Me ƴan Najeriya ke cewa kan sauya sheƙar Shekarau daga NNPP zuwa PDP?

Shekarau

Asalin hoton, Shekarau Facebook

A ranar Litinin 29 ga watan Agusta ne ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar zai karɓi Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau zuwa jam'iyyar PDP.

A yayin wata hira da BBC Hausa, Sanata Shekarau ya ce ya zaɓi komawa tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP ne saboda yadda magoya bayansa suka nuna a koma can don rashin adalcin da ya ce an yi musu a NNPP.

Wannan shi ne karo na biyu da Sanata Shekarau ya sauya jam'iyya a cikin shekarar 2022. Ya bar APC zuwa NNPP a watan Mayu, sai kuma ya bar NNPP zuwa PDP a Agusta.

Wannan lamari ya matuƙar jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ƴan Najeriya, musamman ma al'ummar jihar Kano.

Me mutane ke cewa?

Wasu daga cikin al'umma na bayyana kaɗuwarsu da matakin ne, yayin da wasu ke nuna cewa babu abin mamaki da al'amauran ƴan siyasa.

A shafin Facebook an tattauna batun sau sama da 70,000.

Wasu sun nuna damuwa kan yadda an siyasa ke sauya sheka a duk lokacin da suka ga dama, suna cewa hakan na faruwa ne saboda kare ra'ayin kawunansu.

Yayin da wasu ke ganin babu wani baike a sauyin jam'iyya tun da dama ita siyasa 'yar ra'ayi ce.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mun duba sakonnin mutane a shafin BBC Hausa Facebook kan labarin.

Tahir Musawa ya rubuta cewa:

"Shi yasa Duk wanda yake fada akan ‘yan siyasa, to babban sakarai ne. Na tabbata akwai waɗanda suka yi rantsuwa a baya, cewa Shekarau ba zai taba komawa PDP ba.

"To ai yanzu dai ga shi. Ubangiji Allah Ya sa mu dace, Ameen."

Jamilu Lawan Riji ya ce:

"Mu dai fatanmu Allah ya zaba mana shugabanni masu tausayin mu da kuma kaunar mu."

Amadu Habu Gamawa ya rubuta cewa:

"Wannan lamari dama jama'a sun dade suna jira saboda abu ne mai wahalar gaske su zauna a inuwa daya."

Bashar Ababukar ya ce:

Wadannan ƴan siyasar namu na Najeriya akidarsu ta siyasa suna yi ne don kansu ba don talakawa ba. Allah ya gyara zukatanmu baki daya, ameen."

Mallam Sagir Muh'd Saidu Daga Zaria a Kadunan Nigeria ya ce:

"Mun gaji da gafara sa amma har yanzu ba mu ga ƙaho ba.

"Yaushe ne 'yan siyasar Najeriya za su gane cewa akwai bambanci tsakanin ƙuduri da kuma rayuwa! Saboda haka ƙudiri gaba yake da rayuwa!"

Sani Mailangelange Yawuri ya ce:

"Hakika a siyasa babu abokin dindindin kuma babu makiyin dindindin. Da fatan Allah Ya samar wa talaka mafita."

'Ba a yi mana adalci ba'

Dama tun da fari ɓangaren Sanata Shekarau ya nuna damuwa game da rashin adalcin da ya ce an yi musu a jam'iyyar NNPP.

Sannan majalisar tuntuɓa ta tsohon gwamnan - wadda ake kira shura - ta fara nema wa tsagin makoma ta hanyar tattaunawa da sauran jam'iyyu.

Wata majiya da ta zanta da BBC ta ce sun kammala shirin tarɓar Atiku tsaf a Kano ranar Litinin bayan sun yi nazari kan tsare-tsaren da ya gabatar musu.

"Sun gabatar mana da tsare-tsarensu, mun yi nazari a kansu kuma za mu karɓe su. A taƙaice dai sanarwa kawai ake jira."

Cikin hirarsa da BBC Hausa a farkon makon nan, Shekarau ya ce babu gaskiya a batutuwan da jagoran jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso ke yi cewa sun shiga jam’iyyarsa a makare.

Wata majiya ta bayyana cewa tun farko an yi yarjejeniya cewa za a bai wa ɓangaren Shekarau kashi kusan 35 na muƙamai, amma daga baya shi kaɗai aka bai wa tikitin takarar sanata.

A nasa ɓangaren, Kwankwaso ya ce sun shiga jam'iyyar a makare amma sun faɗa wa Shekarau cewa su bari a kafa gwamnati don a daidaita rabon.

Me ƙwararru ke cewa?

Masana a harkokin siyasa sun fara tsokaci kan wannan lamari inda suka ce wannan sauyin sheka ta Sanata Shekarau na nuna cewa an kasa samun daidaito tsakanin ɓangaensa da na Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso.

"Wataƙila kuma an samu rashin cika wasu daga cikin alkawuran da aka yi. To hakan na alamta cewa ya hakura da duk wata maslaha da aka cimma a NNPP, bisa dalilin cewa komawa PDP shi ne mafita gare shi da mabiyansa," a cewar Dakta Kabiru Sufi, masanin siyasa kuma malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a a jihar Kano.

Malamin ya ce hakan zai iya yin tasiri da dama a siyasar tshon gwamnan jihar Kanon a daidai wannan lokaci musamman da ya kasance halataccen ɗan takarar NNPP na sanata.

"Yana iya rasa wasu daga cikin magoya bayansa da ba su yarda da fitar tasa ba, kamar dai yadda wasu ba su bi shi ba a lokacin da ya fita daga APC ya koma NNPP ɗin.

"Hakan zai jawo masa raguwar magoya baya, musamman ganin cikin lokaci ƙanƙani wasu su zauna a APC sun ƙi bin sa yanzu kuma wasu za su zauna a NNPP su ƙi bin sa PDP," in ji Dakta Sufi.

Sai dai malamin ya ce babu mamaki kuma a yanzu wasu tsofaffin magoya bayansa da suka zauna a APC su biyo shi PDP ɗin.

"Dud da dai a yanzu ba a ga wasu jiga-jigai sun yi haka ba, amma ana iya hasashen faruwar hakan nan gaba," ya ce.

A hannu guda kuma masanin ya ce babu mamaki wannan sauyin sheka ya kawo maslaha ga matsalolin da suka daɗe suna addabar jam'iyyar PDP.

"Musamman ganin dukkan ɓangarorin da ke adawa da juna a PDP din sun hallara a gidan Shekarau ranar Lahadi, to yana iya zama sanadin shiryawarsu.

"Sai dai idan har ya yi kasadar nuna ɓangaranci to akwai yiwuwar matsalar ta ci gaba da ta'azzara."

Masanin ya ce ana iya samun sauyi a wannan tafiya amma ba lallai ya kasance gagarumi ba.

"Lallai jam'iyyar PDP na bukatar shigar irin su Shekarau don sake samun tagomashi," ya ƙara da cewa.