Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masarautu mafiya girman hawan sallah a ƙasar Hausa
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist (Multimedia)
- Aiko rahoto daga, Abuja
Hawan sallah dai wata daɗaɗɗiyar al'ada ce a tarihin masarautun ƙasar Hausa.
Sarakunan ƙasar Hausa sun fara yin hawan sallah ne bayan zubar da addinin gargajiya tare da rungumar addinin Musulunci.
Masarautu da dama ne ke gudanar da bikin hawan sallah ko dai ƙarama ko kuma babba inda a lokacin ake samun jama'a, da suka hada da manya da yara, maza da mata har da ma baƙi daga faɗin Najeriya da wasu ƙasashen, suna tururuwa domin kallon hawan.
Shi hawan sallah biki ne da sarakuna ke gabatarwa. A Ƙasar Hausa, a kan fara bikin hawan sallah tun daga filin idi.
BBC ta yi nazari kan girman hawan sallah a wasu manyan masarautun ƙasar Hausa kamar Kano da Zazzau da Bauchi da Daura da kuma Sokoto.
End of Labari mai alaƙa...
Masarautar Kano
A wannan Masarauta ta Kano, Sarkin Dogaran Kano, Muhammadu Sunusi ya ce akwai hakimai da dama da suke yin hawa kuma a baya-bayan nan an ƙara yawansu tun daga Makaman Kano da yake fara fita zuwa Yariman Kano wanda shi ne na ƙarshe.
A baya dai Hakimin Ƙaraye ne yake zuwa a ƙarshe kafin a raba Masarautar zuwa gida biyar - Masarautar Kano da Masarautar Ƙaraye da Masarautar Bichi da Masarautar Gaya da kuma Masarautar Rano.
Sai dai ya ce a yanzu, Masarautar Kano na da hakimai 50 kuma duk mai iko a cikinsu yana hawan sallah, idan kuma hakimi ba zai iya hawa ba saboda dalili na rashin lafiya, yana iya wakilta wakili da zai yi hawan a madadinsa.
Game da adadin dawakan da ake hawa da su a bikin sallah kuma, Sarkin Dogaran ya ce babu wani ƙayyadadden adadin dawakan – ya danganta da arzikin hakimi ko ikonsa.
Ujudud Sanusi, mataimaki ga Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi ƙarin bayani inda ya ce a wannan karon, an yi gyara a tsarin hawan inda a bana, hakimai 55 ne za su yi hawa a wannan masarauta sannan dawakai 2,229 za a fita da su hawa idan an haɗa da dagatai 350 lokacin ƙaramar sallah kuma kowanne hakimi yana da aƙalla dawaki 15.
Ya ce a sabon tsarin, Makaman Kano ne farkon fita sai Zannan Kano ya zama hakimi na karshe a jerin hawan bana.
Ita kuwa rundunar Sarki wadda ake cewa Giwar Sarki tana ƙunshe da dawaki 1,099 - ƴan sulke suna da dawaki 250 sai ƴan lifidi masu 750 da ƴan bindiga mutum 150 sai masarta guda 12 da doki ɗan gaban taguwa guda ɗaya sai taguwa ɗaya da ƴan kagira mutum 100 sai rumfar masu dawaki 24 da zagage mutum 12 akwai kuma banga-banga masu dawaki 50.
Sai tambari rakuma 4 da dawakin zage12 waɗanda ake cewa amaren dawaki wanda Sarki zai iya sauka daga kan dokinsa ya sauya da wani ko don gajiyar dokin ko kuma ana buƙatar doki mai sauri sai majasiddida tawagarsa dawaki 5 da dagatai dawaki 350 idan da ƙaramar sallah ne sannan da babbar sallah dagatai ba sa zuwa.
Masarautar Zazzau
A cewar, Shugaban Gidan Tarihi na Arewa (Arewa House), Shuaibu Shehu Aliyu, duk wani hakimi da ya cancanta yana hawan sallah a wannan masarauta - ko yana da ƙasa ko ba shi da ƙasa saɓanin baya da dole sai hakimi yana da ƙasa.
