Da gaske an yi Sarauniya Amina ta Zazzau?

    • Marubuci, Daga Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 6

Sarauniyar Zazzau Amina na ɗaya daga cikin sarakunan da aka taɓa yi a ƙasar Hausa, waɗanda hikayoyi da labarai suka ruwaito. Kodayake wasu masanan na cewa ba sarauniya ba ce.

Akasarin kundayen da masu bincike suka rubuta a ƙasar Hausa da sauran sassa sun bayar da tarihin Sarauniya Amina a matsayin basarakiyar da ta mulki Masarautar Zazzau, wadda yanzu ke cikin jihar Kaduna a arewacin Najeriya.

Duk da cewa labarinta hikayoyi ne da ba su da tabbas, marubuta da dama sun tafi a kan cewa an haife ta ne a shekarar 1533, kamar yadda Daniel Iweze da Umasom Amos na Jami'ar Benin suka bayyana a maƙalarsu mai taken Matriarchs in African Societies: Examining the Roles of Queen Amina of Zazzau and Queen Idia in State and Empire Building in Pre-Colonial Nigeria.

Mahaifiyarta ma basarakiya ce mai suna Sarauniya Bakwa Turuku. Sauran 'yan'uwan Amina namiji ne mai suna Karama, da kuma mace Zariya.

Marubutan sun ruwaito labaran da ke bayyana cewa Sarauniya Amina ta mulki Masarautar Zazzau tsawon shekara 34 kafin mutuwarta a shekara ta 1610.

Rayuwar Sarauniya Amina tana yarinya

Hikayoyi sun ce tun tana 'yar ƙaramarta Amina ke da sha'awar shiga fada, inda take rarrafawa zuwa fadar domin zuwa wajen kakanta Sarki Zazzau Nohir.

Saboda ƙaunar da yake yi mata, yakan ɗauke ta ya ɗora ta kan kujera a gefensa a lokuta masu muhimmanci, kamar ganawa da masu mulki da sauran sarakuna.

Ta girma da ƙaunar siyasa duk da yadda mahaifiyarta Bakwa Turuku ta dinga ƙoƙarin saita ta kan bin hanyoyin matantakarta.

Kazalika, an ce tana sha'awar ɗaukar takobi tun tana ƙarama, inda har ta saba hulɗa da dakaru da samun horo, abin da ya kai ta ga zama jaruma.

An hakaito cewa tun tana shekara 16 mahaifiyarta ta zama sarauniya a Zazzau, inda ta naɗa ta magajiya mai jiran gado kuma aka ba ta bayi 40.

Bajintar da ta sa Amina ta gaji sarauta

Mahaifiyar Amina ta mutu a wuraren shekarun 1566, kuma duk da cewa Amina ce babba ɗan'uwanta Karama ne ya gaji sarautar saboda yadda mutanen masarauta suka nemi a yi hakan.

Yayin mulkin ɗan'uwan nata, Amina ta sha nuna bajinta.

Lokacin da wani sarki mai suna Karmajeji ya kai wa masarautar Zazzau hari kuma ya yi nasara saboda fasahar da ya ƙirƙira ta amfani da hular kwano, Amina ta shiga yaƙin kuma saci irin wannan fasahar, inda daga baya ta jagoranci ƙera hulunan kwano ga dakarun masarautar.

Sakamakon haka ne rundunar Amina ta yi nasara a hare-haren da ta dinga kaiwa ƙasashe maƙwabta kamar Nupe, da Kwararafa, da Katsina, da Narasarawa. Irin wannan bajinta ta sa ake yi wa Amina laƙabi da Yar Bakwa Ta San Rama.

Karama ya yi mulki na tsawon kimanin shekara 10. Bayan mutuwarsa ne kuma aka zaɓi Amina a matsayin sarauniya a shekarar 1576 saboda ƙwarewarta a fannin siyasa da jagoranci.

Gudunmawar da Amina ta bai wa Masarautar Zazzau

An ruwaito cewa Sarauniya Amina ta bayar da gudummawa sosai wajen gina masarautar Zazzau bayan hawanta mulki, ciki har da cibiyoyi irin na siyasa da harkokin mulki a ƙasar Hausa.

A lokacin mulkinta, an shiga da kayayyaki kamar gishiri daga Sudan zuwa ƙasar Hausa, inda aka yi cinikin ta hanyar musaya da bayi da kuma hatsi.

Duk garin da ta ci da yaƙi sai ta bayar da umarnin gina ganuwa. An ce ta gina Ganuwar Amina wadda aka ce har yanzu akwai ɓurɓushinta a birnin Zariya.

