Ko ɗaukar mataki kan kisan mafarauta a Uromi ka iya zama izina?

Asalin hoton, others
Tun bayan kisan da wasu ƴan sintiri suka yi wa wasu mafarauta 16 ƴan asalin jihar Kano a garin Uromi na jihar Edo cikin makon da ya gabata, hukumomi suka sha alwashin ɗaukar matakan da suka dace domin hukunta waɗanda suka aikata laifin.
Tuni aka yi ta samun kiraye-kiraye daga ƙungiyoyin kare haƙin bil'adama da ƴan siyasa da ɗaiɗaikun jama'a, na gudanar da bincike domin tabbatar da adalci kan mafarautan da aka kashe.
Bayanai daga garin na cewa mazauna garin da maƙwabta na tserewa daga garuruwan nasu saboda zaman ɗar-ɗar da fargabar hare-haren ɗaukar fansa da kuma kamun ƴansanda.
Matakan da aka ɗauka kawo yanzu?

Asalin hoton, Hon Salisu Muhammad Kosawa
Gwamnan jihar ta Edo, Monday Okpebholo ya fara ɗaukar matakai domin tabbatar da adalci ga mutanen da aka kashe.
Tuni ya sanar da dakatar shugaban ƴan sintiri na jihar tare da sanar da kafa kwamiti domin bincike kan lamarin a wani abu da ake kallo a matsayin fara ɗaukar matakan gaggawa.
Haka kuma gwamnan ya kai ziyarar zuwa gwamnatin jihar Kano da ma garin da mafarautan suka fito domin jajanta musu da haƙurƙurtar da su kan abin da ya faru.
Mista Okpebholo ya kuma yi alƙawarin biyan diyya ga mafarautan da aka kashe tare da tabbatar da an hukunta masu laifin.
Daga ɓangaren gwamnatin tarayya kuma shugaban ƙasar Bola Tinubu ya bayar da umarni ga jami'an tsaro su gaggauta binciko waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu domin su girbi abin da suka shuka.
Hukumomin jihar sun ce kawo yanzu an kama mutum 40 da ake zargin suna da hannu kan al'amarin.
Ko matakan da ake ɗauka za su yi tasiri?
Dakta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security, kuma mai sharhi kan al'amuran tsaro a yankin Sahel ya ce matakan da ake ɗauka za su yi tasiri ne kawai idan an magance abubuwan da suke haddasa irin waɗannan matsaloli, ba wai ɗaukar matakan gaggawa ba.
''Babban abin da ya haddasa matsalar shi ne rashin tsaro da ƙasar ke fuskanta'', a cewar mai sharhin.
Ya ƙara da cewa har yanzu babu wani matakai da aka ɗauka na magance matsalar rashin tsaro da ƙasar ke fama da shi.
''A wasu ƙasashen idan irin haka ta faru sai an kira zaman majalisar tsaron ƙasa domin tattaunawa kan batun tare da ɗaukar matakan gaggawa'', in ji ce.
''Wannan al'amarin ya shafi abubuwa guda biyu masu muhimmanci da za su iya gina Najeriya su kuma rusata nan take, wato 'addini da ƙabilanci', kamar yadda ya bayyana.
Ya ce da ya kamata majalisar tsaron ƙasar ta zauna ta ɗauki matakai ƙwarara domin tabbatar da hakan ba ta sake faruwa a nan gaba ba.
Wane tasiri maganganun da aka yi kan batun suka yi?
Tun bayan faruwar lamarin aka yi ta samun kiraye-kiraye daga ƴan siyasa da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam na neman adalci da waɗanda aka kashe da yin alla wadai da lamarin.
Dakta Kabiru Adamu ya ce kiraye-kirayen sun yi tasiri musamman wajen hana ɗaukar fansa.
Sai dai ya ce maganganun ba za su yi tasiri ba wajen kawo ƙarshen wannan matsala a ƙasar.
''Abin da zai yi tasiri shi ne hukunta waɗanda suka aikata laifin da kuma magance aihinin abin da ke haddasa matsalar'', a cewar masanin tsaron.
Ta yaya matakan da za a ɗauka za su zama izina a nan gaba?

Asalin hoton, BBC PIDGIN
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dakta Kabiru Adamu ya ce zai zama izina ne kawai ga masu aikata irin wannan laifi idan ka ɗauki matakai masu ƙwari domin magance ainihin abin da ke janyo matsalar tsaro a Najeriya.
''Idan majalisar dokokin ƙasar ta zauna kan batun ta kuma umarci hukumomin tsaron ƙasar su tabbatar sun magance matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta, musamman ayyukan ƴanbindiga'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa yana da kyau majalisar ta bai wa hukumomin tsaron wa'adin zuwa wani lokaci ta kuma riƙa bibiya domin magance matsalar.
Haka kuma masanin tsaron ya ce yana da kyau a zaƙulo waɗanda suka aikata wannan laifi a kuma hukunta su don ya zama izina a nan gaba.
''An sha yin irin wannan abu a Najeriya, amma daga ƙarshe sai a ƙare ba wanda aka hukunta kan laifin, kan haka ne abin ya ƙi ƙarewa'', in ji shi.
''Hukunta waɗanda suka aikata irin wannan laifi, shi ne zai zama izina ga masu aikata irin hakan, ta yadda nan gaba babu wanda zai yi marmarin ɗaukar doka a hannu'', a cewar Dakta Kabiru Adamu.