Ya ce hawan sallah a ƙasar Zazzau ya kasu gida uku - hawan safiyar sallah da hawan bariki da hawan daushe.
Hawan Safiyar Sallah: A wannan hawa, Sarki yana tafiya da dawowa a kan dawakai saɓanin lokacin baya da ake hawa mota.
Hawan Bariki: Ana yin wannan hawa bayan kwana ɗaya da sallah. Sarki yana hawa daga fada zuwa GRA zai je ya gaishe da gwamna kuma hawan ya samo asali tun zamanin Turawan Mulkin mallaka kuma har yanzu ana yin haka.
Hawan Daushe: Hawa ne mai tarihi a ƙasar Zazzau. Ana yinsa bayan kwana biyu da sallah. Ya kuma ƙunshi dukkan hakimai. Hawa ne da ake baje ƙwanji a gwada gasa ta ado. Yana daga cikin babban hawa na Zazzau.
Game da yawan dawakan da ake tsammanin kowane hakimi ya yi amfani da su kuwa, shugaban gidan tarihin ya ce "ba a so kowane hakimi da zai yi hawa, ya yi tawaga da dawakai ƙasa da goma, amma daga 10 har zuwa ɗari ya halasta - ya danganta da ƙarfin hakimin da zai yi wannan hawa".
Shuaibu Shehu Aliyu ya bayyana cewa rundunonin da ke marawa Sarki baya yayin hawa suna da yawan gaske.
Ya lissafo su kamar haka: ƴan buwaran Sarki da zagagen Sarki - masu tafiya a ƙasa da ƴan sulke da ƴan kwalkwali da ƴan bindiga da ƴan karma da ƴan polo da dawakin zage - waɗanda suke tafiya kan fararen dawakai akwai kuma ƴaƴan Sarki sai sauran hakimai su biyo baya.
Waɗanda kuma suke fara shiga gaban Sarki mutane 15 ne "amma wanda yake fara shigewa shi ne Waziri kuma na ƙarshensa shi ne Sarkin Gwandu." in ji Shuaibu Aliyu.
Ya ce Sarkin Gwandu shi ne yake taho da sauran tawaga da sauran al'umma waɗanda za su biyo shi har zuwa wajen da za a gama hawan da ake a ranar.
Daraktan Arewa House ya kuma ce rundunar Sarki ta ƙunshi Sarkin Yaƙi da Sarkin Tsakargida da kuma Ja Gaba.
Masarautar Daura
A wannan Masarauta kuwa, akwai Hakimai masu ƙasa guda 18 wadanda dole ne su taya Sarki Hawan Sallah.
Haka kuma ya zama dole, su sa wakili idan sun samu wani uzuri.
Bayan su akwai Hakiman Karaga wadanda bisa ra'ayinsu suna iya Hawan Sallah.
A cewar Galadiman Daura, Ahmadu Diddiri Ahmed, ya ce adadinsu yana da wahala domin ba dukkan Hawa suke yi ba akwai ma wadanda sai Sallah Gani kadai suke hawa, inda ake samun aƙalla Hakiman Karaga 10 suna hawa.
Game da yawan dawakan da ake hawa da su kuwa, a Masarautar Daura, babu adadin yawan dawaki, sai dai ana ƙiyasta 100 a tawagar Sarki, haka mafi ƙaranci dawakai 15 ga tawagar Hakimi.
Cikin rundunonin tawagar Sarki akwai:-
• Yan Lifida (a dawaki)
• Yan baka da yan bindiga (a kasa)
• Yan Jibga (a dawaki)
• Yan Kwalkwali (a dawaki)
• Yan Sulke (a dawaki)
• Yan Garkuwa (a dawaki)
• Yan Rabi-rabi (a kasa)
• Dogarai (a kasa)
• Makada Yan Kasa
• Zagage (a kasa)
• Giwar Sarki
• Makada da Yan Tambura (a dawaki da rakuma)
• Dawakan Zage
Ƴan Lifida sune tawagar farko da ke marawa Sarki baya sai kuma Dawakan Zage a karshe.
