Yaya shirin Trump na garkuwa ga sararin samaniyar Amurka zai yi aiki?

Shugaban Amurka Donald Trump zaune kan kujera a ofishinsa da ke fadar White House. Kusa da shi akwai hoton garkuwar kare sararin samaniya na Golden Dome da kuma sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth.

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 5

Donald Trump ya yi alƙawarin samar da garkuwa domin tsare sararin samaniyar Amurka da ake kira da Golden Dome wanda ya ce zai fara aiki kafin ƙarshen wa'adin mulkinsa.

Tun da farko ya yi alƙawarin saka kuɗi dala biliyan 25, amma ya yi hasashen a ƙarshe kuɗin zai kai dala biliyan 175, sai dai hukumomi sun yi gargaɗin cewa a ƙarshe kuɗin zai iya ninka adadin da aka yi hasashe sau uku.

Shirin ya ƙunshi fasahohin zamani na doron ƙasa, da cikin ruwa da kuma sararin samaniya - ciki har da na'urorin da ke sararin samaniya da za su iya gano makamai da ke kusantowa da kuma waɗanda za su tare su.

Za a gina shingen ne ta hanyar faɗaɗawa da kuma gina sabo kan wanda ake da shi a yanzu domin kariya daga ƙaruwar barazanar hare-hare daga ƙasashe kamar Rasha da China.

Ta yaya garkuwar za ta yi aiki?

Ɗaya daga cikin abin da ya ja hankalin Trump a shirin samar da garkuwar shi ne shingen Isra'ila, wanda ke amfani da na'urori domin kakkaɓo makamai masu linzami masu cin gajeren zango wanda take amfani da shi tun 2011.

Sai dai girman shingen Amurka zai ninka na Isra'ila, kuma za a tsara shi ta yadda zai kare sararin samaniya daga hare-hare masu girma.

Zai yi amfani da ɗaruruwan tauraron ɗan'adam, wani abu da a shekarun baya zai yi tsadar da ba za a amince a yi ba, amma wanda a yanzu za a iya yi.

''Ronald Reagan ya so ya gina shi shekaru da dama da suka wuce, amma ba su da fasahar,'' in ji Trump, yana magana kan shingen kare sararin samaniya daga makamai masu linzami wanda aka fi sani da ''Star Wars'' wanda tsohon shugaban ƙasar ya so yi a shekarun 1980.

Shingen na Golden Dome na da ƙarfin tare makamai masu linzami da aka harbo daga sauran ƙasashen duniya, ko kuma wanda aka harbo daga sama,'' a cewar Trump.

Babban daraktan cibiyar kula da ƙirƙire -ƙirƙiren fasaha da kwamfuta na Amurka, Rear Admiral Mark Montgomery mai ritaya, ya shaida wa BBC cewa shingen zai dogara ne ga rukuni uku ko huɗu na taurarin ɗan'adam da za a ƙara a cikin ɗaruruwan tarurarin ɗan'adam da ake da su.''

''Akwai taurarin ɗan adam, ɗaruruwansu, da za su gano idan an harbo makamai.

Sannan akwai wasu da za su riƙa bibiya.

Sannan kuma akwai waɗanda ke kakkaɓo ko lalata makamai masu linzami da abokan hamayya suka harbo,'' in ji shi.

Za a iya gina garkuwar cikin shekara uku?

Shugaba Trump a gaban wata taswira da ke nuna yadda garkuwar take

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Garkuwar na da ƙarfin kare sararin samaniya daga makamai masu linzami da wasu ƙasashen duniya suka harbo, ko kuma wanda aka harbo daga sararin samaniya.'' in ji Trump.

Shashank Joshi, editan fannin labarai kan tsaro a jaridarThe Economist, ya shaida wa BBC cewa sojojin Amurka za su ɗauki shirin da muhimmanci, amma ba zai yiwu a kamalla shi a cikin shekarun wa'adin Trump ba, kuma kuɗin da za a kashe zai laƙume adadi mai yawa na kasafin kuɗin fannin tsaron Amurka.

Tsohon Admiral Montgomery ma ya yarda da hakan.

