Zambia ta yi watsi da wasu shafukan batsa da ke cikin litattafan koyar da dalibai

.

Asalin hoton, Getty Images

Ma'aikatar ilimi a Zambia ta yi watsi da wasu shafuka na litattafan koyarwa da ke dauke da abubuwan batsa wadanda ake ta yadawa a shafukan sada zumunta.

Ma'aikatar ta ce an sauya yadda shafukan suke kuma sam ba su yi dai-dai da tsarin koyarwar Zambia ba, kamar yadda wata sanarwa ta shaida.

Sanarwar ta ce daya daga cikin shafukan na bogi - wanda ke bayani karara kan batsa - ya samo asali ne daga Tanzania kuma ya soma karade shafukan sada zumunta a kasar a 2021.

"Litattafan da ke yawo a shafukan sada zumunta ba su fito daga ma'aikatar ilimi ba. Bangon littafin ba na bogi bane amma shafin da ake yawo da shi ba daga cikin litattafan na Zambia bane," in ji Douglas Syakalima, ministan ilimi.

Ma'aikatar ta kuma sauya sunan darasin koyar da zamantakewar aure zuwa darasi kan kiwon lafiya da zaman rayuwa sakamakon korafe-korafen da malaman makaranta da malaman addini suka gabatar.