasɗinu wadda jam'iyyar Fatah ke rinjaye a cikinta – ta karɓi mulkin yankin bayan Isra'ila ta janye sojojinta a 2005, kafin daga baya ta rasa ikon wuri ga Hamas a 2007 bayan rikicin cikin gida mai tsanani.
An kafa jam'iyyar Fatah ne ta hannun wasu mutane da dama, ciki har da tsohon shugaban Hukumar, marigayi Yasser Arafat.
A shekarun 1990s, ƙungiyar 'yantar da Falasɗinu (PLO) ƙarƙashin jagorancin Fatah ta bayyana cewa ta daina amfani da makami wajen yaƙar Isra'ila, tare da goyon bayan kudirin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke neman kafa ƙasar Falasɗinu bisa kan iyakokin da aka tsara tun bayan yaƙin 1967.

Asalin hoton, Paul J Richards / AFP via Getty Images
Shugaba Trump

Asalin hoton, AP
Donald Trump ya sha nanata cewa dole ne a fatattaki Hamas domin kawo ƙarshen rikicin, amma hangen nesansa game da makomar Gaza bayan yaƙi ya riƙa sauyawa da lokaci.
A baya, ya taɓa cewa ana iya mayar da Gaza " wurin yawon shakatawa mai ɗauke da otal-otal na Gabas ta Tsakiya," tare da matsar da mazauna yankin zuwa Masar ko Jordan amma waɗannan ra'ayoyin ba su bayyana a sabon shirin nasa ba.

Asalin hoton, Reuters
Amma mene ne cikakken bayanin? Su waye waɗannan ƙwararrun Falasɗinawa? Kuma me aka sani game da "Majalisar Zaman Lafiya"?
Shirin Trump bai fayyace cikakkun bayanai game da wannan ƙungiyar ƙasa da ƙasa ba, ko da yake kafafen labarai sun ruwaito sunayen wasu baƙin ƙasashe da ake zargin za su shiga ciki. Babu tabbacin hakan a hukumance, kuma Trump kwanan nan ya ce bai tabbatar ko Tony Blair yana da "karɓuwar da zai iya riƙe wannan matsayi ba."

Asalin hoton, BBC News
Masu shiga tsakani

Asalin hoton, Julien De Rosa / AFP via Getty Images
Masar da Qatar waɗanda su ne manyan masu shiga tsakani sun goyi bayan tsarin ƙasa da ƙasa da ake kira "New York Declaration."
Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da wannan shiri a matsayin ɓangare na ƙoƙarin warware rikicin Isra'ila da Falasɗinu da kuma bunƙasa mafitar samar da ƙasashe biyu.
New York Declaration ta tanadi kafa kwamitin wucin gadi da zai kula da harkokin mulki a Gaza ƙarƙashin kulawar Hukumar Falasɗinu. Ta jaddada cewa ikon mulki da aiwatar da doka a duk yankunan Falasɗinu ciki har da Gaza ya kamata ya kasance a hannun Hukumar Falasɗinu.
Wannan hangen nesa ya yi daidai da bayanan jami'an Masar da na Qatar da ke danganta makomar Gaza da kafa ƙasar Falasɗinu.
Ko Hukumar za ta samu damar nuna yadda za ta iya tafiyar da Gaza a karo na biyu, zai dogara da abubuwa da dama da ba ta da cikakken iko a kansu yanzu..







