Yara a wajen sallar Idi da masu hawan doki na cikin hotunan Afrika na mako

Sallah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu 'yan yankin Baye Fall su biyu suna gaida juna sanye da kaya masu kyawun launi a ranar Juma'a, a wani ɓangare na murnan bikin ƙaramar sallah, bayan kammala azumin wata Ramadana.
Sallah

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mai goyon bayan tsohon shugaban ƙasar Ivory Coast Laurent Gbagbo kenan a yayin wani biki da kwararren ɗan siyasar ya sake bayyana burinsa na sake zama shugaban ƙasar, duk da cewa a bayan nan an haramta masa takara.
Sallah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A washe gari wata yarinya kenan a alƙahira babban birnin Masar tana koyon yadda za ta sarrafa filawa, yayin da Musulmai ke shirin bukukuwan sallah Idi.
Sallah

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Daya daga cikin bukukuwan da ake yi a addinin Musulunci kenan. Yayin da rana ke shirin fitowa ta saman dalar Masar da ke Giza a ranar Laraba, mutane na jiran lokacin sallar Idi ya yi su je su yi sallah.
Sallah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda aka yi sallah a Nairobi babban birnin Kenya mutane sun taru a filin wasan kurkat da ake kira Ali Muslim Club suka yi Idi.
Sallah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A filin wasan zari ruga da ke Cape Town babban birnin Afrika ta Kudu, wasu Musulmai suna shirin dafa abinci domin ciyar da mutum 90,000 a ranar Sallah.
Sallah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana fara bikin sallah karama ne da an kammala azumi, wannan wata mata ce ta ci ado a ranar sallah da lalle a hannunta a birnin Legas da ke Najeriya.
Sallah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan hoton an ɗauke shi a Dakar babban birnin Senegal, wata mata sanye da fararen kaya tamkar sauran Musulmi domin halartar Idi a bakin teku.
Sallah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Abuja babban birnin Najeriya, mutane na zuwa gidajen wasa da sallah - nan kuma wasu yara ne a saman lilo mai hoton tsuntsaye.
Sallah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu kuma sun zaɓi su yi wasansu a ƙasa a wajen wasa na Magic Land...
Sallah

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu mahaya kan sirada a garin Masarautar Zazzau da ke Zaria a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya a ranar Sallah.
Sallah

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shagon sayar da littafai kenan a Landan a ranar Alhamis. An cika kantar da littattafai masu launuka iri-iri gwanin sha'awa.
Sallah

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani mai sayar da ganyaye kenan a Cape Town a ranar Litinin, duk da ana ruwa amma yana ci gaba da harkokinsa.
Sallah

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Bo-Kaap da ke makwabtaka da Cape Town, wuri ne da ya shahara saboda yadda ake zane-zane cikin launuka masu ƙayatarwa na al'adun Musulunci, ga wani zane da aka yi na nuna goyon bayan Falasɗinawa a ranar Juma'a
Sallah

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wata 'yar wasar Zambia tana murnan samun nasarar tikitin zuwa gasar Olympics da suka yi bayan doke Moroko a Rabat babban birnin ƙasar a ranar Talata.