Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An naɗa sabon sarkin Kuwait
An sanar da naɗin sabon sarkin Kuwait bayan mutuwar sarkin ƙasar Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Jaber al-Sabah.
Sabon sarkin, mai suna Sheikh Meshal al-Ahmad al-Jaber al-Sabah, ɗan uwa ne ga Sheikh Nawaf.
A yau Asabar ne aka sanar da rasuwar marigayin mai shekara 86.
Sabon sarkin wanda tuni ya fara gudanar da wasu ayyuka, ya shafe akasarin rayuwarsa a ɓangaren tsaro da tattara bayanan sirri na Kuwait.
Tuni aka ayyana makokin kwana 40 a faɗin ƙasar, domin nuna alhini kan rasuwar tsohon sarkin.
Wane ne tsohon sarkin?
Sheikh Nawaf Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah shi ne sarkin Kuwait na sha shida, kuma shi ne na shida tun bayan lokacin da ƙasar ta samu 'yancin kai daga Burtaniya.
Sheikh Nawaf ya zama Yarima Mai Jiran Gado na shekaru 14, kafin a 2020 a mayar da shi sarki bayan mutuwar Sheikh Sabah Al-Ahmad.
An haifi Sheikh Nawaf a ranar 25 ga watan Yunin 1937 a Fareej Al-Shuyoukh a birnin Kuwait.
Ya girma a fadar Dasman ta birnin Kuwait, inda nan ne gidan iko lokacin mulkin mahaifinsa, Yarima Ahmed Al-Jaber, ya kuma yi karatun a Kuwait, cikin makarantun da ya yi har da Mubarakiya.
Sheikh Nawaf ya aure Sharifa Sulaiman Al-Jassem Al-Ghanim a shekarun 1950, yana da yara huɗu maza da 'yarsa mace ɗaya.
Sheikh Nawaf ya riƙe mukaman siyasa da dama, inda ya fara da gwamnan jihar Hawalli a 1962 na tsawon shekara 16, sai kuma ya zama ministan cikin gida a 1978.
A 1988, ya zama ministan tsaro, kuma shi ne ya jagoranci ƙasar lokacin da aka yiwa Iraƙi mamayar watanni bakwai, wanda shiga tsakanin Amurka ya kawo ƙarshen shi a wani haɗin gwiwar aikin soji da aka yi a yakin Gulf na biyu a 1991.
Sheikh Nawaf ya zama sarki ne bayan mutuwar Sheikh Sabah Al-Ahmad.
Kuma yana da rawar takawa wajen tsara manufofin harkokin waje, Inda ya riƙa aikin shiga tsakanin a rikicin yankuna daban-daban.
Ana kiransa "shugaban diflomasiyya." na Kuwait da yankin Larabawa.
Ya zama sarki a ranar 29 ga watan Satumba 2020, inda aka rantsar da shi washe gari a gaban majalisar ƙasar.