Dattawan Arewa sun ce za su sasanta Dangote da AbdusSamad BUA

Wata dambarwa tsakanin hamshaƙan attajirai mafi arziƙi a Afirka, da suka mallaki manyan masana'antu da harkokin kasuwanci a Najeriya da ma sauran ƙasashen nahiyar, tana ci gaba da jan hankula da damun hatta manyan dattijan arewacin Najeriya.
Wutar rikici tsakanin Aliko Dangote da AbdusSamad Rabi'u, dukkansu daga jihar Kano, ta shafe tsawon shekaru tana balbali, amma abin da ya iza ta a baya-bayan nan, shi ne farashin sumunti.
A baya, an ga yunƙuri daga wasu shugabanni ciki har da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, don sasanta tsakanin mai gungun kamfanin Dangote da takwaransa da ya mallaki gungun kamfanin BUA, ga alama dai rikicin har yanzu bai zo ƙarshe ba.
Sai dai a yanzu, Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta shigo ciki, inda ta fito bainar jama'a ta sanar da ɓacin rai game da faɗan manyan, har ma ta yi tayin sasanta tsakaninsu.
Dattijan dai sun bayyana damuwa game da cacar-bakin ɓangarorin biyu, wanda suka ce abin kunya ne.
Sun ƙara da cewa kamata ya yi hamshaƙan attajiran su fi mayar da muradin al'ummarsu da ke cikin halin talauci da matsalar tsaro, a gaba da komai.
Dakta Sadiq Umar Abubakar Gombe, mataimakin daraktan gudanarwa na ƙungiyar, ya shaida wa BBC cewa abin mamaki ne a ce mutum na farko da na biyu da suka fi kowa a arziƙi a Afrika, sun fito suna irin wannan cacar-baki a duniya," in ji shi.
Ya ce "ganin abin da ke faruwa tsakanin ƴan kasuwar ne, ya sa shugabanmu Farfesa Ango Abdullahi ya ga dacewar a kira su, domin a zauna da su don jan hankalinsu.
Ba dai haka kawai waɗannan gaggan 'yan kasuwa suke rikici da juna ba, BUA da Dangote suna sarrafa kayayyakin masarufi kusan nau'i iri ɗaya don sayarwa a babbar kasuwar Afirka ta Yamma da sauran ƙasashen nahiyar.
Sun mallaki masana'antun sarrafa kayan abinci kamar taliya da sukari da gishiri da fulawa da maggi da shinkafa, da kuma kayan gini kamar sumunti.
Faɗan kasuwar sukari
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dangote da BUA, manyan 'yan kasuwa biyu ne da ke hamayya da juna a fagen harkar sarrafa sumunti da sukari.
Kafofin labaran Najeriya sun ce hamayya tsakanin ɓangarorin biyu ta yi tsanani, inda har takan kai su ga zuwa kotu, da shiga kafofin yaɗa labarai, kuma ana ganin baƙin kishin har a kan titi.
Kamfanin Sumuntin Dangote shi ne mafi samar da sumunti a Najeriya, da yake sayar da fiye da kashi 60 na ɗaukacin sumuntin da ake kai wa kasuwa a ƙasar.
Kamfanin Sumunti na BUA shi ne mai samar da sumunti na biyu mafi girma, kuma yana sayar da kimanin kashi 20 na duk sumuntin da ake kai wa kasuwa.
Rahotanni sun ce taƙaddama tsakanin kamfanonin sumuntin hamshaƙan 'yan kasuwan biyu, ta fara ne a 2008, lokacin da BUA ya fara kai sumuntinsa kasuwa.
Cikin sauri kuma ya kafa kansa, har ya zama babban abokin hamayyar Kamfanin Sumuntin Dangote, kuma daga lokacin ya fara kankane kasuwa.
A wani al'amarin kuma, kamfanin sukari na Dangote shi ne mafi girma a Najeriya. Yana sayar da fiye da kashi 70 na duk sukarin da ake kai wa kasuwa, yayin da BUA yake biye da shi da yawan cinikin kashi 20.
A shekara ta 2020, kishi ya sake tashi a tsakani, bayan kamfanin sumunti na BUA ya zargi takwaransa na Dangote da toshe hanyar zuwa mahaƙar ma'adanin limestone a jihar Edo.
Jaridar Blueprint ta ce hamayya kan harkokin samar da sukari tsakanin 'yan kasuwan biyu ta yi tsanani a 2014, lokacin da sukarin BUA ya shiga kasuwa.
A shekara ta 2020, kamfanin Dangote ya zargi BUA da ƙayyade farashin sukari ta haramtacciyar hanya. Sai dai BUA ya musanta zargin, har yanzu kuma batun yana kotu.
Blueprint ta ce a watan Yunin 2023, kamfanin sukari na BUA ya zargi kamfanin sukari na Dangote da tura 'yan banga su far wa masana'antar sukarinsa ta Fatakwal.
Zargin da kamfanin Dangote ya musanta, amma BUA ya gabatar da shaida don kafa hujja kan iƙirarinsa. Jaridar ta ce har yanzu batun na hannun 'yan sanda suna bincike.
Me Dangote ya ce?
Kamfanin Aliko Dangote dai ya zargi rukunin kamfanin BUA da yunƙurin ɓata masa suna a bainar jama'a da kuma shatale wa harkokin kasuwancinsa ƙafa.
A wata sanarwa da ya fitar mai shafi bakwai wadda aka wallafa ranar 2 ga watan Nuwamba, Dangote ya yi watsi da iƙirarin cewa ana bincikensa kan shiga haramtacciyar harkar canjin kuɗaɗen waje.
Da kuma halasta kuɗin haram, da yawansu ya zarce dala biliyan uku, tun zamanin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
"Hankalin hukumar gudanarwa ta Dangote Industries Limited ya je ga wani ƙage da aka ƙirƙira, wanda kuma ke yawo a shafukan sada zumunta kan zargin shiga haramtacciyar harkar canji ta kuɗaɗen waje.
"Wannan zargi ne kawai da ba shi da tushe balle makama," in ji Kamfanin.
Dangote ya ce ba ɗabi'arsa ba ce mayar da martani a kan zargin da ba na gaskiya ba, amma duk da haka, ya ce an taɓa yi masa wannan ƙage a can baya.
Gungun kamfanonin Dangote ya nuna yatsa ga Rukunin Kamfanonin BUA a kan shirya maƙarƙashiyar wannan mugun yarfe a kafofin yaɗa labarai ta hanyar fakewa a matsayin wani ɗan ƙasa da ke nuna damuwa kan al'amuran da ke faruwa.
Ya ce an yi haka ne kawai don yi masa zagon ƙasa a harkar kasuwancinsa.
Dangote ya sake jaddada cewa yana samo canjin kuɗaɗen waje na dumbin harkokin da yake gudanarwa ne daga kasuwar canjin kudi tsakanin bankuna bisa amincewar CBN.
Kamfanin ya ƙara da cewa an bi halastacciyar hanya wajen amfani da kuɗaɗe a aikin faɗaɗa ayyukansa a faɗin Afirka.

