Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Su wane ne kan gaba a haɗakar kayar da Biya a zaɓen 2025?
Gabanin zaɓen shugaban ƙasa a Kamaru, da alama haɗakar ɓangaren adawar ƙasar na ci gaba da samun ƙarin gwiwa, a ƙoƙarin su na kawar da gwamnatin shugban ƙasar, Paul Biya.
Haɗakar ta ƴan adawa ta fara tayar da saiti, bayan wasu ƴan takarar shugaban ƙasar sun fara janye wa domin mara wa juna baya.
Fitaccen lauya kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan'adam, Akere Muna ya janye aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a Kamaru, inda ya sanar da goyon bayansa ga Bello Bouba Maigari, wanda ake ganin yana cikin manyan ƴan adawa a zaɓen.
A wajen wani gangami a jiya Lahadi, a birnin Douala Mr. Muna na jam'iyyar UNIVERS ya buƙaci magoya bayansa su mara baya ga Maigari.
Mr Muna ya zamo ɗan takara na biyu da ya janye domin goyon bayan Bello Bouba Maigari, bayan Caxton Seta Ateki.
Ba dai wannan ne karon farko da Muna ya janye daga takarar shugaban ƙasa a Kamaru ba, domin ko a 2018 ya janye domin mara baya ga jagoran ƴan adawar ƙasar, Maurice Kamto wanda ya sha kayi a zaɓen.
Bayan sanar da nasarar shugaba Paul Biya a zaɓen kuma, Mr. Kamto ya yi iƙirarin cewa shi ne ya yi nasara, tare da zargin an tafka maguɗi.
A yanzu dai yawan ƴan takara a zaɓen shugaban ƙasar Kamarun da aka tsara yi a ranar 12 ga watan Oktoba ya ragu, daga mutane 12 ga aka tantance tun da farko, zuwa 10 da suka rage a yanzu.
Ƴan adawar Kamaru dai sun kafa wata gamayya da nufin goyon bayan takarar Bello Bouba Maigari, domin fuskantar shugaba Paul Biya, wanda bai taɓa faɗuwa zaɓe ba.
Amma har yanzu akwai ƴan takarar da suka ƙi shiga, inda suke ganin sun fi yarda su tsaya takara ba tare da yin wata haɗaka ba.
Bello Bouba Maigari mai shekara 78 gogaggen ɗan siyasa ne da ya taɓa zama Firaministan shugaba Biya.
Ya rike muƙamai da dama a gwamnati, bayan haɗaka da ya ƙulla da shugaba Biya mai shekara 92.
Maigari ya fara kalubalantar shugaba Biya ne a 1992, lokacin da aka yi zaɓen shugaban ƙasar na farko tun bayan ɓullo da tsarin jam'iyyu da dama.
Yayin da ƴan adawa ke ci gaba da tsara dabarun cimma nasara a zaɓen, shi kuwa shugaba Biya yana wata ziyara a Turai.
Ya dai ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa ta wani bidiyon ƙirƙirarriyar basira da ya wallafa a kafar sada zumunta, sannan ya dogara ga ministocinsa domin su yi masa yaƙin neman zaɓe a sassan ƙasar.
Su wane ne ke ƙulla haɗakar?
Dattawan yankin arewacin Kamaru mai yawan ƙuri'u sun tashi tsaye domin ganin ƴan takarar yankin sun ƙulla haɗaka domin mara bayansu ga mutum ɗaya domin cimma nasarar kawar da shugaba Biya a zaben watan Oktoba.
Ambasada Muhammad Sani, daya daga cikin dattawan yan siyasar ƙasar ta Kamaru, ya shaida wa BBC cewa "Muna cikin ɗarɗar dangane da siyasar Kamaru saboda Allah ya ba mu damar ficewa daga masifa da bala'i da muke ciki fiye da shekara 40. Damar ta zo amma muna neman mu ɓarar da ita. Mun samu mutum biyu suna neman su kawo son rai.''
Ya ƙara da cewa ''Dukkanninsu tsakanin Bouba Bello Maigari da Issa Ciroma Bakary sun gaza haɗa kai. Wannan na nuni da cewa za mu ɓarar da damar da mu ƴan arewa muke da ita. Muna son su zo su dunƙule a mara wa mutum ɗaya baya. Wannan ita kaɗai ce damar da Allah ya ba mu na sauya siyasar. Kuma idan dai suka haɗe kai to da izinin Allah za mu ƙwace sarauta ba su isa ba." In ji Ambasada Muhammad Sani.
Bello Bouba Maigari
Bello Bouba Maigari, mai shekaru 78 ya kasance abokin tafiyar shugaba Paul Biya a tsawon fiye da shekaru 30. Maigari ya kasance tsohon firaiminista a jamhuriyar ta Kamaru.
Yanzu haka zai yi takarar domin ƙalubalantar Paul Biya a jam'iyyar NUDP duk da cewa bai ajiye muƙaminsa na ministan harkokin yawon buɗe ido ba.
Shi ne ministan gwamnati na biyu daga arewacin ƙasar da ya bayyana aniyarsa ta takarar neman shugaban ƙasa a baya-bayan nan wani abu da ke nuna ɓaraka tsakanin shugaba Paul Biya da masu faɗa a ji a arewacin ƙasar.
Yanzu haka dai ya riga ya samu goyon bayan ƴan takara biyu, da suka haɗa da fitaccen lauya kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Akere Muna da kuma Caxton Seta Ateki.
Issa Tchiroma Bakary
Shi ma wani tsohon makusancin Biya wanda takararsa ta zo da mamaki, shi ne Issa Tchiroma Bakary, ɗan shekara 75 da haihuwa. Shi ma ya fito ne daga arewacin ƙasar kuma ya yi tasiri sosai wajen taimaka wa Biya samun ƙuri'u daga yankin.
Bayan shafe shekara 20 yana aiki a muƙamai da dama na gwamnati, Tchiroma ya ajiye aiki a matsayin ministan ƙwadago da koyar da sana'oi domin shiga takara da Biya.
Tchiroma, wanda shi ne jagoran jam'iyyar Cameroon National Salvation Front (CNSF), ya soki tsarin tafiyar da gwamnatin Biya kuma ya yi alƙawarin bayan yin nasara zai yi wa baki ɗaya tsarin garambawul.