Kwankwaso ko Abba: Wa ƴan Kwankwasiyya za su bi?

Asalin hoton, BBC COLLAGE
Tun bayan da raɗe- raɗin cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki ba tare da mataimakinsa da kuma jagoran jam'iyyar, Rabi'u Musa Kwankwaso, mabiya Kwankwasiyya a jihar suka shiga wani halin da ba a taɓa gani ba na ruɗewa.
Wata majiya dai ta tabbatar wa BBC cewa ana sa ran gwamnan na Kano, Abba Kabiru Yusuf zai sanar da sauya sheƙar zuwa jam'iyya mai mulki a ranar Laraba lokacin taron majalisar zartarwar jihar.
Gwamnan zai koma APC ne ba tare da mataimakinsa da kuma jagoran NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso ba.
Kawo yanzu dai ba za a iya cewa an raba gari tsakanin Abba da ubangidan nasa, Rabi'u Musa Kwankwaso ba. To bayanai na nuna cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya kaɗu da batun.
A halin yanzu za a iya cewa kai ya rabu sannan mabiya na cikin rudu dangane da wane ɓangaren za su bi, Abba ko Kwankwaso? BBC ta duba wasu abubuwa da ke tabbatar da ɓaraka a tafiyar Kwankwasiyya kamar haka:
Kwankwaso ya gargaɗi masu son sauya sheƙa

Asalin hoton, Kabiru Marmara/Facebook
Jagoran NNPP a Kano kuma tsohon Gwamnan jihar, Rabi'u Musa Kwankwaso ya gargadi 'yan jam'iyyar masu shirin koma wa jam'iyyar APC mai mulki, inda ya ce "babu wani mutum da ya yi butulci kuma ya samu nasara."
A wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ya nuna Kwankwaso yana yin jawabi ga dandazon'yan jam'iyyar cikin harshen Turanci, Kwankwaso ya aike da sako ga masu shirin sauya sheka.
"Na yi mamakin ganin fuskokin wasunku da dama a nan - ku fada wa masu shirin sauya sheka cewa babu wani mutum da ya yi butulci kuma ya samu nasara - Wani yana tunanin ya yi butulci na shekara 10 kuma yana ganin kamar ya ci nasara amma idan ka kalle shi za ka ga ya fadi kasa wanwar…" in ji Kwankwaso.
Ana dai ganin wadannan kalaman tamkar barazana ce ga yan jam'iyyar ta NNPP da ka iya bin zugar gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC.
Ko kalaman da Kwankwaso za su yi tasiri ga magoya bayan nasa na hana bin gwamna Abba? lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan.
Korar shugaban jam'iyyar NNPP na jihar

Asalin hoton, Dungurawa/Facebook
Babban abin da ya faru a ranar Talata shi ne korar shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano, Hashin Dungurawa da shugaban mazaɓarsa ta Gargari da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.
Jam'iyyar ta kori Hashin Dungurawa da aikata laifuka guda shida kamar yadda Shu'aibu Hassan shaida a wani bidiyo da ya yi yayin wani taron manema labarai a Kano.
- Haddasa fitina a cikin jam'iyya ta hanyar raba kan ƴan jam'iyya
- Rashin iya shugabancin a matakin jam'iyya
- Rashin daraja ƴan jam'iyya a matakin mazaɓarsa
- Rashin mutunta mai girma gwamnan jihar Kano
- Yi wa jam'iyya zagon ƙasa
- Korar ƴan jam'iyya masu muhimmanci daga jam'iyya
Bisa waɗannan laifukan ne shugaban jam'iyyar ta NNPP a mazaɓar Gargari ya ce "don haka daga wannan rana ta 30 ga watan Janairu na 2025 ka da ya sake ayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyya na jiha."
Wannan dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan da Hashim Sulaiman Dungurawa ya fitar da wata sanarwa inda yake musanta zargin da ake yi masa tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar na haddasa rikici tsakanin gwamna Abba Kabir da jagoran NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso.
Rabuwar kai a Kwankwasiyya
Kusan za a iya cewa a karon farko an samu wata babbar ɓaraka tsakanin mabiya ɗarikar Kwankwasiyya a Kano, inda wasu bidiyoyi da suka rinka waɗari a soshiyal midiya ak rinƙa ganin masu sanye da jar hula suna sanar da korar junansu daga jam'iyya.
"Duk da cewa har yanzu ba a kai ga fito na fito ba amma dai an kai gaɓar da kowane ɓangare ke cewa ya kori ɗaya ɓangaren daga jam'iyyar wanda hakan yana nuna samun babbar ɓaraka a tafiyar Kwankwasiyya," in ji Dakta Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano.
Kwankwaso ko Abba?

Asalin hoton, Abba/Facebook
Tun a ranar Litinin bayan da batun sauya sheƙar na gwamna Abba Kabir ya riski mabiya na Kwankwasiyya kan su ya kulle saboda tunanin wane ɓangare ya kamata su karkata.
Wasu dai na cewa suna nan a duk inda "jagora" yake sannan suna jiran umarninsa, yayin da wasu kuma ke cewa za su bi Abba ne tun da shi ne gwamna. Sai dai kuma mafiya yawa na kiran jagororin guda biyu da su hada kai su tafi APC tare.
Kusan kowace ƙaramar hukuma a cikin ƙananan hukumomi 44 sun yi taron masu ruwa da tsaki inda suka rinƙa yin kira ga gwamna Abba Kabiru Yusuf da jagoran NNPP, Rabi'u Mus Kwankwaso da su yi aiki tare su kuma ɗauke su zuwa jam'iyyar ta APC.