Asalin hoton, KANO GOVT
Mene ne martanin AbdusSamad BUA?
Da yake martani, a cikin wata sanarwa da hukumar gudanarwar kamfanin ta fitar a ranar Juma’a, BUA ya tuna yadda ya bijirewa 'manakisar' kamfanin Dangote tsawon shekara 32, yayin da kamfanonin biyu ke tserereniya a fannoni daban-daban na kasuwa don samun tagomashi.
“Ana son a ɓata mana suna.
"Mun bunƙasa, muna faɗaɗa ayyukanmu tare da ba da gudummawa ga tattalin arzikin Najeriya, ba tare da mun yi zagon ƙasa ba.
"Abin da ke da nauyi ne mu magance iƙirari da kuma ƙoƙarin cin zarafi da Aliko Dangote ya yi wa BUA, in ji sanarwar.
Don nuna tsinkaye da hangen nesa, yana da muhimmanci a sake duba tarihi - tarihin da ba na hamayya ba, amma na juriya; ba na gaba ba, na yin haƙuri.
BUA ya ce Aliko Dangote na ƙoƙarin yi masa zagon ƙasa ne a wata sanarwa mai shafi hudu da ya fitar a baya-bayan nan, bayan ɗaukar nauyin gangami tsawon watanni don ɓata masa suna ta hanyar amfani da wasu mutane.
Kamfanin ya kuma ce can a baya kusan shekara 30, Dangote ya yi ta ƙoƙarin ganin bayansa a harkar kasuwanci.
Ya yi iƙirarin cewa Dangote ya taɓa jefa shi cikin wani yanayi da ya kusa kai wa ga kotu ta rufe masa kadara.
Kamfanin ya kuma zargi Dangote da yunƙurin wargaza shirinsa na kafa masana'antar sukari a Lagos, ta hanyar amfani da masu mulki.
Ya kuma zargi Dangote da ƙoƙarin hana shi kasuwancin sumunti duk da yake ya samu lasisin yin haka daga gwamnatin Yar’adua.
Zarge-zargen da kamfanin Dangote ya musanta.
Bai kamata ba - Dattawan Arewa
Kungiyar Dattawan Arewa dai, ta ce duk da yake tserereniyar kasuwanci tana da tushe, amma hamayya irin ta BUA da Dangote, ba ta dace ba, musamman a yanzu, da mutanensu ke cikin ƙuncin rayuwa.
"Akwai yadda za a yi hamayyar kasuwa, ba tare da an fito fili ana irin waɗannan abubuwa da muke gani a wajensu ba," in ji Dakta Sadiq.
Dattawan sun roƙi gudunmawar addu'o'i daga jama'ar Arewa a kan niyyar da suke da ita, ta sulhunta manyan ƴan kasuwan biyu.

Asalin hoton, Sambokhan Giwa
Sun kuma yi kira ga ɗaukacin shugabanni da masu ruwa da tsaki a yankin, su ma su sanya baki wajen sulhuntawar.
Sanarwar ƙungiyar ta ƙara da cewa; “Dattawan Arewa sun damu matuƙa game da rashin fahimtar juna da kuma takun-saƙa tsakanin fitattun ‘yan kasuwan, abin da ke nuna mummunar illa ga tattalin arziƙi da siyasar yankin.
Dakta Sadiq ya ce yankin da suka fito na arewa shi ne ya fi kowanne zama cikin ƙuncin rayuwa a Najeriya.
Ya ce abin da ya kamata su yi, shi ne ƙoƙarin ɗaukar matasa aiki don rage zaman banza da talauci, maimakon tade ƙafar juna a bainar jama'a.










