Me ɗage haramcin haƙo ma'adanai a Zamfara ke nufi?

Asalin hoton, Others
A ƙarshen makon nan ne ministan kula da harkokin ma'adanai na Najeriya, Dele Alake ya sanar da ɗage haramcin haƙo ma'adanai a jihar Zamfara mai fama da matsalar tsaro.
Wannan dai ya kawo ƙarshen shekaru biyar na haramcin da gwamnatin ta saka ga masu haƙo ma'adanai da aka alƙanta da matsalar tsaron da ta ƙi ta ƙi cinyewa.
Mista Alake ya ce "sun ɗauki matakin ne bayan gamsuwa da cewa an samu sauƙin matsalar tsaro a yankunan sakamakon nasarorin da jami'an tsaro suka samu kan wasu gawurtattun ƴanta'adda da suka haɗa da Halilu Sububu."
"Shugaban Tinubu ya amince da ɗage haramcin haƙo ma'adanai a jihar Zamfara. Jihar tana da albarkatun ƙarƙashin ƙasa sannan bisa samun sauƙin matsalar tsaro da aka yi, fanni ma'adinan zai taimaka wa gwamnatin Najeriya da kuɗaɗen shiga." In ji Alake.
Ministan ya ƙara da cewa "jihar Zamfara na da albarkatun gwal da ma'adanin lithium da jan ƙarfe saboda haka ɗage haramcin zai haɓaka tattalin arziƙin jihar ta Zamfara da ma faɗin ƙasar."
Zamfara ta shiga sahun jihohi masu albarkatun ƙasa
Alhaji Nasiru Alhassan Bamanga wanda shi ne sakataren zartarwa na hukumar kula da ma'adinai da bunƙasa albarkatun ƙasa ta jihar Zamfara, wanda kuma ya jima yana faɗi tashin ganin an ɗage wannan haramci na haƙo ma'adan, ya ce yanzu jihar za ta shiga sahun jihohin da ke cin moriyar kaso 13 na abin da suke samarwa.
"Kamar yadda ka sani dukkannin jihohin da ke da albarkatun man fetur, suna amfana daga kaso 13 na abin da aka haƙo saboda haka ita ma jihar Zamfara nan ba da jimawa ba za ta shiga jerin jihohin da ke amfana daga kaso 13 na abin da aka haƙo a jihar. Kenan jihaR za ta samu kuɗin shiga kuma ƴan jihar su ma samu ayyukan yi.
Shugaban hukumar ya kuma ƙara da cewa "Muna godiya ga Allah da ya sa muka ga wannan rana domin sanin alfanun haƙar ma'adanai da irin abubuwa na alkairi da ke cikin wannan harka."
"Idan ka cire noma babu wata harka ko sana'a da ke bai wa dubban mutane arziki kamar haƙar ma'adanai tun daga mai haƙa da mai sayarwa da mai saye saboda haka sakamakon haramcin da aka ɗora na shekaru biyar dubban al'ummar jihar Zamfara sun talauce sakamakon rasa ayyukan yi da suka yi. Haka su ma gwamnatin jiha da ta tarayya dukkansu sun rasa kuɗin shiga." In ji Alhaji Nasiru Alhassan.
Ra'ayin masana tsaro
Malam Kabiru Adamu, shugaban kamfanin tsaro na Beacon Consulting ya ce ɗage wannan haramci "lallai zai taimaka wa jihar samun ƙaruwar arziƙi amma fa sai idan gwamnati ta yi amfani tsarin bisa gaskiya da riƙon amana da kuma karɓar haraji, inda hakan zai iya taimaka wa wajen rage matasan da ba su da ayyukan yi da ke haddasa matsalar tsaron da jihar ke fama da shi."
To sai dai kuma dangane batun da ministan ma'adanai na Najeriya da ya yi cewa sun ɗage haramcin ne saboda samun cigaba a sha'anin tsaro, Malam Kabiru Adamu ya ce "har yanzu ba mu samu bayanai da ke nuna cewa an kawar da matsalar tsaron da za ta bayar da damar gudanar da ayyukan ma'adanai a jihar."
Abin da ke faruwa shi ne akwai wasu ƙasashe da ke gudanar da ayyukan haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba inda suke bai wa ƴanbindiga makamai domin su tabbatar da babu gwamnati a yankunan domin cigaba da haƙar ma'adan ba bisa ƙa'ida ba." In ji Shugaban na Beacon Consulting.










