Da gaske Tinubu ba ya kare 'yan jam'iyyarsa daga binciken cin hanci?

Asalin hoton, Bola Tinubu/Facebook
Gwamnatin Tinubu ta yi iƙirarin cewa babu wani da zai zarge ta da kare 'yan siyasa ko jami'an gwamnati idan binciken cin hanci da rashawa ya biyo ta kansu, duk kusancinsu da ita.
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya ce hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta samu gagarumar nasara a aikinta na yaƙi da cin hanci cikin shekara biyu na gwamnatin Tinubu saboda ba sa yi mata katsalandan.
Da yake jaddada ƙudurin gwamnatinsu na ɗabbaƙa adalci, Kashim Shettima ya ce babu wani ɗan siyasa ko jami'in gwamnati da ya fi ƙarfin doka a ƙarƙashin gwamnatinsu.
Sai dai ƙungiyar Transparency International a Najeriya ta ce ba za a iya tabbatar da iƙirarin ba a zahiri.
"(Jami'an yaƙi da cin hanci) su da kansu sun san irin wahalar da suke sha, su sadaukar da rayukansu, su tabbatar sun kama waɗanda ake zargi da laifi, amma sai ka ga an sako su. Akwai misalai da yawa!" Cewar Auwal Musa Rafsanjani, jagoran Transparency a Najeriya.
EFCC dai ta ce a cikin shekara ta yi nasarar ƙwato dukiyar da ta zarce naira biliyan 500, sannan ƙoƙarinta ya kai ga an yanke wa mutum 7000 hukunci a gaban shari'a.
Ya bayyana haka ne yayin taron ƙara wa juna sani ga alƙalai da masu shari'a da hukumar EFCC ta shirya ranar Litinin da haɗin gwiwar cibiyar horas da alƙalai ta ƙasa a Abuja.
Kashim Shettima ya ce gwamnatinsu ta duƙufa wajen tsare gaskiya da tabbatar da yin bayani a kan harkokin tafiyar da mulki.
Me 'yan fafutuka suka ce?
Transparency International a Najeriya ta ce alal haƙiƙa ma 'yan siyasa da yawa suna sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki ta APC da zarar sun fuskanci za a bincike su a ƙasar.
Jami'in ƙungiyar, Auwal Musa Rafsanjani ya ce yawancin masu irin waɗannan sace-sace, da sun ga za a yi bincike a kan wata badaƙalarsu ta baya, sai su koma jam'iyyar shugaban ƙasa.
"Kuma da mutum ya shiga jam'iyya mai mulki, to za ka ga kamar ya samu kariya," in ji Rafsanjani.
Jami'in na Transparency International ya ce ko waɗannan kuɗaɗe da kadarori da ake cewa an ƙwato, ba a hannun 'yan siyasan da ke cikin jam'iyya mai mulki ba ne.
Ya yi iƙirarin cewa idan aka duba za a ga mutanen da aka ƙwato dukiyar a hannunsu, kusan duka ba sa alaƙa da gwamnati.
BBC ta kuma yi nazari a kan wasu jami'an da hukumar EFCC ta bincika ko ta gurfanar gaban kotu a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
Godwin Emefiele
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Cikin manyan binciken cin hanci da rashawa da hukumomi ke yi a Najeriya ƙarƙashin gwamnatin Tinubu har da na tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, wanda aka kama tun ranar Juma'a 5 ga watan Oktoban 2023.
Ya riƙe wannan muƙamin tsawon shekara goma, kafin sabon shugaban ƙasar Bola Tinubu ya dakatar da shi.
EFCC a ranar 9 ga watan Oktoban 2025 ta ce ana ci gaba da yi wa tsohon gwamnan Babban bankin Najeriya shari'a a kotun laifuka na musamman ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Rahman Oshodi a Lagos, bisa zargin tafka almundahanar dala biliyan 4.5.
Sanarwar da hukumar ta wallafa na cewa an gabatar da ƙarin shaidu a kan Godwin Emefiele wanda yake fuskantar tuhuma 19 da ke da alaƙa da karɓar tukwici da kuma neman cin hanci.
EFCC ta ce shi da abokin shari'arsa duk sun musanta tuhume-tuhume da ake musu.
An yi ta sukar Godwin Emefiele saboda wasu matakai da ya ɗauka lokacin yana riƙe da muƙamin gwamnan Babban Bankin ƙasar, ciki har da sake fasalin takardun kuɗi na naira a ƙoƙarin rage tasirin kuɗi a zaɓen 2023.
Rahotanni kuma sun ce Godwin Emefiele ya yi yunƙurin shiga zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC mai mulki don ƙalubalantar masu neman tikitin takarar shugaban ƙasa kamar Bola Tinubu.

Asalin hoton, Getty Images
Aminu Tambuwal
Aminu Waziri Tambuwal, tsohon gwamnan Sokoto ya fuskanci bincike a hannun EFCC, inda jami'an hukumar suka yi masa tambayoyi bisa zargin cire kuɗi kimanin naira biliyan 189 daga asusun gwamnati.
