Addinina ya fi muhimmanci a kan ƙwallon ƙafa - Ouattara

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ian Williams
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
- Lokacin karatu: Minti 5
''A gare ni, addini ne farko. Addini na gaba da ƙwallo.''
A yayin da watan Ramadan ya kusa kawo ƙarshe, ɗan wasan ƙwallo na Bournemouth Dango Ouattara ya bayyana abin da ya fi mayar da hankali a kai.
Ɗan wasan gaba daga Burkina Faso mai riƙo da addini ne da ke sallah sau biyar a rana, hakazalika ya na wasu sallolin nafila gabanin ya buga ƙwallo da kuma bayan ya kammala bugawa, wanda a cewar sa na taimaka masa wurin 'ƙanƙan da kai.''
''Yana taimaka mana mayar da hankali kan mu, mu ga abin da muka yi mai kyau da kuma abin da ba mu yi da kyau ba,'' kamart yadda ɗan shekara 23 ya shaida wa sashen wasanni na Afrika na BBC a lokacin da muka haɗu da shi a masallacin unguwarsu da ke Poole.
''Ya na kuma taimaka mana gyara kura-kurenmu a cikin alumma, ya kuma taimaka mana mu tsaya kan tafarkin da ya dace.''
A lokacin da muke tattaunawa, Ouatarra na yawan amfani da kalmomi kamar su ''kwanciyar hankali'' da ''natsuwa'' wajen bayyana alfanun addinin musulunci.
Mutum ne shiru-shiru mai zurfin tunani da ke da kunya, babu wani abu mai tsada tattare da shi.
Ya iso da wuri saboda tattaunawarmu, yana sanye da kaya farare daga sama har ƙasa, ya kuma buƙaci ya fara yin sallah kafin mu zauna mu fara tattaunawar.
''Addinina na taimaka min shawo kan matsaloli da dama, in kuma mutunta mutane, sannan in mutunta zaɓinsu da addininsu,'' in ji shi.
''Ko a filin ƙwallo ne, ko a wajen fili tare da abokai, ko kuma da ƴan'uwana, yana taimaka min in samu kwanciyar hankali a rayuwata ta yau da kullum.''
''Dole sai ka yi imani kafin za ka iya yin wani abu''
'Alummar na nuna ba kai kaɗai bane'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wannan kakar, da alamu Ouattara ya yarda da iyawarsa.
Duk da cewa ba kowanne wasa ake farawa da shi ba, ya zura ƙwallaye 9 a wasanni 30 da ya buga a ƙungiyar ta the Cherries, ciki har da ƙwallaye uku rigis da ya zura a ragar Nottingham Forest a watan Janairu.
Wannan adadin cigaba ne sosai daga kakar da ta gabata inda ya zura ƙwallo ɗaya kacal.
Yanzu da ƙungiyar wadda Andoni Iraola ke horaswa ke fuskantar kalubalen samun gurbin gasannin Turai, Ouatarra ya ce tawagar na da 'daɗin' wasa ciki.
''Sirrin wannan shekarar shi ne tawagar bata sauya ba, kusan duka ƴan wasan suna nan, mai horas wa ma yana nan. Yana da muhimmanci ka samu ƙungiyar da take ci gaba da bunƙasa tare,'' in ji shi.
''Kana gani a kowanne lokaci cewa ƴan wasa na jin daɗin ƙungiyar''.
"Za mu yi duk mai yiwuwa domin mu je matakin gaba.''
Ouattara, wanda aka haifa a Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso ya je ƙungiyoyi da dama kafin ya zo ƙungiyarsa ta yanzu a Turai.
Ɗan ƙwallon wanda aka siya kan pan miliyan 20, ya kasance ɗan Burkina Faso na biyu da ya buga ƙwallo a gasar Premier lokacin da ya fara fitowa a Janairun 2023, baya ga kyaftin din tawagarsu ta ƙasa kuma tsohon ɗan wasan gaba na Aston Villa Bertrand Traore.
