Manyan batutuwa huɗu da ke cikin littafin rayuwar Janar Babangida

    • Marubuci, Mansur Abubakar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida ya fitar da sabon littafin tarihin rayuwarsa inda ya fallasa sirruka da dama game da lokuta daban-daban da aka shiga ruɗani a zamanin mulkinsa tsakanin 1985 zuwa 1993.

Littafin mai taken 'A Journey in Service' ya haifar da muhawara kan abubuwan da littafin ya ƙunsa da kuma abubuwan da za su iya faruwa in da abubuwan ba su kasance a haka ba - musamman batun soke zaɓen shugaban ƙasa na 1993 da kuma kisan abokin ƙuruciyarsa.

Yayin da wasu ke yaba masa kan irin ayyukan ci gaba da ya samar a ƙasar, wasu na cewa an tafka mummunar rashawa a lokacin mulkinsa.

Ga wasu muhimman batutuwa huɗu da littafin nasa ya ƙunsa.

Soke zaɓen 1993

Wannan ne batu mafi girma a littafin, wanda abu ne da ake ganin ya sauya tarihin Najeriya. Wasu na cewa har yanzu ƙasar ba ta farfaɗo daga illar soke zaɓen shugaban ƙasa na 1993.

A cikin littafin, Babangida, wanda yanzu yake da shekara 83 a duniya, a karon farko ya bayyana da-na-saninsa kan soke zaɓen.

An sa ran zaɓen zai kawo ƙarshen mulkin soji na shekara 10 a wancan lokacin, kuma soke zaɓen ya jefa ƙasar cikin ruɗani.

Yanzu haka an ayyana ranar da aka gudanar da zaɓen - 12 ga watan Yuni - a matsayin ranar dimokuraɗiyya ta ƙasar.

Daga baya an tursasa wa Babangida ajiye mulki.

An kama tare da ɗaure mutumin da ake tunanin cewa shi ne ya lashe zaɓen, Moshood Abiola, sannan kuma aka kashe matarsa.

Shugaban Najeriya na yanzu, Bola Tinubu ya jinjina wa Babangida tare da yaba masa bisa amsa laifin abin da ya faru.

"Abin da ya faru, abin da na sani ne. Ƙasar nan na son ganin na nuna nadamata," kamar yadda Babangida ya rubuta a cikin littafin.

Janar Babangida, wanda aka fi sani da IBB, ya amince a cikin littafin cewa Abiola, wanda ya mutu a 1998, ne ya lashe zaɓen.

Sai dai a daidai lokacin da ake tattara sakamakon zaɓen a shekarar ta 1993, gwamnatin mulkin soji ta wancan lokacin ta dakatar da tattara sakamakon - wani abu da ya janyo zanga-zanga da shiga halin rashin tabbas.

A wancan lokaci, ya kafa hujja da batun sayen ƙuri'a da kuma ƙoƙarin kare ɓangaren shari'a na ƙasar a matsayin hujjar soke zaɓen.

Jamiu, wanda ɗa ne ga Abiola ya ce nuna nadamar da Babangida ya yi da kuma amincewa Abiola ne ya lashe zaɓen abu ne da ya zo wa iyalinsu da mamaki.

"Wataƙila Janar Babangida na son zama lafiya ne," kamar yadda ya faɗa wa BBC.

Mulkin dimokuraɗiyya ya dawo a Najeriya a shekarar 1999, wata 11 bayan rasuwar wani shugaban mulkin sojan - Sani Abacha.

Kashe abokinsa na yarunta

Janar Mamman Vatsa da Babangida sun taso a tare, sun yi makaranta ɗaya, aji ɗaya kuma sun yi rayuwar soja tare. Kisan da aka yi wa Vatsa a shekarar 1986 bayan kama shi da laifin kitsa juyin mulki na ɗaya daga cikin abubuwan da suka janyo cece-kuce a lokacin mulkin Babangida.

"Mun kasance abokai na ƙut da ƙut," kamar yadda Babangida ya bayyana.

"Mun taso tare a Minna kuma mun yi aji ɗaya a Bida. Mun yi abubuwa da dama tare. Matata za ta iya tuna lokacin da ni da shi muke kwana a ɗaki ɗaya kafin mu yi aure. Mukan sa kaya ɗaya! Mu makusantan juna ne sosai."

