Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zanga-zangar yaƙin Gaza: Me ake nufi da Intifada?
- Marubuci, By Ghada Nassef
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
An gudanar da gagarumin kame a lokacin zanga-zangar da aka gudanar a jami'o'in Amurka kan yaƙin Gaza.
Saƙonnin da aka wallafa a shafukan sada zumunta game da zanga-zangar da ake tangantawa da Intifada - kalmar Larabci da ke nufin bore.
Akan danganta kalmar ne da lokutan gagarumar zanga-zangar Falasɗinawa kan yi don nuna adawa da Isra'ila.
Da yawa daga cikin saƙonnin da aka wallafa, na tambaya ne ko sabuwar intifada ce za ta samu sakamakon yaƙin Gaza.
Wata kalmar da ake ambatawa ita ce “Fikirar Intifada” da kuma masu cewa a faɗaɗa "Intifada zuwa duniya".
Ɗaliban a jami'o'i sun ƙaurace wa ɗaukar darussa inda suka kafa tantuna domin gudanar da zanga-zanga nuna adawa da ayyukan soji da Isra'ila ke yi a Gaza.
Kawo yanzu dai an kama ɗaruruwan masu zanag-zanga a wasu jami'o'in Amurka.
Jami'o'in sun haɗa da Jami'ar Columbia da ta NYU da ke New York, da Jami'ar California da ke Berkeley da kuma Jami'ar Michigan.
Kwalejin Emerson da Jami'ar Tufts da ke Boston da Jami'ar Fasaha ta Massachusetts da ke kusa da Cambridge, duk sun fuskanci jerin zanga-zangar.
Jami'ar Columbia ta dakatar da ɗalibai da dama, lamarin da ya haifar da kiraye-kirayen haƙura da ɗaukar matakan ladabtarwa ko ma fasa.
Ɗalibai Yahudawa da dama da ke jami'ar sun bayyana damauwarsu kan abin da suka kira barazanar rayuwa a jami'ar
Amma wasu masu zanga-zangar sun ce muzgunawar da ake yi wa ɗalibai Yahudawa ba ta da yawa.
'Yan gwagwarmaya na kiraye-kiraye ga jami'o'in da su ''nesanta kansu daga kisana kiyashi'' tare da daina aaka da kamfanonin da ke ƙera makamai da sauran kamfanonin da ke goyon bayan Isra'ila a yaƙin Gaza.
Me ake nufi da Intifada?
Intifada kalma ce ta Larabci da ke nufin ''bore''. An amfani da kalmar ne wajen bayyana lokutan da Falasɗinawa ke yawan gudanar da zanga-zangar adawa da Isra'ila.
Intifada na farko da aka yi tsakanin shekara 1987 zuwa 1993. An kuma yi na biyu tsakanin 2000 zuwa 2005.
Tun bayan fara yaƙin Gaza na yanzu ranar 7 ga watan Oktoba, aka fara amfani da kalmar ''Intifadar duniya'' a shafukan sada zumunta, inda ake kiran mutane a faɗin duniya da su fito su nuna bore ga Isra'ila.
An kuma yi amfani da wasu kalmomin da suka haɗa da ''Intifadan laturoni'' da ''Intifadar fikira'' tare da kiran a ƙaurace wa kayayyakin Isra'ila.
To me muka sani game da intifadar Falasɗinawa ta farko?
Intifadar farko: Disamban 1987 – Satumban 1993
Bore na farko da Falasɗinawa suka yi ya fara ne ranar 8 ga watan Disamban 1987 a Gaza, a lokacin da wata motar ɗaukar tankar Isra'ila ta faɗi kan ƙananan motoci da ke ɗauke da Falasɗinawa.
Lamarin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa huɗu.
Kafin wannan rana Falasɗinawan da ke zaune a wuraren da Isra'ila ta mamaye sun shafe fiye da shekara 20 a fusace.
Gine-ginen Yahudawa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan aka aka mamaye a Zirin Gaza na ci gaba da bazuwa, yayin da Falasɗinawa ke fama da matsin tattalin arziki tare da fuskantar arangama da sojojin Isra'ila.
Domin mayar da martani kan faɗuwar motar, sai bore ya ɓarka a sansanin 'yan gudun hijira na Jubalia, inda boren ya ci gaba da bazuwa cikin sauri a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Zirin Gaza.
Matasan Falasɗinawa sun yi arangama da sojojin Isra'ila ta hanyar amfani da duwatsu da bom din fetir. Inda sojojin Isra'ila ke amfani da harsashi, lamarin da ya haifar da suka daga ƙungiyoyin duniya ciki har da Majalisar Dinkin Duniya.
