Dalilin da ya sa kotu ta dakatar da asusun banki huɗu na Mele Kyari

Asalin hoton, Getty Images/EFCC/X
Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja babban birnin Najeriya ta bayar da umarnin dakatar da wasu asusan da ke da alaƙa da tsohon shugaban kamfanin mai na NNPCL Mele Kyari.
Kotun ta bayar da umarnin dakatar da asusan na bankin Jaiz saboda zargin zamba da kuma halasta kuɗin haram.
Mai Shari'a Emeka Nwite ne ya bayar da umarni bayan wani lauyan hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci, Ogechi Ujam, ya nemi kotun ta dakatar da amfani da asusan har zuwa lokacin da hukumar za ta kammala bincike a kansu.
"Na saurari mai ƙorafi kuma na duba takardun ƙorafin da suka shigar masu ɗauke da hujjoji da bayanai. Na lura cewa buƙatarsu ta cancanci a amince da ita," kamar yadda alƙalin ya bayyana.
Mai Shari'a Nwite ya ɗage sauraron batun har zuwa ranar 23 ga watan Satumba domin ganin rahoton binicken.
Abin da muka sani game da lamarin
A ranar 11 ga watan Agsuta ne EFCC ta shigar da buƙatar mai lamba FHC/ABJ/CS/1641/2025, inda ta zargi Mele da yin amfani da asusan waɗanda aka alaƙanta da aikata haɗa-baki, da karya ƙa'idar aiki, da kuma halasta kuɗin haram.
Asusan da umarnin ya shafa na bankin Jaiz ne da suka ƙunshi: 0017922724 – Mele Kyari; Jaiz Bank account number 0018575055 – Guwori Community Development Foundation and Jaiz Bank account number 0018575141 – Guwori Community Development Foundation (Flood Relief).
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar EFCC, binciken farko-farko sun nuna cewa akwai kusan naira miliyan 600 da ke cikin asusun da take zargi na ayyukan haramun ne.
A cikin ɗaya daga takardun ƙorafin na EFCC, Amin Abdullahi ya ce hukumar ta yi aiki ne da wani ƙorafi da cibiyar ''Guardians of Democracy and Rule of Law'' ta aike mata ranar 24 ga watan Afrilu.
"Bayan samun rahoton ne da ke ƙunshe sakin layi na 4, tawagata ta ƙaddamar da bincike daban-daban da suka ƙunshi tattara bayanan asusan banki daga bankunan kasuwanci," a cewarsa.
Ya faɗa wa kotun cewa binciken farko ya gano biyu daga cikin asusun na ɗauke da sunan Mele Kyari, yayin da sauran biyun ke ɗauke da sunan wata ƙungiya mai zaman kanta.
EFCC ta kuma ce bincike ya nuna Mele Kyari na da alaƙa da asusun kuma an samu shigar kuɗaɗen da ake zargi na haram ne a cikinsu daga NNPC da sauran kamfanonin man fetur da ke hulɗa da NNPC ɗin.
"Bayanan wannan bankin sun nuna dangin Kyari da ke yi masa aiki ne ke kula da waɗannan asusun," a cewarsa.
Abdullahi ya ce sun bi diddigi kuɗi N661,464,601.50 da ke cikin asusan zuwa ga Mele Kyari.
"Ƙarin bincike ya nuna sun yi ta ɓoye sawun hada-hadar a matsayin kuɗaɗen da aka biya na ƙaddamar da wani littafi da kuma ayyukan wata ƙungiyar bayar da agaji mai zaman kanta."
A shirye nake domin kare kaina - Kyari
Mele Kyari wanda ya jagoranci NNPC daga 2019, lokacin da marigayi Muhammadu Buhari ya naɗa shi, zuwa Afrilun 2025, lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya sauke shi, ya sha musanta zargin almundahana a lokacin mulkinsa.
Ya taɓa musanta cewa EFCC ta kama shi kan zargin ɓatan dala biliyan 2.9, waɗanda aka ware domin gyaran matatar mai.
Wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X tun watan Mayu, Kyari mai shekara 60 ya siffanta rahotonnin da cewa "na ƙeta ne" da zimmar ɓata masa suna.
A lokacin, ya ce yana "kan hutun aiki" bayan shafe shekara 30 yana aiki da kamfanin, inda ya nanata cewa a shirye yake ya bayar da bayanan abubuwan da ya yi.
"Ina sake nanatawa cewa na yi aiki da tsoron Allah da sanin cewa ni Musulmi ne kuma zan bayar da bayanan abubuwan da na yi a gaba Allah. Saboda haka, a shirye nake na bayar da bayanan abubuwan da na gudanar a mulkina a wannan duniyar," in ji Kyari.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Lamarin Mele Kyari na ɗaya daga cikin manyan binciken da EFCC ta bayyana da take yi kan yadda aka aiwatar da gyaran matatun fetur.
Binciken ya shafi aƙalla jami'ai 14 da ke aiki a yanzu da waɗanda suka yi ritaya daga NNPC, a cewar rahoton jaridar Premium Times.
Hukumar ta nemi bayanan jami'an kuma, a cewar rahotonni, sun bi diddigin sama da naira biliyan 80 da suka faɗa asusun wani tsohon darakta na NNPC.
Mai magana da yawun EFCC Dele Oyewale ya faɗa wa manema labarai cewa binciken ya shafi kuɗaɗen da aka ware domin gyaran matatar mai ta Kaduna, da Warri, da Fatakwal.