Ahmadu Diddiri Ahmed ya ce bayan tawagar Sarki, sai Hakimai suna bi baya, kowa da tawagarsa.
Tawagar Galadiman Daura ita ke bin tawagar Sarki, sai Kauran Daura shi ne na karshe bayan dukkan tawagogin Hakimai.
Sai Ƙaura ya kai jafi hawa ya kare, babu sauran Hakimin da zai kawo jafi.
Masarautar Sokoto
A Masarautar Sokoto, hakiman da ake sallah da su sune waɗanda suke cikin garin Sokoto da kuma maƙwabtan garuruwa amma sauran hakimai na zama a garuruwansu su yi bukukuwan sallah.
Sai dai a cewar, Haruna Sambo Wali, mai bincike a kan Tarihin Daular Usmaniyya da ƙasar Hausa, ya ce cikin masu naɗin Sarki da suke shigowa a yi hawa da su akwai– Arɗon Shuni wanda shi ne Hakimin Shuni.
Bayan shi kuma akwai Sarkin Adar da Ɗunɗaye – Hakimin Ɗunɗaye da shi ma yake shigowa cikin Sokoto sai kuma Baraden Wamakko da dukkansu suna daga cikin masu naɗin Sarki.
Haruna Sambo Wali ya ƙara da cewa ko da hakiman sun shigo cikin gari, ba hawa suke yi ba, “suna shiga ne a motocinsu, su je masallacin idi, a gama su biyo mai alfarma, a zo fada a yi gaisuwa a yi jawabai sannan su koma gida.”
A cewarsa, hakimi ɗaya tilo da yake hawa shi ne Mai Girma Dallatun Sokoto, shi a cikin gari yake kuma shi ne Hakimin Tudunwada. “Amma har Sarkin Yaƙin Gagi da yake yana cikin Sokoto, shi ba ya cikin waɗanda suke shigowa cikin gari, a unguwarsa yake sallah.”
Ya ce a Sokoto, hakimai sune Uban Ƙasa a Sokoto saɓanin yadda yake a wasu masarautun ƙasar Hausa. Ya ce akwai banbanci kasancewar a Sokoto, suna bin tsarin Musulunci ne ba al’ada ba.
Dangane da adadin dawakan da ake amfani da su a lokutan hawan sallah kuwa, Haruna Wali ya ce suna da yawa amma ba su kai na wasu wuraren ba saboda “ba kowa ne yake hawan sallah ba, nan Sokoto, ba mu da tsarin kowa ya zo ya yi hawan sallah.”
“Da za mu yi za su iya fin doki misali 10,000 amma yanzu ba za su fi ɗaruruwa ba ake hawa da su.” In ji shi.
Ya kuma ce Mai Alfarma Sarkin Musulmi shi kansa ba hawa yake ba a don haka zai yi wuya ya ce ga tawagar da ke marawa Sarki baya a lokacin hawa. Sai dai har zuwa zamanin Sarkin Musulmi Abubakar yana hawa, a cewar masanin.
“Ana dai jawo dokinsa a aza masa lema, wannan dokin shi ake kira amarya, Sarkin Dawakin Sarkin Musulmi wanda yake bawan Sarki ne, shi ne yake riƙo dokin Sarkin, ya zo yana tafiya da shi kamar Sarki ne a kai.” Kamar yadda Haruna Wali ya bayyana.
Ya kuma ce akwai ɗan Sarkin Musulmi Usman da ake kira Amir Sa’ad Abubakar III kuma ba shi da sarauta amma yana hawan sallah, ya kan yi hawa ya zo a gaban Sarki, ya yi gaisuwa da shi da sauran ƴan Galadimomi ƴaƴan Sarki waɗanda suka gaji sarautar Sarkin Musulmi – duk da yake suma wasun su ba su da sarauta, sukan zo tare da shi cikin tawagarsa, su yi gaisuwa a gaban Mai Alfarma Sarkin Musulmi da kuma Gwamna.