Rikici tsakanin ɓangarorin biyu ya ci gaba da zafafa, har zuwa 1993.
Boren ya zo wa mutane da dama da mamaki, ciki har da Isra'ila da ƙungiyar PLO ta Yasser Arafat, wanda a lokacin ke zaman gudun hijira a Tunisiya.
Daya daga cikin manyan abin da intifadar ta haifar shi ne ɗaukar hankalin duniya musamman kan Falasɗinawan da ke zaune a wuraren da Isra'ila ta mamaye, da kuma musamman matakan da Isra'ila ta ɗauka na muzguna wa masu boren.
Wata jimla da aka fi amfani da ita, ita ce jimlar da ministan tsaron Isra'ila na lokacin, Yitzhak Rabin ya yi amfani da ita da ke cewa ''a karya ƙasusuwan'' masu zanga-zangar.
Rabin ya ce harbin Falasɗinawa zai ruguza kimar Isra'ila a idon duniya, saboda harba harsasai a kan Falasɗinawa za sa duniya ta tausaya musu.
A yayin da Intifada ta ci gaba, Falasɗinawa sun daina jifan duwatsu da kwalabe kan sojojin Isra'ila, inda suka koma amfani da bindigogi da gurnetin da aka ƙera a gida da sauran abubuwan fashewa.
Wata majiya a hukumance da masu sharhi na ganin cewa Falasɗinawa sun kashe fiye da dakarun Isra'ila 100 a lokacin Intifadar farko, yayin da sojojin Isra'ila suka kashe aƙalla Falasɗinawa 1,000.
An kawo ƙarshen Intifadar ne a ranar 13 ga watan Satumban 1883, lokacin da Isra'ila da ƙungiyar PLO suka sanya hannu a yarjejeniyar Oslo, wadda ta farfaɗo da yarjejeniyar zaman lafiya.
Isra'ila ta amince da ƙungiyar PLO a matsayin wakiliyar Falasɗinawa, kuma PLO ta ajiye makamai.
Intifada na biyu: Satumban 2000 – Fabrairun 2005
An kira intifada ta biyu da Intifadar al-Aqsa.
Masallacin al-Aqsa shi ne wuri na uku mafi daraja a wajen muslmi, kuma shi ne silar fara rikicin da ya ɗauki shekara biyar ana gudanarwa.
Jaogorin Falasɗinawa sujn yi amfani da sunan wurin ne don nuna girman boren, kuma ba wai rikici hukumomin Falasɗinawa suka shirya ba kamar yadda Isra'ila ta bayyana.
A ranar 28 ga watan Satumban 2000, shugagabn hamayyar Isra'ila, Ariel Sharon da sojoji da 'yan sandan Isra'ila ke bai wa kariya, ya ziyarci masallacin.
Mutum bakwai ne aka kashe a ranar farko na zanga-zangar tare da raunata fiye da mutum 100.
Abin ya fara ne lokacin da wasu Falasɗinawa masu zanga-zanga suka riƙa jifan masu kare Mista Sharon da takalma da duwatsu, lamarin da ya sa wurin ya yamutse ya, tare da da ɓarkewar zanga-zanga a fadin yankunan Falasɗinawa.
Hoton wani ƙaramin yaro mai shekara 12, Mohammed al-Dura da aka harba a lkacin da yake rike da mahaifinsa ya zama ɗaya daga cikin hotunan boren na biyu da suka ɗauki hankali.
Sai dai wani bincike da Isra'ila ta gudanar a 2000 ya ce wani rahoton gidan talbijin na Faransa 'French TV news 'da ya ɗora alhakin kisan yaron kjan sojojin Isra'ila, ba shi da tushe.
Babban bambancin da ke tsakanin boren farko da na biyu shi ne girman arangamar da rikicin da aka samu.
Intifada na biyu ya fi na biyu samun rikici.
Majalisar Dinkin Duniya, ta ce fiye da mutum 5,800 ne aka kashe tun fara Intifada na biyu a watan Satumban 2000 zuwa ƙarshen shekarar 2007, kusan shekara biyu bayan kawo ƙarshen Intifadar.
Duk da cewa abu ne mai wahala a iya tantance alƙaluman mutanen da suka mutu lokacin boren, masu sharhi da dama na ganin cewa Falasɗinawa sun fi 'yan Isra'ila mutuwa a boren.
Hanyoyin da Falasɗinawa ke bi wajen kai hari sun haɗa da harba rokoki da harin ƙunar baƙin wake a kan gine-gine da motocin.
Sai dai duniya na sukar Isra'ila kan hanyoyin da take bi wajen mayar da martania wasu lokuta, to amma Isra'ila ta ce tana mayar da martani ne kan shiryayyun hare-haren makamai.