Sanata Aminu Tambuwal ɗan majalisar dattijai a ƙarƙashin jam'iyyar PDP kuma ya yi gwamnan jiha daga 2015 zuwa 2023.
Rahotanni sun ambato EFCC na cewa cire kuɗaɗen da aka yi zargi ya saɓa wa dokar hana halasta kuɗin haram ta 2022.
'Yan adawa ciki har da jagoran adawa na Najeriya Atiku Abubakar sun soki EFCC saboda kama Tambuwal, inda suka zargi Shugaba Tinubu da mayar da hukumomin yaƙi da cin hanci na ƙasar makamin yaƙar 'yan adawa don ya matsa musu lambar komawa jam'iyyarsa ta APC.
Hadi Sirika
Babbar Kotun Abuja ta ci gaba da shari'ar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika a farkon watan Yulin 2025.
Yana fuskantar shari;a tare da 'yarsa, Fatima Hadi Sirika da kuma surukinsa Hamma Jalal Sule da kamfanin Al Buraq Global Investment Limited.
EFCC na yi wa mutanen uku da kamfanin tuhume-tuhume guda shida da aka yi wa gyaran fuska masu alaƙa da tozarta muƙaminsa da kuma halasta kuɗin haram.
An zargi babban wanda ake ƙara da yin amfani da muƙaminsa na minista daga ranar 11 ga watan Nuwamban 2016 zuwa 29 ga watan Mayun 2023 wajen raba wa iyalinsa kwangiloli.
Kuɗin dai sun kai naira biliyan biyu da miliyan ɗari bakwai.
Yahaya Bello
Hukumar EFCC ta ce kotun ɗaukaka ƙara shiyyar Lagos ta tabbatar da wani umarnin kula da wasu kadarori guda 14 da kuma kuɗi naira miliyan 400 masu alaƙa da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a ranar 6 ga watan Agustan 2025, .
Kadarorin sun haɗar da wani sashen otel a ginin Burj Khalifa da ke Dubai a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, da kuma kuɗaɗen da ake zargin an samu daga haramtattun ayyukan.
Haka zalika, EFCC a ranar Laraba 8 ga watan Oktoban 2025, ta ce tana ci gaba da gabatar da shaidu a shari'ar da take yi da Yahaya Bello gaban Mai shari'a Maryanne Anineh ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin karkatar da naira biliyan 110.4 daga asusun gwamnatin jihar Kogi.
Ta ce ana yi wa tsohon gwamnan kuma ɗan jam'iyyar APC tuhuma 16 masu alaƙa da babban laifin cin amana da halasta kuɗin haram.
Olu Ogunloye
Shari'ar tsohon ministan lantarki da ƙarafa, Olu Agunloye na ci gaba da gudana a babbar Kotun Tarayya da ke Apo a Abuja.
EFCC a ranar 9 ga watan Oktoba ta ce wani shaida ya sanar da kotu cewa tsohon ministan ya yi biris da umarni da ƙudurin taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya na ranar 21 ga watan Mayun 2003, inda ya ba da kwangilar aikin lantarki na Mambilla ga wani kamfani Sunrise Power da Transmission Company Limited a kan dala biliyan shida.
EFCC ta gurfanar da Olu Ogunloye ne da tuhuma bakwai da aka yi garambawul da ke da alaƙa da tafka rashawa da kuma almundahanar ba da kwangilar aikin lantarki ta Mambilla.
Sambo Dasuki

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon mashawarcin shugaban ƙasa kan sha'anin tsaro, Kanal Sambo Dasuki mai ritaya na ci gaba da gurfana a gaban Babbar Kotun Tarayya ta Mai shari'a Charles Agbaza a Abuja.
Wata sanarwar hukumar a ranar 8 ga watan Oktoban 2025, EFCC ta ce an sake ɗaga shari'ar zuwa ƙarshen wannan wata na Oktoba don bai wa hukumar damar sabunta jerin shaidun da ta gabatar da kuma ci gaba da zaman sauraro.
Sambo Dasuki yana fuskantar ƙarar da EFCC ta shigar ne a kan tuhuma 32 da aka yi wa gyaran fuska masu alaƙa da babban laifin cin amana da halasta kuɗin haram kimanin naira biliyan 33.2.
Wata tuhuma ta ce: "kai, Kanal Sambo Dasuki mai ritaya lokacin kana mashawarcin shugaban ƙasa kan sha'anin tsaro ranar 27 ga watan Nuwamban 2014 a Abuja cikin hurumin wannan kotu mai alfarma, an damƙa maka amanar dukiya, ciki har da: kuɗi naira biliyan goma, da nufin aiki da su kan al'amura tsaro na musamman, amma ka aikata babban laifin cin amana, lokacin da cikin rashin gaskiya ka fitar da kuɗin don zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP, hakan kuma laifi ne da za a iya hukunta ka a ƙarƙashin sashe na 315 na kundin penal.
