Abubuwan da wasu ƴan Najeriya ke so Buhari ya yi

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Getty Images

A yayin da ake ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban a Najeriya, da sace mutane da matsin tattalin arziki da ake ciki, wasu ƴan ƙasar sun fara fitar da rai da samun irin sauyin da suka sa ran samu a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

Akwai ɗumbin matsalolin da suka daɗe suna addabar mutane a ƙasar kamar yadda bayanai ke nunawa, kama daga hauhawar farashi da rashin tsaro da ma yajin aikin jami'o'i.

Sai dai ga alama lamarin ya ta'azzara a baya-bayan nan ta yadda har ƴan ƙasar suke nuna ɓacin ransu a inda duk suke ganin za su iya, musamman shafukan sada zumunta.

Daga ƙarshen makon da ya gabata zuwa ranar Litinin kawai, wasu abubuwan tashin hankali sun faru, kamar sakin bidiyon da masu tayar da ƙayar baya suka yi da ke nuna yadda suke dukan fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna da suka sace wata huɗu da suka wuce.

Sannan harin kwanton ɓauna da aka kai wa rundunar dogarawan fadar shugaban kasa a daren Lahadi a Abuja.

Dangane da waɗannan al'amura marasa daɗi da ke faruwa ne ya sa BBC Hausa ta tambayi masu bin shafukanta na sada zumunta, kan ko "me za su iya gaya wa shugaban Najeriyar idan za su samu damar aika masa da wasiƙa?"

Mun tsamo wasu muhimman saƙonnin za mu wallafa su a cikin wannan labarin.

A shafinmu na Facebook inda aka wallafa saƙon, cikin sa'a uku da wallafa shi ya isa ga mutum sama da 230,000, sannan sama da mutum 8,000 ne suka yi tsokaci zuwa lokacin.

Tunawa da alkawari

Ga alama mutane da dama a shafin sun fi mayar da hankali ne kan cewa za su rubuta wa Shugaba Buhari wasika su tuna masa alkawuran da ya yi kafin ya hau mulki.

Da yawa suna cewa ba alkwarin kashe-kashe da sace al'umma ya yi musu ba, ya yi musu alkawari ne na kare tare da tsare rayukansu da kuma kare martabarsu a matsayin su na ƴan Najeriya.

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya yi wa ƴan Najeriya alkawura da dama musamman na kawo sauyi a lokacin da yake kamfe

Ga wasu daga cikin saƙonnin:

Muhammad Shehu Altine ya ce: "Ya ji tsoron Allah ya tuna alƙawarin da ya yi wa ƴan Najeriya. Ba abin da ke dauwama har abada, mulki da rayuwar duka masu ƙarewa ne.

Sophiis Boutik ya ce: "Zan tura masa saƙon cewa na farko shin ko ya manta da alkawuran da ya ɗauka kafin ya samu mulki, duk abubuwan da ya fada cewa zai yi a cikin kashi 100 bai yi ko 30 ba.

Yabar rayukanmu kara zube ba ilimi ba tsaro ba wutar lantarki ba abinci komai ya yi tsada, ba noma musamman harkar tsaron nan idan kana cikin gida a zo a dauke ka ba ka tsira ba.

Idan ka fita daman shi wannan sai yadda Allah ya yi da kai. To yasani cewa zai mutu kuma zai haɗu da Allah sai yasan yadda zai kare kansa.

Allah mun tuba Allah ka kawo mana ɗauki muna cikin bala'i a Najeriya.

Masu addu'a

Ga alama da yawan masu tsokacin sun saduda tare da miƙa wa Allah dukkan lamarin.

Sun ce su maimakon rubuta wa Shugaba Buhari wasiƙa, gara su ci gaba da addu'a suna miƙa al'amarinsu ga Allah.

A ganinsu a yanzu babu wata sauran mafita da ta wuce duƙufa da addu'o'i don Allah Ya ceto ƙasar daga halin da take ciki.

Al'mansoor Gusau ya ce: "Allah (SWT) ya kawo mana karshen wannan musiba alfarmar Annabi Muhammad (SAW).

A ƙarƙashin tsokacinsa sai da mutum 35 suka amsa wannan addu'ar.

Usama Kulubat ya ce: "Allah ya sa kagama lafiya Allah ya shiga lamarin ƙasata."

