Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Tarihin Hausawa na Bayajidda ƙarya ne'
Shugaban Jami'ar Koyo daga gida ta Najeriya, NOUN, farfesa Abdallah Uba Adamu, ya ce, tarihin Hausawa da wasu ke dangantawa da Bayajidda shafcin gizo ne.
Ya kuma ce duk mutumin da ba shi da alaka da garuruwa guda bakwai da ke arewacin Najeriya, to ba Bahaushe ba ne. Sai dai a kira shi mai magana da yaren Hausa.
Garuruwan dai su ne birnin Kano da Katsina da Daura da Zazzau da Rano da Gobir da kuma Biram.
Farfesa Abdallah ya kuma yi watsi da batun da wasu manazarta ke fadi cewa Hausa yare ne ba kabila ba, a inda ya ce Hausawa na da daulolinsu.
Ga dai abin da farfesa Abdallah Uba Adamu ya shaida wa Ibrahim Isa, bayan gabatar da mukala kan cikar BBC Hausa shekara 60 da kafuwa.