Manyan dalilan da suka sanya na fita daga APC zuwa NNPP - Shekarau
Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Tsohon gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce ya fita daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar NNPP ne domin ceto Jiharsa daga mawuyacin halin da take ciki.
Tsohon gwamnan wanda kuma tsohon Minista ne, ya shaida wa BBC Hausa cewa "mun dade muna tattaunawa da dan uwana Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, muna nuna damuwarmu ga makomar Kano" shi ya sa suka hada domin ganin sun fitar da Jihar daga matsalolin da ta ke fama da su.
"Mun tattauna mun gaya wa kanmu cewa wajibi mu kawo sauyi a Kano...idan ba mu waiwayi al'ummarmu mun sama wa Kano mafita ba, Allah zai tuhume mu. Damuwarmu ita ce ci gaban al'ummar Kano da Najeriya," in ji Sanata Shekarau.
Ya kara da cewa sun bar APC ne domin ba a yi musu adalci don haka suke ganin komawarsu NNPP ita ce hanyar da za su kawo sauyi ga al'ummarsu.
Sanata Shekarau ya ce "ni a ganina siyasa mu'amala ce. Shi ya sa nakan ce duk jam'iyyun nan uwarsu daya, ubansu daya. Ba sunan jam'iyyar muke bi ba, abin da muke bi shi ne inda za su samu mutunci da walwala" yana mai cewa samun mukami ba shi ne babban burinsu ba domin kuwa "wannan a hannun Allah yake".