Gangar jikina ce kawai a raye – Ɗan Libyan da ya tsira daga ambaliyar 2023

Abdul Aziz Aldali with his late mother

Asalin hoton, Abdul Aziz Aldali

    • Marubuci, Marco Oriunto
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 5

Bayan shekara guda, har yanzu abin da ya faru na bala'in ambaliyar - da ta shafe birnin Derna na ƙasar Libya tare da kashe dubban mutane - na ci gaba da zama a zukatan waɗanda suka tsira da rayukansu.

“Rayuwarmu ta tsaya cak! Kawai dai gangar jikina ce a raye. Amma bana cikin hayyacina,” in ji Abdul Aziz Aldali, wani matashi da ya tsira da rauwarsa.

Ya rasa mahaifiyarsa da mahaifinsa da wani ɗan'uwansa, lokacin da wata guguwa haɗe da ruwa ta auka birnin da suke zaune ranar 10 ga watan Samtumba.

"Ina ɗaukarsu a matsayin shahidai. Makwabtanmu, a danginmu na Nasser, an samu shahidai 24. Ruwan ne ya cinye su,'' in ji Mista Aldali.

An gina birnin a gefen gaɓar kogin Derna. Akwai ƙoramu guda biyu da ke kwarara ta wasu masatsun ruwa biyu kafin ya tsallaka ta gefen birnin zuwa cikin teku.

Mamakon ruwan sama da rashin gyaran magunanar ruwa, sun tilasta fashewar madatsun ruwan biyu, wanda suka tunbatsa zuwa birnin da misalin ƙafe 2:00 na dare na ranar 11 ga watan Satumba.

“An samu kwararowar ruwa mai ƙarfi zuwa cikin gidanmu, inda a cikin diƙiƙai ya cika hawa biyu na gidanmu, ko'ina ya cika da ruwa babu matsakar tsinke,” in ji Aldali.

“Ni kaina na rikƙa yawo a cikin ruwan yana da watangaririya da ni, na iya ninƙaya, amma ba za ka iya jurewa ruwan ba, sakamakon yadda yake ci gaba da tuɗaɗowa.”

Ana cikin haka ne kuma sai igiyar ruwan ta tunkuɗo shi daga cikin gidan.

“Ina cikin budum-budum a ruwa sai na hango ƙarfen sabis. Ruwan ya turo ni kusa da ƙarfen, sai na riƙe ƙarfen iya ƙarfina.”

An ƙiyasta cewa ruwan da ya mamaye birnin ya kai ƙarfin ton miliyan 24.

“Na ga mutane - ƙananan yarawaɗanda ba za su iya ceton kansu ba, amma ya Allah ya ƙaddara za su rayu,” in ji shi.

Abdul Aziz Aldali's home in Derna

Asalin hoton, Abdul Aziz Aldali

Bayanan hoto, Har yazu ba a sake gina gidan su Abdul Aziz Aldali mai hawa biyu ba.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kamar sauran mazauna birin, Mista Aldali ya fice daga birnin, inda ya yanzu yake zaune a Umm al-Rizam, wani ƙungurmin ƙauye mai nisan tafiyar minti 40 a mota daga kudancin Derna.

Fiye da mutum 5,900 ne suka mutu, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, yayin da har yanzu ba a ga mutum 2,380 ba a birnin wanda mutum kusa 90,000 ke zaune a cikinsa.

To sai dai mazauna birnin sun ce adadin mutanen da suka mutun sun haura wannan adadi.

“Kusan duka abokaina kowa ya rasa ɗan'uwansa. Mutanen birnin Derna sun yi amanna cewa fiye da mutum 10,000 ne suka mutu a ambaliyar,” in ji Johr Ali, ɗan jaridar ɗan asalin Derana, wurin da a yanzu ke zaune a birnin Santanbul na Turkiyya, kuma ke bibiyar lamarin.

Da yawa daga mazauna birnin Derna har yanzu na cikin ɗimauta da damuwa kan halin rashin tabbas da 'yan'uwansu waɗanda suka ɓata ke ciki.

“Na dai ga gawarwakin 'yan'uwana,” in ji Aldali. “Wannan duniya bana jin daɗinta saboda rashin iyayena. A kullum ina roƙon ubangiji ya haɗani da su a gidan aljanna.