Sai dai, Babangida ya ce ya gano cewa ashe Vatsa na kishi da shi tun suna yara.

"Zan iya tunawa a lokacin rayuwarmu tun daga yara zuwa matasa abu ne mai cike da kishin da yake yi da ni. Ya riƙa jin zafin cigaban da nake samu, musamman lokacin da ya yi tunanin cewa ina samun cigaba fiye da shi, ko da a makaranta ko lokacin da muke aikin soja."

An kashe Vatsa da wasu mutane tara a watan Maris na 1986. An ce sun kitsa juyin mulki, wanda in da ya yi nasara, da ya jefa ƙasar cikin garari.

"Dole ce ta sanya na zaɓi ɗaya, ko na zaɓi ceto rayuwar abokina ko kuma makomar ƙasar," kamar yadda ya rubuta a cikin littafin.

Juyin mulkin Najeriya na farko

Wani abin muhawara shi ne juyin mulkin 1966 wanda ya tuntsurar da gwamnatin Najeriya ta farko bayan samun ƴancin kai daga Birtaniya. An kashe firaiministan Najeriya Tafawa Balewa, tare da wasu manyan jami'an gwamnatin tarayya da ta yanki.

Kasancewar akasarin waɗanda suka kitsa juyin mulkin sun fito ne daga kudu maso gabashin ƙasar, an riƙa bayyana juyin mulkin a matsayin na ƴan ƙabilar "Ibo" - wani abu da Babangida ya ce ba haka ba ne.

Ya bayyana rawar da Manjo John Obienu, jami'in soja ɗan ƙabilar Ibo - ya taka wajen tarwatsa juyin mulkin, inda ya ce an kuma kashe jami'an sojoji da dama ƴan ƙabilar Ibo a lokacin juyin mulkin.

Littafin ya kuma bayyana gudumawar wasu jami'an sojin daga wasu ƙabilun - kamar Yarbawa - a wajen kitsa juyin mulkin.

Tsohon shugaban na Najeriya ya ce asalin manufar juyin mulkin ita ce kuɓutar da Obafemi Awolowo daga ɗaurin da ake yi masa, da kuma naɗa shi a matsayin shugaban ƙasa.

Babangida ya ce: "Lokaci ne mai tsanani ga rundunar sojin Najeriya. Kmar yadda na bayyana a baya, a matsayin matashin jami'in soja wanda ya ga yadda abubuwa suka wakana daga gefe, da alama ba ƙabilanci ne ya tunzura yin juyin mulkin ba.

"Misali, jagoran juyin mulkin, Manjo Kaduna Nzeogwu a suna ne kawai za a ce ɗan ƙabilar Ibo ne. An haife shi kuma ya girma na a Kaduna, iyayensa sun fito ne daga Okpanam a jihar Delta ta yanzu. Nzeogwu na magana da Hausa raɗau! Wataƙila shi da ƴan tawagarsa sun yi tunanin cewa za su iya sauya akalar ƙasar nan domin samun ci gaba.

Danganta ƴan ƙabilar Ibo da juyin mulkin ya haifar da far wa ƴan ƙabilar a faɗin ƙasar, wani abu da ya haifar da yaƙin basasa a lokacin da wasu ƴan ƙabilar Ibo suka yi yunƙurin ɓallewa daga Najeriya a 1967. An kashe aƙalla mutum miliyan daya a wayƙin wanda ake kira yaƙin Biyafara.

Soyayyarsa da Maryam Babangida

Mutane da dama na kallon mai ɗakin Janar Babangida a matsayin uwargidar shugaban ƙasa mafi tasiri a tarihin ƙasar. Daga 1985 zuwa lokacin da suka bar mulki 1993, mutane sun riƙa nuna sha'awa kan soyayyar da ke tsakanin Babangida da Maryam. Ta rasu ne a shekarar 2009, kuma tun daga lokacin har yanzu tsohon shugaban ƙasar bai sake yin aure ba.

"Kyakkyawa ce, launin fatarta da idanunta masu ɗaukar hankali da murmushintada ke bayyana haƙoranta, fuskarta na ƙyalli kuma idanunta na kaɗawa," kamar yadda ya rubuta a littafinsa.

Ya bayyana Maryam a matsayin mace mai biyayya, uwa ta gari, mai kula da gida kuma mai rajin inganta rayuwar matan karkara. Sannan kuma nagartacciyar ƙawa.