Fasahohin zamanin da za su yi tashe a 2025 a fagen AI da Kirifto

Asalin hoton, Getty Images
An yi musayar sulallan intanet na Bitcoin a 2024 da suka kai yawan $100,000 sannan manhajojin ƙirƙirarriyar basira na AI sun samu wurin zama a aljihu da wayoyin mutane. Yanzu abin tambaya shi ne, mene ne kuma zai fito a sabuwar shekarar 2025?
Ben Morris, editan BBC na hada-hadar fasaha da kuma Zoe Kleinman, wanda shi ma editan harkokin fasahar ne sun yi bincike dangane da manyan fasahohin da za su karaɗe shekarar da muke ciki.
Ben Morris, Editan BBC na hada-hadar fasahar zamani
A lokacin da shekarar 2022 ta zo ƙarshe, hada-hada dangane da kuɗin intanet na kirifto ta ɗan samu tasgaro.
Ɗaya daga cikin kamfanonin da jama'a suka fi hada-hadar kuɗin kirifto da shi, shi ne FTX wanda ya karye da kudin jama'a $8bn da aka kasa ganowa.
A watan Maris 2024, aka yanke wa ɗaya daga cikin shugabannin kamfanin, Sam Bankman-Fried hukuncin zaman gidan kaso na shekara 25 bisa tuhumar zambatar abokan hulɗar da masu zuba jari.
Dambarwar ta sanya tsoro ga baki ɗaya masana'antar ta hada-hadar kirifto.
Alamu na nuna cewa kudin kirifto zai ci gaba da yin tasiri inda jama'a ke zumudin shiga amma ta taƙaitacciyar hanya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
To amma bayan wasu ƴan makonni tare da yadda harkar kirifton ta sake samun tagomashi, sai kwatsam aka samu labarin nasarar zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump a ranar 5 ga watan Nuwamba.
Tunanin shi ne zai bai wa tsarin kudin kirifto dama, kuma alamu na nuna yiwuwar hakan.
A farkon watan Disamba, Donald Trump ya ce zai naɗa tsohon shugaban hukumar hada-hadar hannun jari, Paul Atkins a matsayin mutumin da zai jagoranci hukumar da za ta sanya ido kan hada-hadar kuɗaɗen na kirifto.
Ana dai yi wa Mista Atkins kallon mutumin da ke goyon bayan harkokin kudin kirifto fiye da mutumin da zai gada, Gary Gensler.
Sanarwar da Donald Trump ya yi kan naɗa Paul Atkins, ta ƙara darajar kuɗin kirifto inda hada-hadar ta kai yawan $100,000.
"Nasarar da Trump ya samu na nuni da cewa za a samu sa-ido na musamman a harkar. Za a samu damar kawar da wasu dokokin da ke kawo tasgaro ga bankuna da sauran hukumomi masu hada-hadar kuɗi," in ji Geoffrey Kendrick, shugaban sashen binciken kadarorin digital a Standard Chartered.
Mista Kendrick ya nuna cewa wani sharaɗi da hukumar hada-hadar hannun jari ta Amurka ta fitar mai suna SAB 121, wadda ta fara aiki a 2022 ta sa bankuna da hukumomin kuɗi a cikin tsaka mai wuya wajen gudanar da harkokin kuɗaɗen kirifto.
Wannan mataki dai zai taimaki Trump domin cika alƙawarinsa da ya yi a watan Yuli wajen mayar da Amurka cibiyar hada-hadar kuɗin kirifto ta duniya.