Hukumar kula da aikin ceto wadanda suka ɓata ta kwashe aƙalla wata 12 tana tattara samfurin ƙwayoyin halittar gawarwakin da ka samu da nufin gano 'yan'uwan da danginsu.

“Mun tattara gawarwakin, tare da ɗaukar samfurin ƙwayoyin halittarsu daga ƙasusuwa da haƙoransu da bayanan ajalinsu,'' in ji daraktan hukumar Dakta Kamal Sewi.

An gina maƙabrtu na musamman a wajen birnin Derna domin binne waɗanda suka mutu, to amma ba a rubuta sunayen mutanen da aka binne a ciki ba, lamarin da ya sa dubban iyalai fargabar rashin binne 'yan'uwansu.

So-called Korean apartment blocks built in Derna

Asalin hoton, Moataz Fadil

Bayanan hoto, Jami'an birnin a yanzu, na alfahari da sake gina birnin Derna.

Ruwan ya shafe tituna da dama, ana ci gaba da gyaran makarantu da masallatai, tare da fara gina sabbin gidaje.

Gine-ginen Koriya, waɗanda aka yi wa farin fenti a birnin sun zama abin alfahari da jami'an birnin waɗanda ke ƙoƙarin ganin an kammala sake gina birnin.

Wasu iyalai da suka rasa matsugunansu sun sake komawa Derna, inda suka samu garaɓasar karɓar diyyar da ta kai dala 21,000 da bshi mai rangwame.

To sai dai an jinkirta bayar da tallafin kuɗi ga wasu iyalai, tare da ƙoƙarin sake gina birnin saboda bin ƙa'idojin da sharuɗan aikin gwamnati , da kuma zarge-zargen almundahana.

Wata majiya daga sashen binciken ta shaida wa BBC cewa tsarin na janƙafa saboda rashin ƙa'idoji.

“Wasu iyalan waɗanda suka yi tsammanin sun cancanci samun tallafin, har yanzu ba su samu ba,” in ji majiyar.

Akwai kuma fargabar cewa waɗanda ambaliyar ta shafa sun zama waɗanda ake gwagwarmayar iko tsakanin gwamnatocin Libya masu hamayya da juna, wato guda mai shalkwata a birnin Tripoli da kuma ɗyar mai shalkwata a Bengazi da ke gabashin ƙasar.

Belqasem Haftar - ɗa ga Janar Khalifa Haftar, wani babban soja mai ƙarfin faɗa a ji da ke iko da wasu sassan gabashin Libya - na jagorantar aikin asusun tallafin sake gina birnin Derna.

A man reacts as he sits on the rubble of a destroyed building in Libya's eastern city of Derna on 18 September 2023 following deadly flash floods

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Samun gwamnatin adawa a Libya, ya sanya aikin sake gina Derna zama mai matuƙar wahala.

Yayin da aka samu tallafin dala biliyan biyu a asusun, hakan ya bai wa Haftars damar zama mai ƙarfin faɗa a ji da kuma faɗaɗa ikonsa.

"Asusu ne da babu wanda ya san me ke cikinsa,”kamar yadda Anas El Gomati wani mai sharhi, da ke jagorantar cibiyar Sadeq mai lura da al'amuran siyasa da tattalin arziki ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

To sai dai kakakin rundunar soji Libiya na gwamnati Janar Hatars bai amsa saƙon da BBC ta aike masa ba.

Ammma wata majiya da ta buƙaci a sakaya sunatan sakamakon batun ke da sarƙaƙiya, ya ce gwamnan babban bankin Libya ya fice daga ƙasar bayan samun saɓani da gwamnatin ƙasar da ke wurin.

“Kuɗaɗen da aka ware dominsakin gina birnin Derna, sun taimaka wajen kusanta babban bankin a Tripoli ga iyalan Janar Haftar, to sai dai gwamnatin Tripoli na nuna adawa da matakin,” in ji majiyar.

Yayin da rikicin jagoranci da rikice-rkice ke ci gaba da ƙaruwa, al'ummar Derna irin Abdul Aziz na cike da fargabar sake gina rayuwarsu.

“Muna kira ga jama'a da su ci gaba da yi wa mutanen da ke ƙoƙarin sake gina birnin addu'a, domin su gyara mana birninmu ya yi kyau yadda ya kamata. Allah ya taimake su,” in ji shi.

A woman looking at her mobile phone and the graphic BBC News Africa

Asalin hoton, Getty Images/BBC