Sanarwar ta ce waɗanda ake ƙara sun musanta aikata laifi da aka karanta musu tuhume-tuhumen.
Darius Ishaku, Gabriel Suswam, Abdulfatah Ahmed
Ƙarin wasu mutane da EFCC ta bincika kuma ta gurfanar da su gaban kotu, har da tsohon gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku bisa zargin babban laifin cin amana da karkatar da dukiyar al'umma naira biliyan 27.
Akwai kuma tsohon gwamnan jihar Binuwai Gabriel Suswam da ke fuskantar tuhuma 11 kan zargin karkatar da kuɗi naira biliyan 3.1.
Wata shari'ar ita ce wadda ta danganci Manjo Janar UM Mohammed, tsohon manajan daraktan kamfanin kula da kadarorin rundunar sojojin ƙasa ta Nijeriya.
Kotu dai a cewar EFCC ranar 26 ga watan Agustan 2025 ta yanke hukuncin a ƙwace hannun jarin da ya kai darajar sama da naira miliyan 245 da ke da alaƙa da tsohon hafsan sojan.
Haka zalika, EFCC ta ce ta gabatar da ƙarin shaidu kan ƙarar da ta shigar kan tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed ranar Talata 22 ga watan Yulin 2025, kan zargin almundahana da naira biliyan 5.78, tare da tsohon kwamishinansa na kuɗi.
Willie Obiano
Tsohon gwamnan jihar Anambra Willie Obiano zai gurfana gaban kotun Mai shari'a Mohammed Umar ranar 25 ga watan Nuwamban 2025.
EFCC ta ce ta gurfanar da shi ne a kan tuhuma 9 da ke da alaƙa da halasta kuɗin haram da karkatar da dukiyar al'umma da ɗibga sata da cin hancin da ya kai naira biliyan huɗu.
Umar Ganduje
Auwal Musa Rafsanjani ya ce shi ma tsohon gwamnan Kano, Umar Abdullahi Ganduje, shi ma wanda ake bincikensa saboda ya riƙe muƙamin shugaban jam'iyya mai mulki a baya, ka ga ba a ma iya yin wani abu a kai ba.
Da dai sauran misalai da yawa.
Ya kuma ce mafi yawan mutanen da EFCC ta gurfanar a kotu kuma har aka yanke musu hukunci, 'yan damfara ne da ake kira 'yan yahoo.
Gaskiyar magana in ji shi waɗanda aka yanke wa hukuncin ƙananan ɓarayi ne, amma gagga-gaggan ɓarayi ba sa ɗauruwa, saboda alaƙarsu da gwamnati mai ci da kuma suna da kuɗin da ake zargin suna ba da cin hanci ga su da kansu alƙalan.
Ya yi zargin cewa ba ƙananan kuɗi Najeriya take rasawa ba a kullum sanadin cin hanci da rashawa, amma hukumomin yaƙi da cin hanci ba yadda za su yi saboda ba sa samun cikakken goyon bayan da suke buƙata.
'Kariyar da wasu ke samu na janyo ƙarin sace-sace'

Asalin hoton, Rafsanjani/Facebook
Transparency International a Najeriya ta ce bai kamata ba a ce da zarar ɗan siyasa ya shiga jam'iyya mai mulki, shi kenan ya kuɓuta daga binciken cin hanci da ake zargin ya aikata.
Jagoran na Transparency ya ce al'ummar ƙasar na sane da duk wani abu da ake ciki kuma su ne za su yi wa gwamnati alƙalanci.
Ya ce a cikin misalan da suka bayyana ƙarara na 'yan siyasan da ake zargi da cin hanci amma aka yi biris da bincikensu har da tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa.
Jaridun Najeriya sun ce EFCC ta ƙwace fasfon tsohon gwamnan na Delta, bayan ta kama shi ranar 4 ga watan Nuwamban 2025 bisa zargin karkatar da kuɗi kimanin naira tirliyan ɗaya da biliyan 300.
Haka kuma an zarge shi kan wasu kuɗi naira biliyan 40, waɗanda aka ce ya yi iƙirarin amfani da su wajen sayen hannun jari a wani kamfanin sarrafa iskar gas.
Sai dai a watan Afrilun wannan shekara, Ifeanyi Okowa ya sanar da sauya sheƙa zuwa APC daga PDP bayan ya tsaya matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar mai adawa a zaɓen 2023.
Rafsanjani ya ce ana maganar shigar Okowa APC, sai batun binciken da ake yi masa ya tsaya.
Ya kuma ce shi ma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya shiga irin wannan rigar kariyar, bayan alƙalai sun yi watsi da duk tuhume-tuhumen da aka yi masa tare da shi daga aikata wani laifi.
EFCC dai ta gurfanar da shi a gaban kotu ne kan tuhuma 11 da ta danganci halasta kuɗin haram da tafkar satar da ta kai naira biliyan shida da miliyan 900.
Sai dai a watan Yulin bana, EFCC ta sake nanata ƙudurinta na ɗaukaka ƙara a kan hukuncin.