Tunatarwa kan tsoron Allah

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan Najeriya sun nuna wa Shugaba Buhari ƙauna a shekarun da ya shafe yana neman mulkin ƙasar
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Waus daga cikin dubban saƙonnin kuma sun fi mayar da hankali kan tunatar da Shugaba Buhari ne cewa ya ji tsoron Allah.

Daga cikin masu irin wannan saƙo akwai:

Umar Abdullahi Makarfi ya ce: "Zan fada masa ya ji tsoron Allah, ya sani Allah zai tambaye shi akan waɗannan rayukan da ake kashewa karkashin mulkinsa.

Ummu Ja'afar Shika ta ce: "Ya ji tsoron Allah. Masoya ba su cancanci azabtarwa da cin amana ba. Jinin talakawa amana ne gare shi.

Su ma mutane ne, kuma tabbas Allah yana nan a madakata da sannu zai bi mana dukkanin haƙƙinmu.

Nanerh Hawwerh ta ce: "Zance ya ji tsoron Allah ya tuna alkawarin da ya mana a baya.

Ahmad Abubakar ya ce: Malam Buhari ka ji tsoron Allah. Ka dinga tunanin mutuwa da kwanciyar kabari kai kadai. Ka dinga tunawa cewa wallahi wallahi Allah ba zai ƙyaleka ba.

Hadiza Abubakar ta ce: "Barka da rana Shugaba Muhammadu Buhari. Bayan gaisuwa mai yawa da so da yarda, muna tunatar da kai cewa mutane kake mulka ba dabbobi ko aljanu ba.

"Ka ji tsoron Allah ka ji tsoron ranar da Allah zai tsayar da kai yayi mana hisabi, ka tuna kwanciya kabari.

"Kai Musulmi ne. Ka tuna cewa Allah ba ya yafe hakkin wani akan wani. Tabbas mutane suna cikin Halin ni ya su."

Mubarak Ibrahim Lawan ya ce: "Buhari ka daure ka dinga karanta kwament na duk labaran da suka shafe ka a shafin BBC.

"Kuma ka daure ka dinga sauraron Sheikh Bello Yabo. A ƙarshe, ka ji tsoron Allah!

Sauka daga mulki

Akwai kuma kason da su nasu saon shi ne kira ga Shugaba Buhari da ya sauka daga mulkin idan ba zai iya ba.

Masu faar hakan ga alama suna sane cewa dama saura bai fi saura wata 10 ba ya kammala wa'adin nasa.

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Ga wasu daga saonnin masu irin wannan ra'ayin:

Isah Dan Sidi ya ce: "Zuwa ga Shugaba Buhari tun da ka kasa kawo karshen matsalar kasar nan, to ka yi wa Allah ka rubuta ka ajiye muamin ka daga yanzu. "Bissalam

Mansur Ahmed ya ce: "Kawai ya sauka."

Umar G. Babangida ya ce: "Ya ji tsoron ALLAH ya sauka daga kan mulki, ko don haduwarsa da Ubangiji saboda alama ta nuna ba zai iya ba. Tsawon shekara kusan takwas kulun sai aruwar masifa da wahala ga an kasa.

Mujittapha Muhammad Auwal ya ce: "Cewa zan yi ya yi wa Allah da Annabi ya sauka, tun da ya gaza cika alkawarin da ya auka.

"Ya tuna lokacin da yake neman uri'ar talakawa da yadda talakawa suka yi ƙoƙari wajan zabarsa."

Babu dabarun warware matsalolin?

Ga alama ruwa ya fara ƙarewa ɗan kada, don kusan dukkan masu tsokacin nan ba bijiro da wasu hanyoyi ko matakai a matsayin shawarwarin da shugaban ƙasar zai yi amfani da su.

Ba mamaki hana na da nasaba da ko dai sun gajiya, ko kuma suna ganin babu sauran dabara.

Wataƙila shi ya sa dukkanin saƙonnin yawanci na addu'a da fata ne.

Amma dai fadar gwamnatin Najeriya ta sha musanta irin waɗannan maganganu tana mai nanata cewa Shugaba Buhari na iya bakin ƙoƙrinsa.

Ko a kwanan nan ma an jiyo shugaban da kansa yana cewa gwamnatinsa ta fi ta baya ƙoƙari ta kowane fanni a Najeriyar.