Yadda cutar Lassa ke kisa da kuma barazana a yammacin Afirka

Cutar Lassa na kisa fiye da Ebola a kowace shekara, sai dai ana yin sakashi da ita - babu riga-kafi.
Bayanan hoto, Cutar Lassa na kisa fiye da Ebola a kowace shekara, sai dai ana yin sakashi da ita - babu riga-kafi, ba a mayar da hankali a kanta sannan a yanzu masu bincike na ta ƙoƙarin daƙile yaɗuwarta
    • Marubuci, Makuochi Okafor
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa health correspondent
    • Aiko rahoto daga, Ondo
  • Lokacin karatu: Minti 5

Cutar Lassa, wadda ta samo asali daga jikin ɓeraye da kuma ke janyo tsananin zazzaɓi, na ci gaba da yaɗuwa a yammacin Afrika, inda Najeriya ta kasance cikin jerin ƙasashe da ake samun ƙaruwar masu cutar.

Cutar, mai haddasa tsananin zazzaɓi mai ɓullar jini a jiki, ba ta da riga-kafi da aka amince da shi da kuma cibiyoyin yin gwaji, abin da ke janyo tarnaki wajen magance ta.

Waɗanda suka warke daga cutar na fuskantar ciwuka na tsawon lokaci da kuma tsangwama.

Kwararru sun ce sauyin yanayi da kuma cunkoson al'umma a wuri guda, na cikin abubuwan da ke ta'azzara cutar - yayin da ake ci gaba da koƙarin ganin an samar da riga-kafinta.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce cutar Lassa na iya zama annoba a duniya a yanzu, inda ƙasashe kamar Birtaniya da Amurka suka ayyana ta a matsayin cuta mai haɗari.

Wani malami Michael Olonite.
Bayanan hoto, Wani malami Michael Olonite, na amfani da yaren Yarbawa da kuma Ingilishi wajen koyarwa a al'ummarsa kan yadda za a kauce wa kamuwa da Lassa da kuma kasancewa cikin tsafta.

Cuta mai kisa da ke yaɗuwa

"Na tsuma. Ba na iya cin abinci, ba na barci. Za a iya bayyana zazzaɓin Lassa a matsayin mai haɗari a duniya saboda irin yanayin da take zuwa da shi," a cewar wani da ya warke daga cutar Michael Olonite daga garin Ayede-Ogbese a jihar Ondo.

Michael wanda ya kasance jagoran al'umma, ya kamu da cutar a 2019 bayan ziyara da ya kai wa wani mara lafiya da suke zuwa majami'a ɗaya.

Cutar, da ke kama sassan jiki da kuma lalata jijiyoyin jini, ta janyo masa nakasu a jiki.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Ba na jin kuzari kamar a baya. Ba na iya zuwa gona. Ba na tafiya mai kyau. Ta lalata min wasu sassa a jiki," in ji shi.

Yayin da yawancin mutane da suka kamu da cutarke ganin ƙananan alamomi a yawan lokuta, tana kasancewa kamar Ebola idan ta yi tsanani, abin da ke janyo barazana ga rayuwar mutum. Mata masu juna biyu da kuma jami'an lafiya ne suka fi shiga haɗari.

Cutar wadda aka fara gano ta a Najeriya a 1960, ta fi shafar ƙasashen Najeriya da Guinea da Laberiya da kuma Saliyo. Sai dai, ana ci gaba da samun masu kamuwa da cutar a sauran ƙasashen yammacin Afrika.

"Zazzaɓin Lassa ta daɗe, an yi watsi da ita. Ta kasance na tsawon lokaci. Kuma ta shafi mutum kusan 100,000 zuwa 300,000 a kowace shekara waɗanda ke kamuwa da ita, inda ake samun mutuwar mutane 5,000," a cewar Dr Henshaw Mandi, wani kwararre kan musabbabin cutuka kuma mai bincike.

Tun watan Janairun wannan shekara, Najeriya ta kasance tana fama da ɓarkewar cutar Lassa. Jihar Ondo kaɗai ta ruwaito samun mutum 100 da suka kamu da ita. Yayin da sama da mutum 500 suka kamu da cutar a ƙasar baki-ɗaya - inda aka ruwaito mutuwar mutum 90.

Ana samun cutar ne daga nau'in wasu ɓeraye da ake kira 'multimammet rats' a Turance. Sun kasance suna shiga cikin gidaje da kuma lalata abinci da aka dafa. a ƙauyuka kuma, ɓerayen na amfani da barin ɗakuna a buɗe wajen afkawa cikin abinci.

"Har a cikin ɗakin kwana, idan suka samu wuri za su shiga. A can ɗakunan girki ma suna can. Har ma da cikin dazuka," in ji Michael.

Yaɗa labaran karya da tsangwama

Michael, wanda ake kira "Baba Lassa", yana wayar da kan al'ummar da yake zaune kan hanyoyin kauce wa kamuwa da cutar, inda yake ziyartar majami'u da kuma kasuwanni.

