Mbappe zai koma Chelsea kan kwantiragin shekara daya, Kane zai iya koma wa Bayern Munich

Kylian Mbabbe

Asalin hoton, Getty Images

Dan gaban Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 24, ya shaida wa Chelsea zai iya komawa kungiyar daga Paris St Germain kan kwantiragin shekara daya da sharadin cewa zai koma Real Madrid ne idan kwantiragin ta kare. (Sport - in Spanish)

Manchester United ta shiga cikin sahun masu neman daukar dan tsakiyar Southampton dan kasar Belgium Romeo Lavia, bayan an yi watsi da tayin da Liverpool ta yi a kan dan wasan mai shekara 19. (Independent)

United ta tabbatar da cewa za a samu jinkiri wajen sanya hannun dan gaban Denmark Rasmus Hojlund daga Atalanta har zuwa karshen mako saboda dan wasan mai shekara 20, ya isa United a ƙurarren lokaci maimakon ranar Talata. (Manchester Evening News)

Shi kuwa dan gaban Ingila Harry Kane, mai shekara 30, zai rage wani bangare na albashinsa a Tottenham don ya koma Bayern Munich.(Bild - in German)

Spurs ta kamala yarjejeniyar daukar dan bayan Wolfsburg Micky van de Ven, bayan ta cimma matsaya da dan wasan mai shekara 22. (Talksport)

Kazalika kungiyar na duba yiwuwar kammala sayar da dan tsakiyar Denmark Pierre-Emile Hojbjerg ga Atletico Madrid wadda ta taya shi a kan fam miliyan 30. (90min)

Inter Milan na sha’awar daukar dan bayan Arsenal dan kasar Japan Takehiro Tomiyasu, mai shekara 24, zuwa kungiyar. . (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Barcelona na tattaunawa da Manchester City a kan komawar Joao Cancelo zuwa kungiyar. (Talksport)

Manchester United ta fara tattaunawa da Real Sociedad a kan sayar da dan tsakiyar Netherlands Donny van de Beek, mai shekara 26, wanda hakan zai taimaka mata wajen siyan dan tsakiyar Fiorentina dan kasar Morocco mai shekara 26, Sofyan Amrabat. (Mail)

Blues ta shirya kara wani abu a kan tayin da ta yi wa Caicedo ɗan Brighton, wanda ta taya shi fam miliyan 100. (Sky Sports)