Masu horar da tawagar Sifaniya ta mata sun yi murabus saboda Rubiales

Luis Rubiales

Asalin hoton, Getty Images

Gabaki dayan masu horar da tawagar kwallon kafa ta mata ta Sifaniya da suka je gasar kofin duniya sun yi murabus in ban da babban koci, Jorge Vilda.

Hakan ya biyo bayan takaddamar da ta bullo, bayan da shugaban hukumar kwallon kafar kasar, Luis Rubiales ya sunbaci 'yar wasa, Jenni Hermoso.

Sifaniya ta ci Ingila 1-0 ta lashe kofin duniya na mata ranar Lahadi a gasar da aka yi a Australia da New Zealand.

Mataimakin koci, Montse Tome da Javier Lerga da Eugenio Gonzalo Martin da mai kula da lafiyar 'yan wasa, Blanca Romero Moraleda da mai horar da masu tsaron raga, Carlos Sanchez, duk sun bar aikin.

Haka kuma wasu da suka shafi tawagar ta mata ta Sifaniya da suka shafi shekaru da ban da ban suma sun ajiye aikin.

Ranar Asabar, hukumar kwallon kafar ta duniya ta dakatar da shugaban hukumar kwallon kafar Sifaniya, Rubiale, bayan da ya sumbaci Hermoso a lefe, bayan cin kofin duniya.

A wani jawabi da kociyoyin suka fitar: ''Dukkan masu horar da tawagar Sifaniya ta mata mun yi tir da dabi'ar da shugaban hukumar kwallon kafar kasar ya nuna.''

Koci, Luis de la Fuente, wanda ya yiwa shugaban tafi, bayan da ya ce ba zai sauka daga mukaminsa ba a ranar Juma'a, ya kuma caccaki Rubiales ranar Asabar.

Shi dai Rubiales bai yadda ya yi murabus ba kan lamarin, amma hukumar kwallon kafar Sifaniya ta ce za ta dauki mataki a kansa.