Mene ne hukuncin wanda ya mallaki takardun bogi a Najeriya?

ma'auni guda biyu a kan sikeli da ke almata kotu

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Talata ne ministan kimiyya da fasahar Najeriya, Geoffrey Uche Nnaji ya sanar da ajiye muƙaminsa sakamakon taƙaddamar da ta taso kan zarginsa da amfani da digirin bogi.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriya, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin ministan.

Wani bincike da jaridar Premium Times ta gudanar ya zargi Mista Nnaji da amfani da digirin bogi daga Jami'ar Najeriya ta Nnsuka, lamarin da ya ɗauki hankalin ƴan ƙasar matuƙa, duk da ya musanta.

Mista Nnaji ya ce ana yi masa bi-ta-da-ƙullin siyasa ne, lamarin da ya zargi "abokan hamayyarsa a siyasa" da yunƙurin ɓata masa suna.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun wani jami'in gwamnati mai ci da mallakar takardun na bogi ba, inda daga bisani suke sauka daga muƙaman nasu sakamakon matsin lamba.

Tambayar da ake yi yanzu ita ce ko mene ne hukuncin wanda aka samu da laifin mallakar takardun bogi?

Mene ne mallakar takardun bogi?

Barista Sulaiman Magashi lauya mai zaman kansa a birnin Kano ya ce dokokin Criminal Code da Penal Code da ake amfani da su a arewaci da kudancin Najeriya da ma dokokin da suka kafa hukumar ICPC sun yi bayani dangane da ma'anar takardun bogi.

"Wannan ya haɗa da mutum ya ƙirƙiri takarda ko kuma mutum ya yi amfani da ita tare da sanin cewa ita wannan takardar ta bogi ce." In ji Barrister Sulaiman.

Hukuncin mallakar takardun bogi

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Barista Sulaiman Magashi ya ce dukkannin dokokin Criminal Code na kudanci da kundin Penal Code na arewacin Najeriya da kuma dokokin da suka kafa hukumar ICPC duka sun tanadi hukunci ga duk mutumin da aka kama da laifin mallakar takardun bogi.

Sashen na 463 na kodar manyan laifuka na Najeriya ya keɓe hukuncin zaman gidan yari na shekara uku ga duk wanda aka kama da mallakar takardun bogi.

Su ma sassa na 363 zuwa 364 na dokokin Penal Code sun yi bayanai kan mene ne takardun bogi.

Ya kuma ƙara da cewa sassan sun tanadi hukuncin mallakar takardun bogi da ya haɗa da zaman gidan kaso zuwa ɗaurin rai da rai ya danganta da irin girman laifin.

"Misalin wanda ya kwafi hatimin shugaban ƙasa ko kuma gwamna. Ko sa-hannun shugaban ƙasa ko sa-hannun gwamna. Ko wani ofishi na gwamnati. Wannan hukuncin na kai wa har ɗaurin rai da rai''.

A Penal Code ma akwai irin waɗannan hukunce-hukunce sai dai hukuncin ya fara daga ɗaurin shekara 17 har zuwa ɗaurin rai da rai...ya danganta da ƙarfin takardar da mutum ya yi boginta."

Barrista Magashi ya ce ita ma dokar da ta kafa hukumar ICPC ta yi tanadi a kan duk wanda ya gabatar da wata takarda ba tare da sanin cewa wannan takardar ta bogi ce ba.

"Shi ma zai fuskanci ɗauri na tsawon shekaru biyu ko tarar naira 100,000 ko kuma a haɗa masa guda biyun. Idan kuma ma'aikacin gwamnati ne to ɗaurin zai iya kai wa har tsawon shekaru uku." In ji Barista Magashi.

Ko ana hukunta masu laifin takardun bogi?

Barista Sulaiman Magashi ya ce akwai shari'o'i da yawa a kan takardun bogi a gaban alƙalai.

To sai dai ya ce har yanzu bai san wani jami'in gwamnati da aka gurfanar a gaban kuliya domin hukunta su.

"Yawanci da zarar sun sauka daga muƙamansu shikenan batun ya tafi. Ba ka sake jin labarin."

Barista Sulaiman ya kuma ce dalilin da ya sa yake ganin ba a hukunta masu laifi shi ne rashin bibiyar batun bayan saukar jami'an daga mulki.

"Da ma ƙungiyoyi masu zaman kansu ne suke bibiyar batun. Su ne ya kamata su ɗauki gabarar bibiyar batun tun daga wurin ƴansanda har zuwa kotu'', in ji shi.

Ya kuma ƙara da cewa ƙungiyoyin ne ya kamata su tabbatar da cewa kotu ta hukunta mutum idan an same shi da laifi.

''Idan kuma ba a same shi da laifi ba sai a sallame shi." In ji Barista Magashi.