Ƙauyawa da dama na ɗaukar Lassa a matsayin camfi kuma suna guje wa asibitoci.

"Mutanen da suka mutu sakamakon Lassa a nan za su kai sama da 50," in ji shi.

"Wata matsala ita ce wani lokaci idan mutum ba shi da lafiya, ba su zuwa gwaji. Suna cewa watakila aikin sheɗanu ne," in ji shi.

Waɗanda suka warke na fama da wasu abubuwa na tsawon lokaci, ciki har da rashin ji da kuma tsangwamar mutane.

Duk da fama da matsalar rashin ji, Michael ya ce ya jajirce wajen wayar da kan mutane.

"Akwai wani lokaci da mutane a cikin majami'ar mu suka ce, 'Ka da wani ya je gidana.' Sai dai mun gode Allah cewa wannan tsangwamar, saboda ilimin da na samu, ba ta damuna," in ji shi.

"Zan ci gaba da fita da kuma amfani da kaina don wasu su gane cewa idan kana da Lassa, za ka iya warkewa daga ita."

Farfesa Sylvanus Okogbenin, wani kwararre kan cutar Lassa a cibiyar kula da cutar a Najeriya, ya kware wajen kula da mata masu juna biyu, waɗanda suka fi haɗarin kamuwa da cutar.

Farfesa Sylvanus Okogbenin, wani kwararre kan cutar Lassa a cibiyar kula da cutar a Najeriya.
Bayanan hoto, Farfesa Sylvanus Okogbenin, wani kwararre kan cutar Lassa a cibiyar kula da cutar a Najeriya, ya kware wajen kula da mata masu juna biyu, waɗanda suka fi haɗarin kamuwa da ita

Cutar ta ƙi ci ta ƙi cinyewa

Mutanen da suka mutu sakamakon cutar Lassa sun kai kashi ɗaya, a cewar WHO, sai dai alkaluman za su iya fin haka lokacin ɓarkewarta zuwa kashi 20.

Ana wahala wajen gano cutar idan ta kama mutum da farko, inda take kama da maleriya da kuma cutar dengue.

Rashin yin gwaji a-kai a-kai na nufin ana dogaro da cibiyoyin yin gwaji, waɗanda ake fama da ƙarancinsu a yankunan da ake fama da cutar.

A yanzu, ana samun ɓarkewar cutar a kowace shekara, abin da ke janyo damuwa kan sauyin yanayi.

"Baya ga ƙasashe da kuma al'ummomin da muke tunanin suna ɗauke da Lassa, muna tunanin abin da ke janyo ta na da girman gaske, don haka babu wani ɓangare na yammacin Afrika da ba ya cikin barazana," a cewar Farfesa Sylvanus Okogbenin, wani da ke kan gaba wajen bincike kan cutar Lassa a asibitin koyarwa na Irrua da ke jihar Edo.

Damuwa a duniya

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO - ta ayyana cutar Lassa a matsayin mai barazana ga duniya. Birtaniya da Amurka kuma sun ayyana ta a matsayin mai haɗarin gaske.

A Najeriya, ƙara ƙaimi wajen saka ido ya janyo samun karuwar masu kamuwa da cutar. Ƙasar na kuma karfafa cibiyoyin kula da masu cutar.

Ministan lafiyar ƙasar, Farfesa Muhammed Ali Pate ya ce Najeriya na haɗin gwiwa wajen samar da riga-kafin cutar da kuma inganta kariyar jami'an lafiya da ke bakin aiki.

"A ɓangaren kiwon lafiya, ana ƙara ƙaimi wajen sama da magunguna da ganin an kirkiro da riga-kafi da kuma ba da taimakon da ya kamata don ceto rayukan mutane," in ji shi.

Dakta Henshaw Mandi ya ce ƙungiyarsu ta ware sama da dala miliyan 150 domin taimakawa wajen yin gwaje-gwaje kan ƙoƙarin samar da alluran riga-kafi har aƙalla guda shida.

Ana aikin gwada ɗaya daga cikin alluran a Najeriya da Ghana da kuma Laberiya.

Masu fafutuka a tsakanin al'ummomi irinsu Michael sun ce za su ci gaba da wayar da kan al'umma.

"Ba zan dakata ba," in ji shi. "Wannan wayar wa za ta ceci rayuka."

Kwararru sun ce ana samun yaɗuwar cutar ce a baya-bayan nan sakamakon sauyin yanayi da cunkoson al'umma wuri guda da kuma mu'amalar ɗan'adam da ɓerayen da ke ɗauke da nau'in cutar.
Bayanan hoto, Kwararru sun ce ana samun yaɗuwar cutar ce a baya-bayan nan sakamakon sauyin yanayi da cunkoson al'umma wuri guda da kuma mu'amalar ɗan'adam da ɓerayen da ke ɗauke da nau'in cutar.