Duk da har yanzu ba ya sakin jiki ya yi Turanci na lokaci mai tsawo, ya tabbatar cewa harshe ne babban matsalar da ya samu bayan ya iso, sai dai ya ce addini ma ya taka rawa a nan.
''Ni da wakili na mun samu mun gano massalaci, daga nan na soma komawa zuwa yadda nake sallah kamar yadda na saba,'' in ji shi
''Bayan na dawo massalaci, sai komai ya fara tafiya min daidai a ƙwallon.''
''Yana taimakawa saboda idan ka sami kanka a wani garin, samun alumma irinka na nuna ba kai kaɗai bane. Za ka samu damar yin sallah da wasu mutanen da kuma haɗuwa da wasu.
''Yana sa mu mayar da hanakali kan addini.''
Mai dafa abinci na ƙungiyar, tashi da wuri da kuma bacci

A wannan shekarar, an soma azumin watan Ramadan ne ranar Asabar 1 ga watan Maris kuma mai yiwuwa a kammala ranar Lahadi 30 ga watan Maris.
Wannan wata ne mai falala wanda Musulmai suka yi imanin cewa a cikinsa ne aka fara saukar da Al Qurani ga Annabi Muhammad (SAW).
Ga masu imani, azumi na taka muhimmiyar rawa, barin cin abinci da abin sha tsakanin fitowar rana da faɗuwarta.
''Ba zan ce Azumi na da wahala ba, abin a ƙwaƙwalwa yake, saboda ni dai na saba yi,'' in ji Ouatarra.
''Ya fi zama dai rashin ruwa. Sai kuma kasancewar za ka tashi a wani lokaci da ba ka saba ba domin cin abinci, shi ne kawai ke gajiyarwa.''
Sai akwai dabaru wajen shawo kan gajiyarsa, wato bacci.
''Nakan tashi ƙarfe 4:30 na safiya, in yi alwala, dama ina da abinci da zan ci wanda tuni mai dafa abinci na ƙungiyar ya dafa.''
''Zan ci, kuma bayan sallah ina da lokaci da zan ɗan koma bacci na sa'a ɗaya ko fiye kafin in fita atisaye.
''Daga nan bayan atisayen, sai in yi Sallah in sake komawa bacci na sa'a 1 kuma. Don haka saboda ina samu in huta koda yaushe yana nufin ina murmurewa yadda ya kamata.''
Duk da azuminsa, da kuma lokacin da ba ya bacci, tsarin atisayen Ouatarra na nan yadda yake.
''Abin ya ma fi sauƙi idan kana da goyon bayan tawagar baki ɗaya, ko ƴan wasan ko kuma ma'aikatan,'' in ji shi.
''Kowa na tambaya 'yaya kake ji? komai na tafiya daidai? babu wahala sosai?'
''Suna fahimta ta kuma suna ƙarfafa min gwiwa.''
Duk da dai shi kaɗai ne Musulmi a tawagar Bournemouth, ba shi kaɗai ba ne ke azumi lokacin Ramadan a matsayin ɗan ƙwallo a gasar Premier ba.
Haƙiƙa watan ya kasance mai muhimmanci, inda a 2021, gasar Premier ta gabatar da sabuwar yarjejeniya da ke bai wa alƙalan wasa damar dakatar da wasan da ake kan bugawa idan rana ta faɗi domin bai wa ƴan wasa damar yin buɗe baki.
Wani abu ne Ouatarra ke nuna godiyarsa a kai.
''Wannan tsarin na gasar Premier abu ne da za a yi san barka saboda ba abu mai sauƙi ba ne buga ƙwallo idan kana azumi,'' a cewar sa.
''Muna fatan za a ci gaba a hakan.''
Dango Ouattara mutum ne da ke girmama kiran Sallan, abin da ya taimaka masa zama ɗan wasan da magoya bayan ƙungiyar Bournmouth suka yarda da shi.








