Jaruman Kannywood da suka fara tashe a 2025

Jarumai

Asalin hoton, Social media/collage

Lokacin karatu: Minti 3

An saba duk shekara ana ganin sababbin fuskoki a fina-finan Kannywood, musamman tun bayan komawar harkar saka fina-finai masu dogon zango a YouTube.

A farko-farko an fi ganin matasa da ƙananan jarumai a fina-finai masu dogon zango, amma daga bisa manyan jaruman sun shiga ana damawa da su.

Haskar ta fuskanci ƙalubalen kasuwanci tun bayan da kasuwancin CD ya mutu murus, lamarin da ya karya masu shirya fina-finai da dama, kuma har yanzu wasu ba su gama farfaɗowa ba.

Kusan yanzu za a iya cewa masana'antar baki ɗaya ta koma fina-finai masu dogon zango kuma kasuwancin fina-finan ya koma YouTube, lamarin da ya taimaka wajen sake farfaɗo da masana'antar ta koma hayyacinta.

Sai dai duk da kasancewar manyan jarumai sun shiga fina-finan na YouTube ana damawa da su, ana ci gaba da samun sababbin fuskoki da suke samun tagomashi da ɗaukaka cikin ƙanƙanin lokaci.

Wannan ya sa BBC ta rairayo wasu sababbin jarumai da aka bayyana shekarar ne suka fara tashe.

Ikram Labarina

Amina Muhammad Rabi'u

Asalin hoton, Amina Muhammad Rabi'u

Amina Muhammad Rabi'u, wadda aka fi sani da Ikiram Labarina sabuwar jaruma ce da ta taka rawa a fim ɗin 'Labarina' wanda hakan ya sa ake mata laƙabi da Ikram Labarina saboda sunan da ta fito da shi a fim ɗin.

Ƴar asalin ƙaramar hukumar Malumfashi ce a jihar Katsina.

Fim ɗinta na farko shi ne Lubna da aka yi kusan shekara huɗu da suka gabata, amma a cikin 'Labarina' zangon da aka yi a wannan shekarar ne ya haskaka ta a idon duniyar fina-finai.

Ta fito a Jamilun Jiddan da Izzar So da sauran fina-finai da dama.

Safiyya Zaɓi biyu

Safiyya

Asalin hoton, Safiyya_zabi_biyu/Instagram

Asalin sunanta Hassana Ibrahim Rano, kuma ƴar asalin jihar Kano ce.

Fim ɗinta na farko ke nan, wanda tashar Arewa24 ta shirya kuma ta ɗauki nauyi.

Sai dai irin rawar da taka ta sa ana yaba mata, sannan ta bayyana cewa a shirye take ta ci gaba a fitowa a wasu fina-finan.

Aisha Soba

Aisha Soba

Asalin hoton, Aisha Soba

Aisha Soba jaruma ce ita ma tauraronta ya fara haskawa a wannan shekarar ta 2025.

Ta fito a wasu fitattun waƙoƙi irin su 'Makauniya' wadda Auta MG ye rera, kuma kamfanin Arewa Medium ya ɗauki nauyi, inda ta fito a matsayin makauniya a bidiyon waƙar.

Ɗanbaiwa Zaɓi biyu

ABBA SBOY

Asalin hoton, ABBA SBOY/Facebook

Ɗanbaiwa jaruma ni da ya ƙara samun ɗaukaka a shirin 'Zaɓi Biyu' na tashar Arewa24.

Asalin sunansa Abba Sboy, amma ya fito ne a matsayin Mansur Ɗanbaiwa a shirin mai dogon zango

Ya taka rawa a fim ɗin 'Kwana 90' inda ya fito da sunan Abba John, sannan ya fito a matsayin Sameer a shirin 'Labarina.'

Sai dai daman an san fuskarsa a Arewa24 bayan fina-finai.

Amina Lulu

Amina

Asalin hoton, Kinlulu/Instagram

Amina Shehu Lulu ko kuma Amina Lulu a taƙaice matashiyar jaruma ce da tauraronta ya ƙara fitowa fili a wannan shekarar da muke ban-kwana da ita ta 2025.

Jarumar ta taka rawar gani sosai a fim ɗin 'Da na sani' na Taskar Kannywood wanda forodusa Abdul Amart ya shirya, inda ta fito a matsayin matar Aminu Momoh mai son wasa da shagwaɓa.

Sai dai ba shi ba ne fim ɗinta na farko kasancewar ta fito a wasu fina-finan daban, amma fim ɗin na kamfanin Abnur ya ƙara fito da basira da ƙwarewar jarumar a harkar fim.