A cewarsa, Sarakin Tambura yana hawa a kan raƙumi ana dukan tambari sannan masarta sukan fito a ƙasa suna tafiya suna busa – za su zo har gaban Mai Alfarma sannan su nemi wajen da za su tsaya su ci gaba da busa.
Masarautar Bauchi
Alhaji Ado Ɗanrimi Garba, wakilin Tarihin Masarautar Bauchi kuma sakataren kwamitin shiryawa da tsara hawan sallah na Masarautar Bauchi ya ce hakimai 43 ne za su yi hawa a bana kuma kowanne zai bi bayan ɗan uwansa.
“Idan muka zuba 20 a gaba, mai martaba yana tsakiyarsu, sauran 23 ɗin kuma suna bayan Mai Martaba saboda bisa al’ada, tawagar da ke baya ya fi ɗaukar mutane masu yawa.” In ji Sakataren kwamitin tsara hawan sallah a Bauchi.
Ya ce yawan dawakan da hakimai za su yi hawa da su za su kai misali dubu ɗaya da ɗari bakwai da wani abu, “tawagar sarki kuma kamar ɗari uku zuwa ɗari biyu da wani abu, aƙalla dai dawaki sama da dubu biyu da raƙuma shida ne za su yi hawa a sallar bana.
Rundunar Sarki da ke hawa a Bauchi da ake kira Giwar Sarki ta haɗa da ƴan bindiga sama da ɗari uku da ƴan baka sama da ɗari uku da ƴan sulke kamar mutum hamsin da ƴan ɗamara kamar mutum ɗari da ƴan lifida kamar mutum ɗari zuwa sama – ba su da iyaka.
“Akwai dawakin zage guda 12 sannan akwai rundunar ƴaƴan sarki da suke hawa a gaban Sarki da suma sun kai 20 akwai kuma zagage 12, akwai makaɗa – tambari, sarkin busa, ja busa, kwando, zabiya, sarkin kiɗan ganga da sarkin kiɗan kotso duk suna cikin giwar sarki.” Kamar yadda ya ce.
Hakimin da yake gaba a lokacin hawa, bisa al’ada shi ne Madakin Bauchi kuma hakan ya samo asali ne tun zamanin yaƙi sai mai biye masa shi ne Sarkin yaƙin Bauchi.
Daga cikin tawagar Sarki kuwa akwai Barwan Bauchi da hakimi a bayan Sarki kuma akwai Ajiyar Bauchi wanda ɗan majalisar Sarki ne kuma babban kansila.
“Idan aka koma ƙasa kuma, akwai Wamban Bauchi da Galadiman Bauchi wanda shi ne a ƙarshe.” in ji Alhaji Ado Ɗanrimi Garba.
Ya kuma ce akwai hawa kashi uku zuwa huɗu da ake yi - Hawan Sallah da Hawan Washe garin Sallah/Hawan Bariki. A baya kuma, lokacin babbar Sallah, Sarki ya kan fita ya zaga ta wuraren da ba ya bi. Akwai kuma hawa da ake yi lokacin girbi.
“A yanzu duka an bar yin su, hawa biyu kawai aka riƙe – Hawan Sallah da Sarki yake fita ta Ƙofar Bai ya je masallacin Idi ya yi sallah ya shigo ta Ƙofar Wambai sannan kuma ya ƙaraso ta Unguwar Jaki, ya biyo ta Kobi ya zo fada.”
An fara yin wannan hawa na sallah tun shekarar 1812. Sai kuma Hawan Bariki da aka fara a shekarar 1914 bayan haɗewar Najeriya a matsayin dunƙulalliyar ƙasa kuma har yanzu ana yinsa.
Yayin wannan hawa na bariki, ana fita ta Ƙofar Fada a bi ta Ƙofar Nassarawa, a je gidan Gwamna, a yi masa daba a can, Sarki kuma ya faɗi damuwar jama’arsa, idan aka gama ya dawo ta Ƙofar Wunti, ya bi ta Illela sannan ya dawo fada a yi masa Jahi.