" Wannan shiri ne da za a shafe shekara 5 zuwa 7 zuwa 10 domin a yi shi yadda ya kamata.''

'' Shin za a sami wasu abubuwa nan da shekara uku da za su inganta tsaron mu? tabbas, in ji shi, amma ya ƙara da cewa samun kashi 100 na tsaro ba zai yiwu ba kafin ƙarshen wa'adin shugaba Trump.

Ofishin kasafin kuɗi na gwamnatin Amurka, wanda ke hasashen tattalin arziki, ya ce kuɗin zai iya kai wa dala biliyan 542 cikin shekara 20 wajen siyan kayyaykin da za a sa a sararin samaniya kawai.

Wane ne zai gina shingen?

Janar Michael Guetlein shi ne mutumin da zai jagoranci gina shingen da zai laƙume biliyoyin daloli.

Tun watan Disamban 2023, ya kasance mataimakin shugaban gudanar da ayyukan sararin samaniya reshen sojojin Amurka wanda ke bayar da gargaɗin makami mai linzami da wasu ayyukan da suka jiɓanci hakan.

Guetlein, babban Janar wanda Shugaba Trump ya bayyana a matsayin ''mutum mai basira sosai'', zai kawo ƙwarewar aiki sosai zuwa wannan shirin a fannin gano makamai masu linzami da aka harbo da kuma ilimin sararin samaniya.

An haife shi kuma ya girma a jihar Oklahoma da ke Amurka, kuma Guetlein ya shiga rundunar sojin saman Amurka a 1991 bayan ya kammala jam'iar jihar Oklahoma.

Me Rasha da China ke cewa game da shingen?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Musabbabin gina shingen shi ne kare Amurka daga harin makamai masu linzami daga Rasha da China.

Bayanan da suka fito a baya bayan nan daga hukumar tattara bayanan sirri na tsaro sun ce za a ƙara girma da kuma ƙara zamanantar da hare haren makami mai linzami, inda ake zargin ƙasashen suna kokarin samar da wani shiri da zai yi amfani da ɓarakar da ke akwai a tsaron Amurka.

Sabon shigen tsaron '' zai samar da wani yanayi na ƙarfafa makamai na yin yaƙi a sararin samaniya,'' a cewar wata sanarwa daga fadar Kremlin da aka wallafa bayan tattaunawa tsakanin Rasha da China a farkon wannan watan.

Sai dai kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya bayyana shirin a matsayin wani abu da ya shafi ƙasa mai cin gashin kanta, kuma yana ganin cewa akwai yiwuwar a dawo da batun tattauna makamin nukiliya.

A gefe guda kuma China ta ce shirin zai kawo cikas ga tsaron duniya ta hanyar ƙara zafafa ayyukan soji a sararin samaniya da kuma barazanar yin gasar yin amfani da makamai.

''Shingen Open Dome na bayar da damar ƙarfafa yin yaƙi a sararin samaniya, kuma yanada wasu ɓangarori da basu dace ba, waɗanda suka sha bambam da yadda za a yi amfani da sararin samaniya lafiya kamar yadda yake a yarjejeniyar amfanin da sararin samaniya'', a cewar wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje a ranar Laraba, inda yake buƙatar su da su watsar da shirin.

Shin Kanada za ta shiga tsarin garkuwar Golden Dome?

A lokacin da yake bayyana shirinsa a ofishin shugaban ƙasa, Shugaba Trump ya ce Canada ta buƙaci shiga cikin tsarin.

A cikin wata sanarwa, Ofishin firaministan Canada Mark Carney ya ce shi da ministocinsa na tattaunawa kan sabon dangantakar tsaro da kasuwanci da Amurka.

''Waɗannan tattaunawa sun haɗa da ƙarfafa NORAD ( Sashen kula da tsaron sararin samaniyar arewacin Amurka) da kuma wasu shirye shiryen kamar shingen Golden Dome.'' a cewar sanarwar.

A lokacin da ya kai ziyara Washington a farkon wannan shekara, ministan tsaron Canada a lokacin Bill Blair, ya bayyana cewa Canada na da sha'awar shiga shirin samar da shingen, a cewar sa ''shiri ne mai kyau'' kuma yanada muhimmanci ga ƙasar.