Antony Blinken ya je China don kyautata alaƙa da Amurka

Asalin hoton, Reuters
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya gana da ministan harkokin wajen China Qin Gang a ziyarar kwanaki biyu da yake yi a China don ganawa da jami'an ƙasar.
Ziyarar ita ce ta farko da wani jami'in Diplomasiyyar Amurka ke kai wa China cikin a ƙalla shekara biyar.
Jami'an Amurka sun ce maƙasudin tataunawar shi ne don kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu wadda a baya-bayan nan ta yi tsami.
Ziyarar na zuwa ne watanni biyar bayan da aka ɗage ziyarar da mista Blinken ya shirya kai wa China, bayan da aka ga wani bala-balan da ake zargin na leƙen asirin China ne, na shawagi a sararin samaniyar Amurka.
Mista Qin ya gana da Mista Blinken ranar Lahadi gidan saukar baƙi na ƙasar.
Jamai'an Amurka sun ce maƙasudijn ganawar shi ne domin buɗe kofar kyautata hulɗa tsakanin manyan ƙasashen biyu, tun bayan saɓanin da aka samu kan bala-balan ɗin
A baya-bayan nan China ta ƙaddamar da atisayen soji a Taiwan wadda take kallo a matsayin wani ɓangare nata.
A ɓangare guda kuma Amurka na da kyakkyawar alaƙa da gwamnatin dimokradiyyar Taiwan.
Daga cikin batutuwan da ake ganin tattaunawar za ta mayar da hankali a kai har da batun yaƙin Ukraine da rikicin kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu, da tsarin fasahar zamani da cinkin ƙwayoyi da batun 'yancin ɗan adam.
Jami'an China na maraba da ziyarar ta Mista Blinken, inda suke cike da fatan kyautata dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
Ba a dai sani ba ko mista Blinken zai gana da shugaban China Xi Jinping a ziyarar tasa ba.
Mista Blinken ya kasance babban jami'in Amurka na farko da ya ziyarci China tun bayan da shugaban Amurka Joe Biden ya hau kan karagar shugabancin ƙasar a 2021.
Ganawar da shugabanin ƙasashen biyu suka yi a tsibirin Bali cikin watan Nuwamban bara ya rage yaƙin cacar baki tsakanin ƙasashen biyu.
To sai dai tun bayan bayyana wata balan-balan da ake zargi ta leƙen asirin China ce a sararin samaniyar Amurka, aka koma kallon hadarin-kaji tsakanin ƙasashen.