Asalin hoton, Getty Images
AI na neman zama na ɗaiɗaikuwa - Zoe Kleinman, Editan BBC ba harkokin fasaha
A daidai lokacin da manhajojin ƙirƙiriyar basira ta AI ke kara samun tagomashi a wayoyinmu - kamfanonin Apple, Google da Samsung sun ƙaddamar manhajojin da ka iya gyara hotuna da fassara da kuma neman shafukan intanet - muna farkon wani zamani ne da ƙirƙirarriyar basira ta zama wani ɓangare na rayuwarmu sannan ke ci gaba da taimaka wa ɗaiɗaikunmu.
Amma fa sai idan mun yarda da faruwar hakan , saboda
Misali, idan muka ɗauki jadawalin tsare-tsaren abubuwan da mutum ke yi a rana. Yanzu manhajar ƙirƙirarriyar basira ta AI za ta tsara maka duk abubuwan da za ka yi a rana idan dai ka bari ta samu bayanan naka. To amma abin tambaya shi ne yaya hakan za ta kasance?
Domin zama mai cikakken amfani, za ta san mutumin da kake gudun haɗuwa da shi, ko kuma alaƙar da kake so ta zama ta sirri?
Kana so ta ba ka taƙaitaccen bayani dangane da lokutan bayar da shawarwari, ko kuma lokacin ganin likita?
Abu ne da ya shafi rayuwarka sannan ka iya zama maras daɗi sannan kuma a lokaci guda mai amfani idan aka samun wata ƴar matsala aka kwarmata bayanan. Shin ka aminta da manyan kamfanonin fasahar zamani da irin waɗannan bayanan naku?
kamfanin Microsoft na ta ƙoƙari a wannan ɓangare. Ya samu kansa a matsala a 2024 lokacin da ya nuna yadda za a yi amfani da wata manhaja mai suna Recall, wadda ta ɗauki hotunan komfutocin kan tebur a kowace daƙiƙa, domin taimakon masu amfani da ita gano abubuwan suka gani amma suka kasa tuna wurin da suka gan su.
Yanzu kamfanin ya yi wasu sauye-sauye ga kayansu - waɗanda ba a ƙaddamar ba.
"Ina tunanin cewa muna shiga wani sabon zamani mai ɗorewa, mai juriya, mai bayar da abokan tarayya a rayuwarku ta kullum," kamar yadda shugaban AI na kamfanin Microsoft, Mustapha Suleyman ya shaida min a baya-bayan nan.
Duk da cewa akwai ƙalubale, Ben Wood, jagoran masu bincike a kamfanin fasaha na CCS Insight, ya yi zaton cewa za a samu ƙarin manhajojin AI da za su dace da buƙatun ɗaiɗaikuwar jama'a a 2025.
"Za a ci gaba da samar da sauye-sauye ta hanyar fito da hanyoyin bayanai da suka haɗa da adireshin imel da saƙonni da kundi da ma tattaunawa a kafafen sada zumunta.
"Wannan zai bai wa kirƙirarriyar basira ta AI damar sauyawa zuwa ga muradun ɗaiɗaikuwar mutane kamar tsari da buƙata da abin da suka fi so," kamar yadda ya ce.
To sai dai Mr Wood ya amince da cewa bai wa AI dama a kan bayanan mutum shi ne babban matakin rayuwa da za a shiga.

Asalin hoton, Getty Images
Zamanin mallakar Bayanai - Ben Morris, editan harkokin fasaha
Daidai yawan kuɗin da aka zuba a harkar ƙirƙirarriyar basira, zai dace da irin yawan cibiyoyin bayanan da ake buƙatar ginawa.
Horarwa da tafiyar da fasahar AI na buƙatar ƙwarewa sosai a na'urar komfuta sannan aikin na tafiya ne yadda ake so da wasu na'urori masu ɗankaren gudu da rumbunan da ke bayar da sabis.
Ana sa ran a tsawon shekaru biyar masu zuwa kamfanoni kamar Google da Microsoft da Meta za su iya zuba jarin kuɗi masu yawan dala tiriliyan ɗaya wajen samar da cibiyoyin tattara bayanai, kamar dai yadda kamfanin CCS Insights ya nuna.
A nahiyar Turai kaɗai, daga shekarar 2024 zuwa 2028, akwai yiwuwar samun cibiyoyin bayanai da kaso 9 cikin 100 a kowace shekara kamar yadda kamfanin Savills ya sanar.
To sai dai irin waɗannan gine-gine bai zama lallai a gina su a birane kamar London da Franfurt da Amsterdam ba saboda tsadar fili da wutar lantarki wani abu da zai saka masu zuba jari yin duba zuwa wasu sassan duniya.
Akwai yiwuwar gina cibiyoyin a biranen Burtaniya kamar Cambridge da manchester da Birmingham.
Har wayau, za a iya gina cibiyoyin a birane irin su Prague da Genoa da Dusseldorf da Milan duka a nahiyar ta Turai.

Asalin hoton, Getty Images
Wani abun da zai fice daga cibiyoyin bayanan da za a iya ginawa, shi ne samun wata na'ura daga Nvidia, kamfanin da ya mamaye kasuwar ƙananan na'urorin duniya da ake amfani da su a fasahar AI.
Akwai hasashen cewa kamfanin zai fara samar da na'urar Blackwell da aka ƙaddamar a watan Maris 2024 da yawa a 2025.
Ita wannan na'ura ta Blackwell za ta bai wa kamfanoni horas da AI domin yin aiki sau fiye da 30 idan aka kwatanta da yadda na'urar ke yi yanzu, kamar yadda Vivek Arya, babban masani kan na'urori a Bank of America Securities.
Akwai hasashen cewa kamfanonin Microsoft da Amazon da Meta da Coreweave ka iya zama sahun farko na samun na'urar Blackwell mallakar Nvidia.
To amma sauran abokan hulɗar kamfanin ma ka iya fafutuka wajen ganin su ma sun