An ce ta haɗa dakaru da suka kai 20,000 waɗanda da su ne ta yi nasarar kame garuruwa da yawa, waɗanda suka haɗa da Katsina, da Kano, da Bauchi, da Rano, da Gobir. Akwai kuma garuruwan da ba na Hausawa ba kamar Kwararafa, da Nupe, da Yawuri.

An ce nasarorin da ƙasar Zazzau ta samu a ɓangaren kasuwanci sun samu ne saboda yadda ta dinga cinye garuruwa da yaƙi. Hakan ya sa Zazzau ta zama cibiyar kasuwanci a kudancin ƙasar Hausa, inda kayayyaki kamar ƙarafa da gishiri da goro da tufafi da fatu suka shahara.

Haka nan, an ce Amina ce ta bijiro da kakkafa sansanonin soja a bayan ganuwar da aka giggina. Ruwayoyi sun ce hakan ya taimaka mata wajen samun nasarori a yaƙe-yaƙen da ta gwabza.

A ɓangaren addini, an ce ta ƙarfafa wa Musulmai da dama gwiwar kai ziyara Zazzau daga Kano da Timbuktu na ƙasar Mali.

Akwai 'yar taƙaddama game da wuri da Sarauniya Amina ta mutu. Yayin da wasu ke cewa ta rasu a Atagara, wasu na cewa ta mutu ne a yaƙin Dekina a shekarar 1610.

Dalilin da ya sa Amina ba ta yi aure ba

Kusan duka labaran da ake ruwaitowa game da rayuwar Sarauniya Amina na cewa ba ta yi aure ba.

Farfesa Abdullahi Musa Ashafa na Jami'ar jihar Kaduna ya ce abin da ake hakaitowa na nuna cewa ba ta yi auren ba ne saboda zaɓinta.

"Abin da ya sa ba ta yi aure ba, kamar yadda ake hakaitowa, ba zai rasa nasaba da cewa ita mayaƙiya ba ce," a cewarsa.

"Wani ƙaulin kuma ya ce takan yi mu'amala da wasu maza, amma kuma sai ta halaka su bayan kwanciya da su."

Mece ce gaskiyar sarautar Amina?

Yayin da wasu masana da dama ke ganin da gaske an yi Sarauniya Amina a tarihi, wasu na ganin ba a yi ta ba.

Hatta waɗanda suka yarda an yi ta suna cewa 'yar sarki ce kawai mai jarumta amma ba sarauta ta yi ba.

"Abin da masana tarihi da al'adar Hausawa suka yi ittifaƙi a kai kusan shekara 300 shi ne, Amina ba sarauta ta yi ba," a cewar Farfesa Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na sashen harsunan Najeriya a Jami'ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sokoto.

"'Yar sarki ce kawai," in ji shi.

Shi ma Farfesa Abdullahi Musa Ashafa ya jaddada wannan ra'ayin, sai dai ya ce an fi ƙarfafa cewa an yi ta da gaske saboda zuwan labarin a littafin Muhammadu Bello, ƙanin Shehu Danfodiyo.

"Abin da ya sa ake yarda da tarihin cewa ta yi zamani shi ne yadda Muhammadu Bello ya kawo tarihinta a littafinsa mai suna Infaƙul Maisur."

Me ya sa ake shakku kan labarin sarautar Amina?

Masana tarihi da dama na nuna shakku game da labarin sarautar Amina ta Zazzau ne ta hanyar ɗiga ayoyin tambaya da ke da alaƙa da tarihi da kuma al'adar Hausawa.

Farfesa Aliyu Bunza ya zayyana dalilan da suka sa ake shakku kan zamanin Amina, waɗanda ya ce masana ne suka yi nazari:

  • Akwai ƙabilu da yawa da suka rayu a Zazzau, kamar 'yan ƙasar Mali, waɗanda su ne suka fara kawo Musulunci ƙasar Hausa. A matsayinsu na Musulmi, shin zai yiwu su naɗa mace ta mulke su?
  • Daga cikin sarakunan Zazzau akwai Barebari. Sai a duba ƙasarsu ta asali Borno a gani, shin sun taɓa saka wata mace sarauniya?
  • Akwai Katsinawa a sarakunan Zazzau. Da aka duba sai aka ga babu wata sarauniya da aka taɓa yi a Masarautar Katsina.
  • Akwai Fulani a cikin sarakunan Zazzau. Shi ma babu binciken da ya tabbatar akwai wata Bafulatana da aka taɓa yi sarauniya.

Farfesa Bunza ya ce sarakunan Zazzau sun fi na sauran ƙasar Hausa ilimi a tarihi.

"A Zazzau aka fara samun sarkin da ke koyarwa. Ba su taɓa naɗa sarki jahili ba. Saboda haka, mu ɗaliban ilimi muke ganin da wahala malami ya yarda mace ta zama sarauniya," kamar yadda ya bayyana.